11

145 1 1
                                    

                ♡ ♡
_*🐘SAWUN GIWA...!*_
          _(The Elephant's Foot)_

 
_★For How Long Will The Elephant's Foot Be Radioactive?_

        *FInd out💥*
     

       *WATTPAD*➖ _HAFNANCY01_

  *°DEDICATED TO:-Mamina (Sis Nerja'art & Yayata (Ummudilshad)*
          
_*•SPECIAL GIFT TO:-Tawar (Maman Kausy)*_

__________________________________

              *BABI NA SHA DAYA♡*
___________________________________

               
                       1️⃣1️⃣

Can Gidan mai girma Shugaban k'asa ma haka abun yake, Ana bikin babban Sallah, ana sakkowa daga idi Manya-manyan mutane masu fada aji suko yo gidan shugaban kasa don mishi barka da Sallah.Wannan na shiga wancan na Fita, kuma kowanne baya Fita har sai ya cika Tumbinsa da kayan ciye-ciye.Su kuku babu duwawun Zama, a juya nan a juya can, Burinsu kawai su tabbatar kowa yaci yayi dam dashi.Dad bai Kubuta daga hannun mutane ba har sai yamma asannan ne ya samu Ganawa da iyalinsa dak'yau.

Ab'angaran Najlat kuwa bayan sun kammala girke-girken da za'a kai gidansu Hajiyar Abul, bata yadda Ummi ta mata rakiya ba kamar yadda dai akeyi, Kuma Umma ce ta K'ara zuga ita Najlat d'in tace karta sake Ummin ta bita.Haka taje gidan ita d'aya, Su Hajiya nata mamakin Zuwanta, ammh kuma ta wani Fuskar ba abun mamaki bane don ko dama can takan kawo musu ziyara a bikin Sallah.Anan ne taci karo da ya'yan yan'uwan Hajiyar, yawanci acikinsu magidanta ne don hadda ya'yansu awurin, Ciki hadda Yah Muhammad d'an gidan Kawu Musa wanda Nana taso a had'ashi da Ummi, d'a ne ga Wani wan Hajiya.Wasu basu san Najlat ba kasancewar bata bawa Abul damar Zagayawa da ita don asan Juna ba.kanta aduk'e tana latse latsen wayarta, Sai Wani shasshan k'amshi take musu, Kuma Tunda ta duk'a bata sake kallon inda suke ba.Nana ce take musu bayani, Wani Usman d'a ga k'anwar Abbi yace"Ke haba yanzu matar da Coach Hassan zai aura kenan.?Shine take gayar damu daga can a tsaye bata matso Kusa ta bamu girmammu na yayun miji ba.?" Ya ida magana cike da Zolaya yana Kallon inda take Zaune, dake Kusan dukkansu awurin sun girmi Abul, mutum d'aya ne kawai shi Abul d'in ya bashi shek'aru.Yah Muhammad ya daga Murya yadda zata ji shi Sosai yace"Ai ni Rashin kunyarta ne yasa kwata kwata bata Kwanta mun arai ba don Kwarai na shaidata Tun shigowarta kune dai baku san dawan garin ba, Kwanaki da hanya ta biyo dasu ta wajajenmu ita da Coach d'in, Sosai naji mamakin yadda Take ta wani shasshan k'amshi, Hajara ma na mata magana dak'yar Take amsawa, shi kansa Hassan he wasn't comfortable with her, sabida d'an nazarin da nayi na Lura kamar yana gudun b'acin ranta, anan na gane cewa shigowa gidan ma dak'yar ta yadda ta shigon, watakila don bata da yadda zatai shiyasa ta bishi suka shigo.kaii kuma Usman kana ma maganar girmama yayun Miji anan, Ka duba ita Uwar mijin Kankat kenan ka ga ta durk'usa ta gaisheta dak'yau.?gaisuwa irin ta surukuta.?Hajiya ko Tayi.?"

"A'ah Muhammad kubar maganar nan ban son Fitina da tashin hankali, babu Ruwanku, Karku Kunna gobara ana zaman zaman lfy, Ni ban san meyasa ma kuka bi kuka dorawa kanku jaraban son girma ba, aganina Huwallahullaziy la'ilaha illaa huwa shine kadai yafi cancanta da'a bawa girma don shi d'in Al-mutakabbir ne (Mai girman girma), ammh ba Mutum ba, Gargad'in k'arshe nake Muku ni banson cin fuska ku fita a harkarta."Azuciye Yah Muhammad yace"Haba Hajiya adunga sara ana duban bak'in gatari mana, girma na Allah na daban ne, haka ma na iyaye daban yake, girmama surukai kamar k'yautatawa ce, Ki bari mu fad'a mata gaskiya don bazamu dauki Wannan rainin acikin Zuri'ar nan ba, Ya zama dole ta sauya Taku tun kafin ta shigo don muddin bata canza ba akwai matsala fa agaba."

Najalat Wacce ta kasa kunnuwa tana ta sauraronsu zuciyarta nata tafarfasa, afusace ta mik'e Cike da Rashin kunya tace"To Mal.Muhammad ka rik'e gaskiyar taka bana so, Kuma insha Allah bazan samu wani matsala a gidan aurena ba, Sai dai kai ka ga matsala da matsaloli a gidan naka auren, Nana ga abinci nan zoki dauka, Hajiya Ni na tafi sai anjima."Tana gama fad'in haka tasa kai tabar Falon kowa ya rakata da Kallon mamaki da al'ajabi, Afusace Yah Muhammad ya mik'e zai bi bayanta yana banbami"Kun ga irinta ko.?ko kun ga abunda nake hangowa.?Shegiya fitsararriya wlh da'ace ina da iko akan Hassan ne sai na hana ya auroki, ammh bari ya dawo sai na zugashi yasa adaga bikin ki koyi hankali Tukun, in kuma kin kasa koya sai afasa period." Ai kuwa karaf acikin kunnenta, tace itama a zuciyen"In kai ne Ubansa sai kasa ya fasa auran nawa, banza Lusari kawai." Kalamanta suka sake harzuk'a shi, k'ok'arin bin bayanta yake, Usman da Wani Yakubu suka yi saurin mik'e wa suka ruk'o shi, Usman yace"Haba Muhammad wlh ba girmanka bane tsayawa kana musayar yawu da 'ya mace, macen ma wacce Take shirin zama matar k'anin baya bayanka, wlh duk ni ne ya jawo Wannan tashin hankalin dana soma tsokanarta, in ba haka ba ai da abun bai kai ga haka ba." Hajiya ta mik'e zata bi bayanta Tana fad'a"Kun ga abunda nake ta gudun Faruwarsa kenan ko.?wlh kun cika Fitina ni ban son yaushe ka zamo haka ba Muhammad, dama ya lafiyar giwa bare tayi hauka.?a wuyanta take kiris take jira, Muna d'an lallabawa,da dadi ba dadi haka muke tafiya don ance Zaman duniya sai hak'uri ammh ku ya'yan yanzu sam bakwa ganewa.Nana yi maza ki tsayar mun da ita kafin tabar gidan, bari na sako hijabi in roketa."

SAWUN GIWA...!🐘Where stories live. Discover now