Zuri,a daya part 19

567 62 5
                                    

*ZURI'A ĎAYA*!💧💞

Maryam Abdullahi(Oumramadan)
Whattpad@OumRamadan1

©Hikima Writers Asso
(Home of peace, joint of entertainment to educate nd enlighten our readers)

*19*




Weeding gown ko wacce tasa ta neela ja ta mufyda coffee yazid wata gizna yasa fara kall sai shek'i take da tashin kamshi,
  Mota d'ayace ta d'aukesu ta irfan,  yazid a tsakiya neela acan karshe mufy kuma a farko, gaban motar kuwa matar irfan ce amna tana zaune da dan karamin cikinta daya fara tasatawa taci ado da wani lace mai azabar kyau,
Hall d'in cike yake taff da abokan ango da kawayen amarya, a kofar shiga aka suka tsaya aka sasu a tsakiya inda mujahed da hassana suke a farko sai faisal da budurwarsa, sai kuma irfan da amna,
  Suna shiga hall din ya cika da ihu a tare suke taka step step din har suka karasa mazauninsu,  irfan ne ya fara bude taro da addu,a kafin ya bada takaitaccen tarihin ango,
  Hassanace ta taso a matsayin aminiyar neela itama ta bada takaitaccen tarihin ta,
  Sai kawar mufy meela cike da iyayi da yanga ta ringa kuranta mufy da yadda ango yake bala,in sonta kafin ta koma mazauninta ta zauna,
   Mc ya bukaci ango da amare su yanka cake su ciyar da junansu , a tare suka mike yazid ya bude farin kyallen da aka rufe wukar da ita ya yanko cake din, ta gefen ido ya kalli neela data turo baki ,ya waiga ya kalli mufy data tsaresa da ido tana masa wani kallo,
  Drinks ya tsiyaya a wani cup me kyau had'e da cake din a hannunsa ya nufi bakin neela, kafesa tai da ido ta turo baki, ya had'e rai yana hararta in ba,a kusa kake ba saika rantse kallan so sukewa junansu, a hankali ta bude bakin ya bata cake din sannan ya zuba mata drink,
  Karba tai itama hannu na rawa ta kasa rik'e cup yadan janyota kadan cikin rada yace "in baki nutsu ba sai ranki ya baci er kauye kawai, so kike ki badani a gaban abokaina"
  Ta turo baki cike da jin haushin abinda yayi mata ta yanko wani katon cake saida ya bude baki kawai sai ji yayi ta shafe masa cake din a fuska, take hall din aka saki wani uban ihu, wani kallo ya mata sanda take bashi drink din tana masa dariya kasa kasa,
  Wukar ya sake karba ya juyo wajen mufy da saura kiris zuciyarta ta buga ,murmushi ya sakar mata ya nufi bakinta da cake din ,hannunsa ta rike cike da son ta turawa neela haushi ta janyosa jikinta saida tasa masa cake din a baki kafin takai bakinta Kan nasa ta gutsiri cake din, sosai aka shiga ihu da sowa ,neela tabe baki tai daganan mc ya bukaci ganin ango da amare a tsakiyar hall din ,
  Fitowa sukai inda hamisu breaker yasa musu wakar jarumar mata,  hadiza tadan sunkuyo wajen neela tace "lilsis pls kidan taka ko yayane karki bamu kunya kinji"
  Kamar zatai kuka tace "nifa gsky aa taya zan iya rawa a nanan?"
  Bata fuska hassana tai tace "ALLAH lilsis zamuyi fada ba rawa zakiba kawai juyawa zaki kin wani tsaya kikam kamar doki"
   Ta turo baki a hankali ta shiga taka rawa tana juyi tuni kallo ya koma kanta aka shiga yi mata ruwan liki, yazid wani mugun kallo yake aeka mata dashi sanda yaga gaba daya maza sun koma kanta ana liki, 
