♡
♡ ♡
_*🐘SAWUN GIWA...!*_
_(The Elephant's Foot)__★For How Long Will The Elephant's Foot Be Radioactive?_
*FInd out💥*
*WATTPAD*➖ _HAFNANCY01_
*DEDICATED TO:-Mamina (Sis Nerja'art & Yayata (Ummudilshad)*
_*•SPECIAL GIFT TO:-Tawar (Maman Kausy)*_
__________________________________*BABI NA SHA BIYAR♡*
___________________________________1️⃣5️⃣
_Last free page_
_______________
"Ya Zaid dama ashe kai ne wanda Abba yake shirin aura mun.?Meyasa.?meyasa zakui haka.?Ko Kun manta cewa ka tab'a shiga sahun maneman yar'uwata ne.?To wallahi ku sani bana yi, bazan tab'a baku goyon baya akan wannan abun kunyar ba, Allah azatona abu ne wanda zan iya shanyewa, ashe abunda ban sani ba al'amari ne wanda zaizo yasha k'arfina" Ta ida magana tana mai rushewa da kuka, Gabaki d'aya yaji kansa yayi wani irin girman gaske tamk'ar wanda aka azawa damin kaya, Fuskarsa ta bayyana tsantsar tashin hankali mara fassaruwa, Tuni idanunsa suka canza launi zuwa jawur don Zaid bai iya shiga tashin hankali ba Musamman in har akan 'ya mace ne.
. Kamar zai saki d'an marayan kuka yace"Zainab pls dan girman Allah karki mana haka, Ki sani babu haramun acikin aurena dake Tunda ban auri Najlat ba, ina dai amsa sunan maneminta ne ammh bata tab'a bani fuskar soyayya ba, dama nine kawai nake ta haukana, inata b'atar da Lokacina akanta, daga baya dana Lura da gaske ba sona take ba shiyasa na fita daga rayuwarta, Cikin hukuncin ubangiji sai ya had'ani da mace mai sona don Allah, Sunanta Harira, Yarinya nutsastsiya kamarki, ada bikinmu zai kama rana d'aya ne danasu Najlat ammh sai Allah ya dauki abinshi, Shekaranjiya take cike kwanaki goma sha bakwai da rasuwa, Zainab ina cikin halin ha'ula'i, Na had'aki da Allah karki karamun wani damuwar akan nada, ki taimaka ki karbi kokon barata agareki ki maye mun gurbin Harira, wallahi i love you Zeeyta, daga jiya zuwa yau kadai gabaki d'aya na rasa tunanina akanki, ga abokina can Junaid shine zai fi baki labari dak'yau."Hak'ika ta tausaya mishi kwarai da gaske da babban rashin da yayi, sai dai bata jin hakan zai sa tayi abunda yakeso, Karon farko arayuwarta tana neman watsawa Abbanta kasa a ido, Runtse idanu tayi wasu zafafun hawaye suka kwaranyo mata, Cikin k'aryewar murya take Fadin"Wallahi Tallahi Ya zaid duk kuyi hak'uri ammh bazan iya aikata abunda kukeso ba, in ku zaku iya had'o idanu da Najlat bazaku ji kunya ba, to ni zanji sosai harda ma na fitar hayyaci, Dan Allah na rok'eku kuyi saurin barin gidan nan don bani son Umma ko ita Najlat d'in su farga da abunda ke shirin Faruwa."
"Zainab karki watsawa Abbanki kasa a ido don karki so kiga yadda yake ta yabonki yace bazaki tab'a bashi kunya ba, so pls in ma so kike in k'ara miki Lokaci kiyi nazari zan ara miki ammh kar kice bazaki aureni ba don wani dalili naki mara k'arfi." Afusace tace"Allah babu wani nazarin da zanyi, amsar guda d'aya ce kuma shine bana yi." Azafafe shima yace"Zainab wai meyasa kika fiya taurin kai ne.?kwata kwata baki da Fahimta." Har ta bud'e baki zatai mishi masifa, da sauri ya Fuzgo hannunta ta fad'o cikin Falon babu shiri don so take ta daga murya har mutan gidan su Farga da halin da suke ciki.
**"Wai miye haka ne ka wani tattare hanya kaki bani wuri in wuce bayan kuma kai ne ina baccina hankalin kwance kazo ka tasheni wai surukaina sun zo gaishemu, ka bani wuri inje in gansu, inga ya kamanninsu yake ammh ka hana, wannan wani irin fitina ce haka.?Anya Habibu kodai kana da wata akasa ne dani.?" Ajiyar zuciya mai zafi ya sauke yana Fadin"Kiyi hak'uri so nake su d'an tab'a abun motsa bakin da aka kai musu kafin ki shiga don na sanki sarai zuwa zakiy ki sasu agaba har su kasa sakewa su ci abun kirki."Wani tsalle tayi ta diro ta gabanshi tana Fadi da kumfar baki"Ay lallai kam naga alama, wato ga mayya wacce zata lashesu ko.?dadin abun dai duk haduwarsa nasan bazai tab'a kama kafar Hassan ba, dallah bani wuri inje inga jememmen fuskar tasa."
YOU ARE READING
SAWUN GIWA...!🐘
Romance"Dallah gafara can malama, har ke kin isa ki mana abunda Allah bai mana shi ba? Akanki ne aka Fara irin hakan? Ko kuwa akanki ne za'a daina? Sai wani ciccika bak'in banza kike awurin kamar zaki iya tabuka abun kirki idan har mukayo gaba da gabanta...