Zuri,a daya part 38

663 63 9
                                    

*ZURI'A ĎAYA*!💧💞

Maryam Abdullahi(Oumramadan)
Whattpad@OumRamadan1

©Hikima Writers Asso
(Home of peace, joint of entertainment to educate nd enlighten our readers)

*38*

*FAGE DIN NAKUNE MASOYAN MUFYDA*


Cikin mintina kalilan ya isa hospt din sbd tsananin gudun da yake ,lokaci d'aya manyan likitoci suka  rufu akan mufy sbd ceto ranta da abinda ke cikinta,first jinin da yake zuba daga jikinta suka fara kokarin tsayarwa duk yadda sukai tunanin matsalar ta wuce nan sbd nakudar data taso mata ganga ganga ga kuma jininta da yayi mugun hawa ,
  Banda yarfe gumi ba abinda suke sbd numfashi ma mufy bata iyasa ,oxygen aka manna mata a hanci ,  can gida Maiduguri kuwa ummi ce ta kalli dad din mufy cikin sanyin jiki tace "yallabai gabana faduwa yake tun dazu gashi inata kiran Daughter amma bata picking call dina" 
Abba ya kalleta yace "ki tai mata addu,a insha ALLAH ba wata matsala"   jinjina kai kawai  ummi tai badan ta amince da maganar saba,
  Neela kuwa tunda ta shiga ta zube a parloun ta dinga rusa kuka numfashinta har wani sama sama yake miss call 10 taiwa yazid bai picking ba,ta share hawayenta cikin tsananin tashin hankali da tausayin mufy ,Zata iya cewa tunda take da mufy bata taba yunkurin cutar da itaba hasalima ba zuwa part dinta take ba illa bakin kishin da take dashi akan yazid ,yes yazid yakai ayi kishinsa sbd ALLAH ya yaishi namiji mai iya soyayyar tsayawa a rai ko ita tanajin matsanancin kishin mufy daurewa kawai take coz ita tanada hkr da kauda kai,  wayarta ta sake dauka ta sake dialing d'in number yazid still bai dagaba, ta lalubo number daddy bugu 2 yayi picking yana d'agawa ta fashe masa da kuka,
  Hankalin daddy ya tashi yace "mamana wane abun ne ya faru?" Cikin kuka tace "daddy aunty mufyda ce ba fada lfy yaya ya fita da ita kuma tun dazu nake kiransa bai d'aga ba"
  Mikewa daddy yayi yace "to meya sameta"
"Daddy jinine yake zuwa ta bakinta da hancinta"  tace tana sake fashewa da kuka,salati daddy ya saki ya kashe wayar ya lalubo number yazid sai da yayi masa 5 miss call yazid ya d'aga murya a shake ,daddy yace "son kuna wane asibitin?"
  Yana fad'a masa ya kashe wayar ya kalli mummy da jikinta yake rawa yace "kwantar da hankalinki ba wata matsala taso mu tafi"  mikewa tai hankali tashe suka shiga mota,
  A bakin room d'in da mufy take suka tadda yazid kansa a sunkuye, daddy ya d'afa kafad'arsa cikin sanyin jiki ya dago,daddy ya rikosa da kyau ganin yadda idanunsa sukai wani irin ja sai fidda wani irin huci yake ,mummy kuwa tuni ta fashe da wani irin kuka ta dinga kallan yadda likitoci suke shige da fice akan mufy dan har yanzu suna kanta sun kasa shawo matsalar ,
  A fusace wani dr ya fito yace "waye mijinta?"
Yazid ya kallesa batare dayace komai ba,dr yace "kai wane irin mijine kasan yanayin jikin matarka amma ka kasa bata kulawa abu Goma da ashirin ga ciwon zuciya gashi jininta yayi mugun hawa munaso muyi mata cs sbd mu ceto abinda ke cikinta amma ba hali dan batazata iya haihuwa da kanta ba sbd numfashi ma bata iyayi dole mu jira jinin jikinta ya sauka shin bakason tane ka aureta"
