BABI NA GOMA SHA SHIDA

980 107 9
                                    

*NANNY...!*
      (Mai Reno..)

*Alƙaluman:*✍🏻

*AISHA ALTO💞*
*JAMILA UMAR (Janafty💕*

_Don"t Forget to Follow us on Wattpad:Janafnancy13 or Aisha Alto Alto_

*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔*
*KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*

      *BABI NA GOMA SHA SHIDDA*

"""Tahir Ya Fito Cikin Fitanshi na Zuwa Office yana Sanye Cikin American Suit Dinsa,Black and White ya matse Wuyansa da Tie yana Dauke da Brifcase Dinsa Lokacin daya Sauko Kasan Falo Ya Iske Basma da Laila da Bassam da Mudu suna zaune Bisa Dinining Suna Breafsat Suna ganinshi Kowanne ya Washe baki Suna Fadin"Daddy gud Mrning...?

Karisowa yayi yana Fadin"Mrning my Childreen How was Ur Nite.."Suka amsa da Fine Kan Basma da Laila ya Dafa kafin yace"Laila da Mudan Hutunku ya kare Fa Tun last Week ko .? Kai Suka gyadamai alamar Hakane Numfashi ya Sauke kafin yace"Ok Bari na Dawo Kila ko Zuwa Gobe Ko Jibi Saturday Sai mu maida ku gida ko..? Kallon Junansu Sukayi kafin Suce"Toh Daddy.."Suka Fada Suna Dariya Jin Harda Bassam zasu Rakasu gida.

Teburin yabi da Kallo kafin yace"Ina iya da Mufeeda Bazasu karya bane..'Basma ce tace"Bamu sani ba Daddy ammh iya Ta Dibarma Mufeeda Ta kaimata Daki Tundaga nan Data Fito sai Ta Koma Dakinta Bamusan Abunda Ya Faru ba.."Basma Taa Fada Tana kallon Tahir din Kafin ya samu Zarafin Mgana Bassam ya karbe da Cewa"Eh mana Daddy Gidan Duk ba Dadi Mufeeda bata Fitowa yanzu Iya ma kamar Akwai Abunda ke Damunta yau Duk kamar ba Ita ba.."Yafada cike da Kewa Irin Abun bayamai Dadi.

Shuru Tahir yayi kafin ya saki Ajiyar Zuciya yace"Ikon Allah Meyafaru ne..? Basma tace"Bamu sani ba Daddy Kila Ita da Momy ne kafin Tatafi.."Da kallo yabi Basma Baki bude kafin Yace"Tatafi..? Faridar bata nan ne..? Ina taje..? Ya jero musu Tambaya Lokaci Daya.

Basma ta Zakuda kafada kafin Tace"Bamu sani ba Daddy Tadai Tafi Har iya ta mata mgana Ta kusa Zaginta.."Ido ya zaro yana kallonta ganin Haka yasa ta Shiga maidamai Abunda ya Faru,Jinjina kai ya Hau yana Jin Wani Bakinciki na Ratsashi,Wato Duk Bayan Rusamai Rayuwa da Farida Tayi bai Isheta ba sai Tabi gari Ta gama Tonamai Asiri ko..? Domin yana da Tabbatacin Bata je Kano Domin bada Safenan ya samu Wayar Umma,bayan Sun gaisa Ta kara bashi hakuri game da Farida Tare da Fatan zasu zauna Su Rungumi kaddaransu kuma yanzu bads Dadewa ba Suka kara Mgana Da Abba duk da Mganar Business ne ammh da Farida Taje kano Jiya Dayaji lbri,Shi ba Wannan bama Damuwarshi naga Goggo Abu Domin Innaro da Ashe Sun Kirashi Awaya Suna Sanar Dashi ya Kokarta yazo Domin Baba Hakimi yayi mugun Fushi da goggo Abu baya Shiga Dakinta kuma yahanata Shigowa Turakarsa kuma Baya Shiga Sabgarta Tayi kuka Tanuna Nadamarta Ammh Baba Hakimi yayi Burus Da Ita Innaro ma Data Nemi Shiga Mganar Hakimi yaja mata Kunni da Kakkausan Muryan Kan in Ta sake ta Kara Shiga Mganar Itama zai Jingine ta Gefe Kamar yadda ya Jingine Goggo Abu..

Jin Haka yasanya Goggo Abu Ta Rikice sai Zazzabi da Ciwon kai Kafin kace kwabo ta Kwanta Ciwo koda Likita yazo Dubata sai Iske Jininta yayi bala"in Hawa nan Dai ya Dubata ya bata Mgunguna,ammh Duk da Haka Baba Hakimi bai Sakin ma Ra"ayinshi ba Koda ma akayi Haka ko Shashen Goggon Abu bai leka Ba gefe Daya kuma Inna Fulera na gida kwance ba lafiya Tun bayan Dawowarsu Hakimi ne Dayaji Lbri yasa Innaro da Ashe Suka Tafi Suka Dubata itama nan Suka Isketa jiiki yayi Zafi Maman lantana ke Kula da Ita Koda Suka zo suka Fada Hakimi bai Bata Lokaci ba ya Saka Aka kaita Asibitin garin Danbatta,Itama dai Damuwar ne ya Rafketa Hawan Jininta ya Tashi Gado Aka bata sai da ta Kwana Daya da Wuni kana aka sallameta Saboda Haka gabadaya Hankalinshi ba"a Kwance yake ba yana Jin Damuwarsa na Saka Ahali Dadama Damuwa gashi ya Lalatama Mufeeda Rayuwa da Farincikinta Gabadaya Saboda Shi bata da Sakewa kamar baya.

Ajiyar Zuciya ya Sauke kafin yace"Umh..Bari nayi mgana da Iya Tukunnah.."Yafada yana Sauke kanshi kasa Cike da bakinciki mai yawa yakama Hanyar Dakin Iya kenan Basma tace"Daddy..." Ya waigo yana kallonta cikin Dankwabe kai da Marairaicewa Tace"Ka fara Shiga Wajen Mufeeda First Daddy..."Tafada Tana Hada Hannuwanta alaman Roko..

NANNY Where stories live. Discover now