Zuri,a daya part 29

742 66 2
                                    

*ZURI'A ĎAYA*!💧💞

Maryam Abdullahi(Oumramadan)
Whattpad@OumRamadan1

©Hikima Writers Asso
(Home of peace, joint of entertainment to educate nd enlighten our readers)

*29*





Sai wuraren 2 saura neela ta farka da salati a bakinta a hankali ta shiga ware manyan idanunta tana karewa inda take kallo, zura da kafafunta tai ta mike jitai jikin nata ba kamar daba duk da har yanzu tanajin zafi a wajen,
   Bedroom d'inta ta shiga  ta cire gown din dake jikinta ta shiga wanka sai da ta sake gasa kanta kamar yadda dr Khadija ta koya mata sannan tai wanka a tsanake ,tana fitowa ta tada sallah bayan ta idar ta cire hijab din gaban dressing mirror ta tsaya ta shafa powder sai lipglos kalan pink ta taje girarta bayan ta mulke jikinta da humra da bodyspry ta tsaya gaban wardrobe tana bin kayan ciki da kallo ta rasa wanda zata dakko ,karshe dai ta dakko waya atamfa da akai mata dinkin riga da sket sosai kayan suka amsheta bata daura dankwali ba sai kawai ta tufke gashin kanta bayan ta gyarasa da mayuka masu kamshi, fitowa parlour tai cikin dauriya ta gyara ko ina duk daba wani datti yayi ba,
  Yazid kuwa gaba daya hankalinsa nakan neela duk lbr da mufy take basa  baya fahimta akai akai yake duba agogon hannunsa wayar mufy ce tai kara tana dubawa tana ummintace da murmushi a fuskarta tace "honey pie ummi na kira "
  Daga haka ta tashi da sauri ta shige bedroom d'inta, wata ajiyar zuciya ya sauke ya dauki wayarsa shima ya nufi part din neela ,ita kuwa bayan ta kammala gyara gidan hadin fruits dinta ta dakko a hankali takesha duk da bataji dadinsa kamar daba tanasha ne kawai sbd yunwar da takeji, can kasan mak'oshi yayi sallama ,sau ďaya ta kallesa ta sunkuyar da kanta dan wata matsananciyar kunyarsa datakeji, shigowa yayi ya zauna kusa da ita a hankali yace
"Ya jikin?"
"Da sauki"  tace cikin sanyin murya,  shiru yayi na en mintuna yadan kalleta ta gefen ido ganin sai juya cokali take a cikin bowl din yasa ya karba ya janyota jikinsa a hankali ya debo fruits din yakai bakinta kamar zatai kuka ta dago ta kallesa ta girgiza kai, hade rai yayi yace "bude bakin Kona miki abin jiya" 
  Da sauri ta bude tun kafin ya k'arasa, ya gimtse dariyar da take cinsa a hankali yake debo fruits salad din yana bata sai da yaga tana niyyar yin amai sannan ya rabu da ita,
  Karbar bowl din tai duk da gabanta yana dukan 3 katya dizgata haka ta daure ta debo fruits din takai bakinsa ,kafeta yayi da ido yanajin wani irin nishad'i da farin ciki yana shigarsa gaba daya mamakinta yake, ganim yaki bude bakin yasa ta dago da kanta kamar zatai kuka ta saci kallansa taga ita yake kallo hannunta ta janye cike da sanyin jiki hawaye na zubowa daga idanunta, da sauri ya rike hannun yana kallan yadda hawayen suka fara sauka a fuskarta jiyai sam baiji dadi ba hannun ya kama dake rike da cokalin yakai bakinsa lumshe ido yayi sanda yakai fruits din bakinsa ,
  Janye hannunta tai tana turo baki ,kallanta yayi ya langwabar dakai yace "acigaba da bani mana everlasting "
  Rufe ido tai cikin jin kunya ta tura baki ,ya danyi murmushi yace "Kodai saina kira miki hajja ne danfa jiya naji kinata kwala mata kira wai tazo "  kukan shagwab'a ta fashe dashi tana sake boye fuskarta a jikinsa, yadan hade fuska yace "nifa banason wannan rufe rufen idon kamar daga ruga kika fito"  ta hade rai tanajin ranta yana baci idan ya kirata da  er kauye, shi kuma yana hakane duk dan ta daina nuku nukun da take ta saki jiki  yana kula da yanayinta kuma yasan maganar na mata zafi,
  Karbar bowl din yayi yace "tunda baza,a baniba ni bara nasha"  shiru tai batace komai ba shima bai sake magana ba ya shiga shan fruits din sai da kusa shanye wa sannan ya ajiye bowl din ,
  "Kinajin yunwa ko"