  A fusace yazid  ya fizgosa yana huci yace "karka gayamin ba dadi bana sonta zan auretane, kai mahaukacin inane bakasan ALLAH ne me dorawa bawa cutaba,zaka kulamin da mata ko fada zaka samu gaba kanayi"  ya k'arashe yana daka masa wata tsawa,daddy dakyar ya banbare dr daga hannun yazid sai huci yake, mummy kuwa zubewa tai a wajen tana ihun kuka ,daddy banda salati ba abinda yake ya kalli dr yace "yanzu likita meye abinyi"
  Yana gyara kwalar rigarsa dan ba karamin shaka yasha a wajen yazid ba cikin shakakkiyar murya yace "addu,a kawai zakuyi" daga haka ya koma dakin yana sauke numfashi, zubewa yazid yayi a wajen ,yayi zaman dirshan yana hawaye ba shakka duk abinda ya samu mufy laifinsa ne duk iya kokarin da yake karta gano abinda ke boye sai da ta binciko,
  Mummy Kallan wayarta tai da take ringing jiki a sanyaye ta daga dan batajin zata iya boyewa falmata halin da yarta take ciki,tana dagawa cikin kuka tace "falmata mufyda bata lfy "  ummi ta fashe da kuka tace "na shiga uku ni falmata meya sameta"  mummy bata samu damar bata amsa ba ta kashe wayar ,daddy yace "haba ameena ya zaki kirasu a darennan ki daga musu hankali kinsan ba kusa suke ba barantana su taho"  cikin kuka mumny tace "ka barni kawai Alhaji ka duba kaga halin da yarinyar nan take ciki ace na kasa sanar da iyayenta halin da take ciki"
  Daddy baice komai sai tagumi daya buga ,har lokacin likitoci suna Kan mufy suna kokarin suga koyaya jininta ya sauka ae mata cs amma har yanzu shiru,  karfe sha d'aya da rabi daddy ya kalli yazid yace "son yakamata ka tafi gida mu zamu zauna anan tunda kabar mamana ita kadai a gida"  girgiza kai yazid yayi dan baijin zai iya komawa gida,mummy kuwa ko kallansu batai ba taci kuka harta godewa ALLAH,   daddy yace "bazaiyi yuwa ka zauna a gida ba ka baro wata acan zamanka bashi zaisa ta samu lfy ba addu,a kawai take bukata"
  Dakyar daddy ya lallabasa ya tafi har lokacin bai samu ganin mufy ba sai lekenta da yayi ta glass din dakin, da sauri ya wuce yana share hawayen fuskarsa duk me imani yaga halin da mufy take ciki dole ya zubar mata da hawaye,
   Yana zuwa gida neela ta mike cikin rawar murya data ci kuka ta koshi tace "yaya ya jikin nata"
Girgiza mata kai kawai yayi dan ba halin magana,zama tai tana hawaye har yayi wanka ya rama sallolin da ke kansa ,ya dade yana addu,a sannan ya shafa ya kalli neela da take gyangyadi a zaune hawaye duk sun bushe a fuskarta, daukarta yayi ya kwantar ya koma gefenta cikin tsananin damuwa da tashin hankali ,kwata kwata baiyi bacci ba haka ya kwana Kan sallaya,
  Washe gari duk yadda yaso neela ta zauna a gida kitai karshema fashe masa da kuka tai ,cikin tsananin damuwa ya kalleta yace "jeki dakko hijab"  da sauri ta wuce bedroom, tana fitowa ya taimaka mata ta shiga mota ya tayar,
  Duk sammakon da sukai saida suka tarar da ummi da abban mufy ,daddy ma ya zo da hajja , mummy da ummi cikin wani irin mugun mamaki suke kallan neela da take takawa da kyar sbd nauyin da cikin yayi mata, waje ta samu ta zauna tana sauke numfashi a sanyaye ta gaida su mummy had'e da yi musu yame jiki,
  Kaf dinsu ba wanda ya samu damar amsawa tsabar shock din da suka shiga ,ummi ta dauke kunburarrun idanunta daga Kan neela dan ita yanzu ta yarta take,
