09

162 4 1
                                    


♡ ♡
_*🐘SAWUN GIWA...!*_
_(The Elephant's Foot)_

_★For How Long Will The Elephant's Foot Be Radioactive?_

*FInd out💥*

*WATTPAD*➖ _HAFNANCY01_

*DEDICATED TO:-Mamina (Sis Nerja'art & Yayata (Ummudilshad)*

_*•SPECIAL GIFT TO:-Tawar (Maman Kausy)*_
__________________________________

*BABI NA TARA♡*
___________________________________

↗0⃣9️⃣

"Hajiya na had'aki da girman Allah ki dubi lamarin Wannan baiwar Allah Ummi tana matuk'ar buk'atar taimako, Ki tuna fa Allah madaukak'in sarki yayi alk'awari ga duk wanda ya tausayawa Mai rauni, Ko kuma wani marayan, to fa shima d'in zai taimaka masa sannan kuma ya taimakawa na bayansa, ga kuma tarin Lada mai yawa da zai samu, Annabi S.A.W yace _"Duk Wanda ya taimaki maraya to zasu kasance tare dashi acikin aljannah."_ Dan tsagaitawa Nana tayi da maganarta Tana 'yar Shesshek'a, Hajiya kuma Tagumi ta zuba Tana sauraron d'iyar tata, tausayin Ummi ne fal ranta, Allah ya gani Tana son taimakon nata ammh kwata kwata ta rasa ta ina ne zata ma Fara.Nana ce ta Sake yanke mata tunani akaro na biyu"Hajiya wlh Muna da halin taimakawa Ummi, domin kuwa in har munyi niyya muna iya dauke nauyin duk wani dawainiyarta daga yanzu har zuwa k'arshen Numfashinta, sai dai kuma ba irin Wannan taimakon kadai take da buk'ata ba, Tana buk'atar araba ta da Wannan gidan ne gabaki d'aya.Muddin ta cigaba da rayuwa acikinsa to fa bazata tab'a samun sukuni da kuma 'yancin rayuwa ba, Nasan tabbas zai yi matuk'ar wuya Abbanta ya maida ruk'onta Hannunmu har izuwa sanda zaku aurar da ita, Kai tsaye zai yi Tunanin ko muna ganin gazawarsa ne alamarinta, Mafita d'aya ce Hajiya ina addu'ar Allah yasa kiyi Na'am da ita."
Kallonta Hajiya tayi gami da cire Tagumi tana Fadin"Khadijah Wani irin Mafita ce kenan kika samo mana akan Baiwar Allah?" Wani irin Lallausar murmushi ta saki kan ta sauke ajiyar Zuciya tace"Mai zai hana ki had'ata aure da Yah Muhammad d'an gidan Kawu Musa?"
Zaro idanu Hajiya tayi Cike da mamaki Tana Fadin"Anya Nana kanki d'aya kuwa.?Wani Muhammad d'in zan bawa Baiwar Allah.?Ai ina jin gwamma da rayuwar da Take ciki ayanzu da Wanda zata je ta Fad'a agidansa."
"Hajiya Yah Muhammad fa sam sam bashi da Matsala, hasalima ma salihin mutum ne Mai sanyin Hali, duk macen da kuwa ta sameshi ta ciri Tuta wlh." Da sauri Hajiya ta tari numfashinta"Naji bashi da matsala ammh Matarsa fa.?wai ni kina abu sai kace Kin manta da halin Hajara ne, Tana da kafirin kishi sosai in har akan Muhammad ne, ko kuwa mantawa kikai ne da abunda ta tab'a Fad'a awani taron biki da akai.? Cewa fa tayi duk wata shegiyar da tayi gangancin had'a kishi da ita to fa Sai ta tabbatar ta zama abun zubar da k'walla awajen Mutane, Muhammad nata ne ita d'aya, Kuma kema kinsan shi Muhammad d'in yana tsananin sonta sosai, Kuma ko an matsa ya auri Baiwar Allah na tabbata bazai iya kwatanta adalci