Zuri,a daya part 37

630 56 9
                                    

*ZURI'A ĎAYA*!💧💞

Maryam Abdullahi(Oumramadan)
Whattpad@OumRamadan1

©Hikima Writers Asso
(Home of peace, joint of entertainment to educate nd enlighten our readers)

*37*





Ganitai bedroom d'in bai wani datti ba dan haka sai kawai ta wuce kitchen ta tadda me aekinta tana goge goge,jikin tane ya fara rawa tunda mufyda ta shigo,
  Mufyda ta kalleta ta saki wani murmushi fuskarta har wani annuri take tace"hansatu meye na rawar jiki kamar kinga wata dodo"
  Hansatu ta dinga kallanta cike da mamaki, mufy ta sake wani murmushin tace "gyaramin kayan miya,kuma ki daina rawar jikinnan kinji"
  A sanyaye hansatu ta gyad'a mata kai ta gyara mata kayan miya karba tai da kanta tai blanding dinsu ta hada lafiyayyiyar soup da taji nama ,ta dafa shinkafa ta hada cowslow hade da lemon kwakwa, fita tai tabar hansatu tana gyara kitchen din cike da mamakinta, 
  Gyara parloun tai tsaf duk da gajiyar da tai dan komai tana yinsane cikin karfin hali dan jitai cikin nata yayi wani kasa sosai, bedroom din yazid ta koma ta gyarasa tass ta wanke toilet din ciki zama tai dirshan a kasa tana maida numfashi dan ba karamar gajiya taiba ,ta kalli agogo taga biyar saura tasan nan da 1hour yazid zai dawo dan yau girkintane, drower ta bude ta gyara komai ta fito da littattafan da suke ciki ta gyarasu ta maida wani pic ne taga ya fad'o a cikin wani hadadden diary ,
  Hoton ta dauka ta tsura masa ido gabanta na dukan uku uku ta dinga kallon kyakkyawar yarinyar da batafi shekara 2 ba yana sanye da wata gown me kamada net an gyara mata gashin ta da yake shek'i tana murmushi aka dauki hoton ,mufyda ta mikar da kafafuwanta da suke rawa ta ajiye hoton tana juya diaryn dake hannunta ta ,bude diaryn tai taga an rubuta ,"tun bakisan kankiba nake sonki aysha,da farko na dauka son da nake miki na en uwantaka lokacin dana girma na fahimci son da zuciya take miki ya zarta na en uwantaka,ya ALLAH kai ka jarabceni da son aysha ALLAH ka mallakamin ita a matsayin matata"
  Gumine ya shiga tsatstsafowa mufyda zuciyarta ta shiga tsintsinkewa ga wani irin sanyi da da taji yana ratsa bargonta, ta runtse ido ta sake bude wani shafin ,taga an rubuta "kece mace ta farko dana faraso aysha ,zuciyata batada wajen da zata iya ajiye wata mace inba keba ,"      jikintane ya fara rawa ta kasa cigaba da karantawa hotunan dake ciki ta dakko ta dinga kallo idanunta jajur tamkar garwashin wuta, hotunan karamar yarinya take kallo kwata kwata ta kasa gane wace sai dai tana mata kama da wata ,wani hoton ta gani dayasa dan cikinta hautsinawa ta bude baki sanda tai tozali da neela tana sanye da riga da sket en kanti kanta ba dankwali sai kananun kalba da akai mata tana dariya daga can gefe ta hango wata mata wacce suke tsananin kama da neela ,
  Lokaci d'aya taji mararta tayi wani irin kullewa,  duk da azabar da takeji cikin zuciyarta da mararta haka ta daure ta cigaba da kallan hotunan,girgiza kanta ta shiga yi da sauri ta juya bangon diaryn taga lallai na yazid ne dan ga full name d'insa nan a jiki,
   Watsi tai da diaryn  hotunan suka tarwatse ta ringa binsu da kallo kamar wata tababbiya tana girgiza kai , yazid kuwa  da wuri yau ya taso daga office ,yana zuwa gida yayi parking din motarsa ya kwaso ledojin daya shigo dasu
  Wajen neela ya fara shiga ya tarar da ita zaune Kan lallausan carpet d'in parloun ta mike kafatunta da suka kumbura tana duba littafin azkar,  murmushi suka sakarwa juna ya karaso inda take sai da ya shafa cikin sannan ya kalleta cike da tausayi dan ba karamar wahala take shaba yace "ya jikin naki everlasting "   a hankali tace masa "da sauki"