Yace mata sanda ya janyota jikinsa yana shafa cikinta da yake plate ,ajiyar zuciya ta sauke jin yadda yake mata wani irin abu tsigar jikinta ta fara tashi ta lafe a jikinsa ta ringa lumshe ido tanajin dadin yadda yake shafa mata ciki,
  Mufy kuwa tana shiga ta ďaga kiran hajja falmata cikin doki tace "I miss u ummi"  ta k'arashe tana zama a bakin bed dinta ,
  "Nima haka Daughter ykk ina sirikina na,komai dai lfy ba wata matsala ko"
  "Lfy lau ummi "
"To masha ALLAH, ince dai ba wata matsala ko ta wajen waccen yarinyar"
  Mufy da kamar jira take a tabo mata inda yake mata kaikayi ta sheke da dariyar mugunta tace "ae in fada miki ummi ko kallo bata isheshi ba a takaicema bai dauketa a mace ba dan ko zama bai cika yi a part dintaba lallai na gamsu ummi baby bayason wannana abar kawai biyayya yayi ni yanzu ma tausayi take ban bakiga yadda yake daukin zuwa wajena ba "
Dadi uwa ya kashe hajja falmata yarinyarta na cikin farin ciki ,dariya tai tace "ah ae na gaya miki Daughter kice kikaki kwantar da hankalinki kina nema kisawa kanki damuwa akan wata can daban ji nake da kanki kika fadamin bai sonta indai kin dauko mu to bazaki tana zama Bora a wajen miji ba "
  Mufy ta sake fashewa da dariya tace "ALLAH ummi na yadda da zancenki sosai kawai ni abinda yake damuna zamanta a gidan inna tuno hakan zuciya sai naji kamar zatai bindiga"
  "Banda abinki  Daughter ina ruwanki da zamanta a gidan nidai ki rufamin asiri kinji dai abinda dr ya fada akanki so nake nan da shekara inga jikokina "
  Hajja falmata tace cikin farin ciki, mufy ta rufe fuska tace "kai ummi"
Dariya hajja falmata tai tace "ae gskyne ke kadai nake da ita kaf duniyarnan zanfi kowa farin ciki na ga jikokina "  
"To ummi daddy fa" 
"Bayanann bauyi wayaba "
"Eh nakirasa bata shiga amma anjima zan sake kira"   hajja falmata tace "to shikkenan ki gaidamin da yazid din"  daga haka sukai sallama fitowa tai ta dudduba bataga yazid ba "honey pie "  ta shiga kwala masa kira tana duba dakunan dake parlourn, ta leka window tana motarsa tananan ,fita tai daga part dinta ta nufi part din neela,
  Shi kuwa yazid daga shafar ciki samun kansa yayi da kissing dinta slowly  yana shafa jikinta jin  bakinta yake tamkar sweet a wannan yanayin mufy ta taddasu sbd nisan da sukai sam basuji sanda ta shigo ba ,tsaye tai tana kallansu kamar hoto tana girgiza kai kirjinta yana zafi jikinta ya shiga karkarwa wani uban ihu ta fasa ta zube a wajen,
  Da sauri yazid ya d'ago zaro ido yayi ganin mufy kwance ba alamun numfashi a tattare da ita a 360 yazo inda take cak ya dagata ya fice da ita zuwa part d'inta,
  Neela tai zaune tana kallan ikon ALLAH bakin ciki haushi kamar yayi mata tabe baki tai tanajin kamar tai kuka dan takaici taja wani siririn tsaki ta gyara kwanciyarta akan kujera,
  Shi kuwa yazid akan doguwar kujera ya kwantar da mufy ruwa me sanyi ya dakko ya watsa mata a jiki ,wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke tanabin inda take da kallo kafin ta kalli yazid daya daure fuska tamau tace "honey pie mafarki nake ko gaskene? Kai nagani bakinka cikin na wannan yarinyar" 
  Ya sake daure fuska tamau yace "inaga sai dai mafarkin kikai, ni bansan meyasa kika cika zargi da korafi ba yakamata ki ringa sassautawa kanki"
  Wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke ta kamo hannunsa hankalinta a tashe yadda taga ya koma mata kamar yazid din da tace "kayi hkr honey pie ina tunanin mafarkin nai wlhy bakaji yadda naji ba kai nagodewa ALLAH dayasa mafarkine kar ALLAH ya sake nunamin irin wannan mummunan mafarkin dazai iya zama ajalina"
  Yazid kallanta ya ringayi cike da mamakinta sai dai ko kadan fuskarsa bata nuna haka ba saima kuma hade rai da ya sake yi.

Zuri,a DayaDove le storie prendono vita. Scoprilo ora