ba, Sosai Baiwar Allah zata cutu don tana da hak'uri sosai, Zata sha wahala kwarai da gaske ahannun Wannan mak'irar matar, Sabida haka Zancen Wani had'asu dashi bai taso ba don bazan tab'a baki goyon bayan ah turata inda zata sha wahala ba, garin neman k'iba asamo rama, Kul wlh bazan lamunta ba, maza ki kawo wata shawarar ammh Wannan binneta anan Tun wuri ban ma son Zancen yaje waje har yakai kunnen Matarsa." Wani wawan ajiyar Zuciya Nana ta sake Saukewa Tana mai girgiza kai don gaskiya Hajiya ta fad'a, Hajara bala'i ce, Sunanta Kadai masifa ce, Zuciyarr Fir'auna gareta, Tana iya aikata duk abunda ta fad'a in har akan kishi ne, kuri tayi da ido tana Kallon Hajiya ido cikin ido, Da magana abakinta ammh Tana tsoron yadda Hajiya zata karbeta don kusan yafi Wancan Muni, Ita kanta Hajiyar ta lura dakwai Sauran Magana acikinta Shiyasa tace"Nana yi maganarki, ina jinki karki ji Tsoro ko fargaba, in shawara yayi mun zan karb'a, in kuma bai mun ba, Zan hanzarta watsar dashi."
Wasa da 'yan yatsun hannayenta ta shiga yi gami da sunnar da kanta k'asa, Cikin rage murya Take Fadin"Hajiya Tunda kink'i ta Yah Muhammad, To me zai hana na bar mata Salisuna.?wlh idan har tayi mishi Ni zan hak'ura, burina kawai arabata da Wannan gidan, Wlh Ni nasan Ummi bazata sha wuya agidan Salisuna ba, Zai kular mana da ita yadda akeso, Zai sota zai kuma k'aunaceta, Ni zan zaunar dashi in Tunatar dashi Ladan da duk Wani mai taimako yake samu ayayin daya Ceto rayuwar Wanda yake Cikin matsin Rayuwa, Na tabbata Salisuna bazai bani kunya ba, zai Fahimceni sa'annan ya bani goyon baya don Yana son Farin cikina, Zanyi k'okari naga na sadaukar da abincin Zuciyata ga Zainab don nema mata Farin cikin data nema ta rasa Tun bayan Rasuwar mahaifiyarta." Ta k'arashe maganarta tana mai rushewa da Kuka mai tab'a Zuciya, da gani kasan ba karamin danne Zuciyarta take k'okarin yi da Wannan sadaukarwar ba.Jikin Hajiya ne yayi sanyi sosai, ga abun dariya ga abun Tausayi, Cikin dauriya Tace"Khadijah Tashi ki bani wuri, banson zancen banza, garin samawa Wani Farin ciki sai ke ki nemi kunsa wa kanki bak'in ciki.? In har ke zaki iya hak'uri, Shin kina ganin shi Salisun zai iya hak'ura dake ne.?Hakk'insa kikeso ashiga fa.?To billahil azimu ki kiyayeni, Kar ma ki sake inji kin masa Wannan zancen don ba karamin sab'a miki zanyi ba, Maza tashi ki bani Wuri, ba kece zaki nuna mun irin taimakon daya dace in yiwa yarinya ba, Dama kallonki kawai nake tayi don baka k'in ta yaro, Sai kuma naga baki da saiti, To daga yau ki zuba idanu kawai ki ga irin Taimakon da zan mata, karki sake ce mun kaza ne ya dace in yi mata don na ara miki Lokaci da kuma dama naki bada shawara mai k'yau ammh kwata kwata baki kan hanya."
Atak'aice dai sai da Hajiya Tayi mata tatass don maganar gaskiya bata ji dadin shawarwarin da ita Nanar ta kawo ba akan Taimakon Ummi.

SAWUN GIWA...!🐘Where stories live. Discover now