  Mummy kuwa wani irin kallo take aekawa yazid kafin ta dauke kai damuwar da suke ciki ma ta ishesu,
  Yazid kuwa waje ya samu bayan ya gaida iyayen nasa,shiru wajen bakajin motsin komai sai ummi da take share hawaye akai akai,
  Wani dr ne ya leko fuska daure yace "yanzu zaku iya shiga ku ganta amma bamason hayaniya da mutum biyu biyu zaku shiga"  ummi ce ta mike har tana tuntunbe mummy ta rufa mata baya,ummi ta toshe bakinta sbd wani irin kuka da yake taso mata ta dinga girgiza kai tana kallan mufy da take fidda wani irin numfashi tayi wani mugun fari fuskarta sai annuri take fitarwa,
Mufyda ta kalli ummi da mummy dakyar cikin wata iriyar murya tace "um,m,in,a"
Ummi ta riko hannunta tana kuka tace "Daughter ya jikin "  ta girgiza kai tana kallan mummy tai wani murmushin karfin hali tace "ummi da mummy kullum burinmu ni daku mu raba yazid da neela ,baku taba tunanin abinda muke kuskure muke aekatawa ba ,bamuda wani buri sai na mu kuntatawa wacce ta daukemu da zuciya daya,kulluk fatan sharri muke binta dashi kullum aebunta muke gani ,kullum so muke ta fita tabarni da yazid yau gashi ALLAH zai daukeni daga duniyar baki daya ya bar yazid da neela karkashin inuwar da bamuso su kasance "
  Taja wani numfashi a wahale tana fidda hawaye ta cigaba da cewa "duk burin da mukaci sai gashi yau za,a wayi gari na tafi nabar musu duniyar ,ummi nayi nadamar abubuwan da na aekata ku yafemin mutuwa zanyi"
  Ummi ta fashe da wani irin kuka me ban tausayi tace "bazaki mutu ba Daughter insha ALLAH zaki samu lfy"  mummy kuwa zaman dirshan tai tana kuka bilhakki, kasa cigaba da zama sukai da sauri suka fice suna wani irin kuka me karya zuciya ,
   Da sauri abban mufy ya shiga d'akin yazid ya rufa masa baya,yanayin da suka tarar da ita ya mugun d'aga musu hankali dan wani irin jijjiga da take cikin karfin hali take cewa "abbana ka yafemin ka nemamin gafara a wajen ALLAH," ta kalli yazid da hawaye yake ambaliya a fuskarsa tace "yaya yazid ka rokamin yafiyar neela kaima ka yafemin nasan na zalunceku na kuntata rayuwarku na shiga tsakaninku ka yafemin"
  Da sauri abbanta ya fice kiran likitoci sbd ganin yadda idanunta suke wani irin juyawa, yazid ya rufa masa baya da gudu yana kwalawa likitoci kira,
  Da sauri suka karaso suka rufu akanta suna kokarin taimaka mata sbd nakudar data sake tasowa ganga ganga,cikin ikon ALLAH tai wani irin nishi daya fito da santaleleyar yarta jajur da ita,kallo d'aya taiwa yarinyar da aka sako mata a kirjinta take numfashinta ya fara harardewa ,duk iya kokarin da sukai ganin daidaita numfashinta abin yaci tura ,dr aliyu ya zare duk wata na,ura dake jikin mufy ya lullubeta da farin zani,
Nannade babyn sukai a farin showle jiki a sanyaye dr aliyu ya fito ya zuba musu ido ganin yadda suka mike kowanne yana jiran yaji me dr zaice, ya zare glass din idanunta ya mikawa mummy babyn, dakyar ya bude baki yace "Sai hkr ALLAH yayi ikonsa akan mufyda ,ALLAHn daya baku ita ya karbi abarsa "   daga haka ya juya cikin sanyin jiki.
ya ALLAH kasa muyi kyakkyawan karshe 😭

Zuri,a DayaWhere stories live. Discover now