  Shagali akai sosai kafin a tashi daga taro,Kamar yadda suka zo haka suka koma , a compound din gidan aka ajiyesu ko wacce aka maidata Part d'inta,
  Mujahed ya kira hassana su fito a maidasu gida, ya kalli sauran en uwanta tai musu alama da ido suka mike,zumbur neela ta mike hankali tace tace "ina zaku?"
  Cikin tausayinta hussaina tace "akwai sakon da zamu karbo a waje yanzu zamu dawo"
  Tai raurau ido hawayen harsun fara zuba tace "to dan ALLAH karku dade tsoro nakeji"
  Kasa magana sukai dan suma gab suke da fashewa da kuka suka fice, neela tun tana sa ran zuwansu harya fidda rai wani irin kuka take me raba zuciya ta kudundune jikinta a can karshen gadon,
  Ango kuwa yana waje ana fafatawa dashi ya rufe ido yace sam ba wanda zai rakasa wani siyan baki, "siyan baki ki siyan raini"
  Yace yana hararsu, bude baki faisal yayi yace "yazid wa ka taba gani daran farkonsu ya shiga shi kad'ai ba tare da abokan saba?"
  "Za,a fara ta kaina"
Yace yana karbar ledojin dake hannunsu, yadan daga murya yacewa me gadi "mal musa insun fita ka tabbatar ka rufemin kofa"
  Daga haka ya juya yayi tafiyarsa yanajin suna masa iskanci yai banza dasu, yana shiga ya saki wata ajiyar zuciya yana huro zazzafar iska daga bakinsa,
   Tsayawa yayi a corridor din dazai sadaka da kowane part sai da yaja wasu seconds kafin ya tura kofar part din mufy,
  Wani sassanyar kamshi ne ya daki hancinsa ya lumshe ido yana shakar kamshin, leda d'aya ya ajiye a kan center table d'in daya gani a parlour kafin ya nufi kofar da yake kyautata zaton tana ciki,
   Yana tura kofar ya ganta zaune a gefen bed ta cire lullubin dake kanta,dago da kanta tai suka kurawa junansu ido ,cikin nutsuwa yake takowa dakin yana karasowa kusa da ita ya rumgumeta tsamm a jikinsa yana shakar kamshin jikinta,sun jima a haka kafin ya saketa a hankali yace "ba wata matsala ko?"
  "Saita kewarka" tace tana masa fari, ya mata wani kallo yace
"Nasan yanzu a gajiye kike ki shiga ki gasa jikinki da ruwan dumi "
  Ya ajiye mata ledar  daya shigo da ita akan drower ,sai da yaga ta shiga toilet sannan ya fita daga dakin ,ya kashe komai na parlourn sannan ya nufi bangaren neela,
   Mufyda koda ta fito bata kawo komai a ranta ba dan tayi tunanin wanka yaje yayi, shiryawa  tai cikin sleeping dress masu azabar kyau ta mulke jikinta da humrori masu kamshi ta sake gyara gashin kanta karamin hijab tasa ta zauna tana jiran shigowar yazid,
  Akai akai take kallan agogwan da yake makale a bedroom din lokaci zuwa lokaci tana sakin tsaki, ranta ne ya fara baci sanda taga yazid ya kwashe awa 2 bai dawo ba,
  Tuni kirjinta ya fara suya idanunta suka kad'a sukai jajur ta fara zubar da zazzafan hawaye ,"kar dai ace honey pie yana wajen waccan abar ? Wata zuciyar tace mata ",anya kuwa me zaije yi wajenta bayan ba sonta yake ba?" 
  "To inbaya can yana ina"
Ta sake yiwa kanta tambayar hawaye na ambaliya a fuskarta, fita tai daga bedroom d'in ta leka duk dakunan dake parlourn bataga gansaba, a haukace ta dawo dakinta tana sakin wani rikitaccen kuka me hade da tsantsar kishi da tashin hankali.

Zuri,a DayaWhere stories live. Discover now