BABI NA GOMA

898 76 9
                                    

*NANNY..!*
_(Mai Reno..)_

*Alkaluman:*✍️

*AISHA ALTO*💞
*JAMILA UMAR(Janafty*💕

_Don't Forget to Follow us On Wattpad: Janafnancy13 or Aisha Alto Alto_

_*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*_

       *BABI NA GOMA*

Ranar barci ko ɓarawo bai Sace Tahir ba, kuka kuwa yayishi kamar Ranshi Zai Fita Daga ƙarshe ya Haƙura ya Fauwalama Allah komai ya kuma Ɗaukeshi A Matsayin Ƙaddararshi, Amma yasan Duk Abunda ya Faru Dashi Farida ce Sila kana Goggo Abu Da'ace Sunyi Duba da Lalurarsa da Irin Halittarsa, Da Duk Haka Bata Faru ba Amma yana Ta Neman gafaran Allah, sai dai Kunya da Nauyi Sun Cikamai Ƙirji Sun Hanashi Sukuni.

Shi yazo ya tashi Bassam Suka Tafi masallaci Sallar Asuba basu Dawo ba sai Wajen Bakwai Saura Koda suka Shigo Iya ta gyara Ko'ina Tana Kichen Tana Musu Abun Karyawa Bedroom ɗinsa ya shige ya Zauna Kawai ya Zabga Tagumin Makomar Rayuwarsa yadda ya Cuci Rayuwar Yarinya kamar Mufeeda.

Su Iya ko tana gama Abun karyawa Ta ɗorama Mufeeda Abunda Zata Tafin mata Dashi Asibiti Tunda Tahir yace in Sun karya Garzali zai Tafi Dasu, Shiko yana Cikin ɗaki yama kasa Fitowa Bawai bayajin Yunwa bane A'a yanaji Domin Rabonshi da Abinci Tun Jiya da Dare, Amma Cikinsa ne A Chushe bayajin Akwai Abunda Zai samu Wajen Zama ga bakinsa ba Tes Kwata kwata Ɗaci ɗaci ma yakeji Shikanshi Damuwa ta Saukar mai Da Zazzaɓi mai Zafi kan gado ya Kwanta ya Lulluɓa da bargo Haka Basma da Bassam Suka zo Suka iskeshi ya Dunƙule yana Hawaye, yanajin Muryansu Suna Kiranshi yayi Saurin Share Kwallah ya Fito da kanshi yana Ƙoƙarin Daidaita kansa.

   Basma ce Ta ƙarasa Tana Zama Gefen gadon Lokaci Ɗaya Take faɗin "Daddy jikin ne...? Ta faɗa Cike da Tausayawa, Kai ya girgiza musu kafin yace "No ba sosai bane Basma, nasha magani da nayi barci zan Warware, kun Shirya ne..." Bassam ne ya Ɗaga mai kai yana Zama Shima gefen Basma Fuskarshi ta bayyana Damuwar Dayake Ciki, Cikin Raunin Murya ya Furta..." Daddy What Wrong With you ne? bama jin Daɗin Ganinka A haka in Momy bata sonka Why not ka samo mana Wata Second Mom ko Basma...?" Ya faɗa yana kallonta, Saurin Kuka ne da Ita sai ga Hawaye Shar ta gyaɗa kai tana Faɗin "Eh mana Daddy, Momy tana Barinka kana Wahala bamai kula dakai ka ƙaro Aure plz kasamu Wacce Zata Dinga Zama dakai kullum muma Mu samu Mommy Wacce Zataso mu sosai Fiye da Momy.." Ta faɗa Kuka na Ƙwace mata ta Kifa kanta Jikin Tahir tanayi, Hannu ya saka yana Shafa kanta Dake Cikin Hijabin yanajin Ƙaunar 'ya'yansa Har Cikin Ranshi Duk da ƙananan Shekarunsu Sun Fahimci Damuwar nashi Acikin Ranshi Faɗi yake dama dama ace bai Aikata Abunda ya Aikata ba, Amma yanzu da Wani ido Zai kalli 'ya'yansa yace Shine ya Ketama Mufeeda Mutumci.

  Cikin Sigan Lallashi yake Faɗin "Shiii..Is Ok karku damu Kunji na samu Sauƙi Sosai Ku Tashi Ku Tafi Garzali zai kaiku Room 9 Take kunji.." Gyaɗa kai Basma Tayi kafin Ta mike Tana Share Kwallah Hannunta Bassam ya Riƙo Kafin su Duka Dukkansu Su Sakarma Tahir kiss a Goshi, Lumshe ido yayi Idanuwansa Sun Cika da Kwallah Cikin Raunin Murya yace "Take care..." Suka Fice Suna Ɗaga mai Hannu Suka Fita Wani Kuka yazo mai ya Shige Cikin Bargo yanayi kamar ya Shiɗe Saboda Takaichi So yake ya Buɗe Ido yaga Duk Abunda ya Faru mafarki ne Amma Ina bakin Alƙalami ya Riga Daya bushe, Abunda yasa Ma ya bari su iya suka Tafi Asibitin bashi da mafita ne don ya cigaba da Hanasu Zuwa Zasu Zargi Wani Abu, shiyasa yakira Dr Hadiza da Safen nan, dayake sun karɓi Numbarn Juna, ya Roƙeta Akan Don Allah mahaifiyar Mufeeda Zatazo Dubata koda Wasa Kada Ta mata Narrated din Abunda ya Faru da Mufeeda baya son Hankalinta ya tashi Sai daga baya zai sanar da ita, jin Haka yasa Dr Hadiza ta Amince da Roƙonsa suka Rabu Akan sai Anjima zai Shigo Asibitin.

Su Basma Sun Iske Jikin Mufeeda da Sauƙi Tana ta Barci ga Nurses nata kula da Ita sai Wajen 1 ta Farka taji Daɗin ganinsu Iya dasu Basma Ta dinga Murmushi, ta daina Kukan yanzu, Tunda Ta fara jin Sauƙi Gasata Suke bana Wasa ba ga mgaunguna gashi tana samun Hutu Dr Hadiza Da Tazo da Safe Haka ta Dinga Tambyar Mufeeda ko Zata Tuna Fuskar Wanda yayi mata Wannan Aiki Ko Zata Taimakesu Su Nemar mata Hakki, Acikin Ranta Kuka Take Har Asarari, Saboda Bazata iya Buɗe baki ta Furta Wanda ya Inganta Rayuwarta ne ya Aikata mata haka Bazata iya karya Alƙawarin da tayima Daddy ba Koza'a Kasheta Akaro na Farko Zata saka mai da Abunda yayi mata Arayuwa, tana kuka take Cemata bata sani ba Dole ta kyaleta.

NANNY Where stories live. Discover now