  "Edd ya kusa cika insha ALLAH kin kusa ki huta babyn nan yana wahalar min dake"  tai murmushin yake dan ita kadai tasan me takeji ,ya ajiye mata ledar daya shigo da ita bayan ya sakar mata kiss ya wuce part din mufy,
  Tunda ya shigo yake lumshe ido sbd wani daddadan kamshin girki dana turaren datai ya gauraye parloun ya ringa wurga ido yaga ta inda zata bullo, ajiye ledar yayi ya shiga kwala mata kira "beauty love " 
Shiru yayi still can ya wuce bedroom dinta bai gantaba ya duba bathroom bata ciki,  nan da nan hankalinsa ya fara tashi ya fito ya duba dayan bedroom din shima bata ciki,hankali tashi ya bude dayan bedroom din,
  Wani mummunan fad'uwa gabansa yayi,still yayi yana kallan mufy da take raba jajayen idanunta akan carpet din dakin tanabin hotunan da kallo tana girgiza kai,
  Jiki a sanyaye ya karaso ya zube a gabanta cikin matsanancin tashin hankali, mufyda ta d'ago idanunta da sukai jajur har sai da yazid yaji wani bala,in tsoron yadda yaga idanunta cikin rawar jiki dana murya ta shiga cewa ,
  "No yazid dan ALLAH kacemin ba kai bane yazid din da nake tunani,kacemin karyane yazid pls,kacemin mafarki nake ,"
  Lokaci ďaya yaji wani hawayen tausayinta ya rufesa ya ringa girgiza mata kai ya kasa magana sbd yasan bazai iya karyata abinda ta gani ba haka baisan wace amsa zai bata ba,  kallansa ta dingayi kirjinta yana wani irin zafi dabai taba mata irin haka ba wannan karan kamar zautacciya ta shiga magana tace "bantaba sanin inada mahaukaciyar zuciyaba sai yanzu da zuciyata ta kasa ganomin aenihin abinda kake so yazid,ban taba sanin nidin banza bace sai yanzu dana kasa tsayawa na fuskanci wanene kai barantana na gano abinda ke zuciyarka,hakika na kasance mara tunani da kishi ya rufemin ido na kasa gane gsky zuciyata ta yaudareni ta zalunceni idanuna sun makance akan kaunarka banaji bana gani akanka ashe haukan banza nake yazid baka taba sona ba neela kake so?,meyasa ka yaudari zuciyata ka kasa sanar dani sirrin zuciyarka ka barni inata hauka ni kad'ai?"
  Girgiza mata kai yake yana rike da hannunta ya bud'e baki zai magana ta d'aga masa hannu ta yunkura dakyar ta mik'e, ya wani irin zaro ido cikin matsanancin tashin hankali yakebin jinin da yakebin kafar mufyda, zumbur ya mike ya shiga kiran sunanta ,bata ko kallesa ba ta fice daga part din cikin tsananin azabar da takeji cikin mararta da zuciyarta,
   Ta murda handle d'in kofar yana biye da ita hankali tashe yake son dakatar da ita amma tuni ta shige zaman dirshan yayi a kofar cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali,
   Mufyda kuwa tana shiga first abinda ta fara tozali dashi katon cikin neela daya linka nata girma ,   ta zazzaro ido jikinta ya ringa wani irin rawa ta d'aga hannu tana nuna neela kirjinta yana wani irin ciwo da zafi,
  Baki ta bud'e zatai magana wani irin tari ya sarketa ta ,durkushe a  wajen tuni ta fara aman jini ga wani bala,in ciwo da kirjinta yake,
  Neela ta zaro ido tana kallan mufy ganin irin aman jini da take ta fasa wani irin ihu ta mike da kyar ta karasa wajenta,  daidai lokacin yazid yashigo sbd ihun daya jiyo,
  Jikinsa ya fara wani irin rawa da mugun gudu ya tare mufy da tuni ta fice a hayyacinta jini ya balle mata ta baki data kasanta ,wata nakudar azabace ta tasowa mufy ta ringa juya kai cikin fitar hayyaci gashi tanason magana amma ba hali sbd jinin da yake fita ta bakinta ,yazid bai taba shiga tashin hankali irin na yau ,ya tallabo mufy jikinsa hawaye na zuba daga idanunsa,
  Da kyar ya kinkimeta da sauri ya fice zuwa parking lot ya bude bayan motar ya sata jikina na rawa ya balle murfin motar ya shiga ,da gudu yaja motar ganin neela taba tahowa sbd yasan zuwanta Karin wani tashin hankalin ne,
  Neela ta durkushe a wajen ta fashe da kukan tausayin mufy sai da ta gaji dan kanta ta mike a sanyaye ta shige part d'inta.

Zuri,a DayaWhere stories live. Discover now