BABI NA ASHIRIN DA ƊAYA

991 84 7
                                    

*NANNY...!*
      (Mai Reno..)

*Alƙaluman:*✍🏻

*AISHA ALTO💞*
*JAMILA UMAR (Janafty💕*

_Don't Forget to Follow us On Wattpad: Janafnancy13 or Aisha Alto Alto_

*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔*
*KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*

    *BABI NA ASHIRIN DA DAYA*

"""Suna Shigowa gidan da Farida Suka ci karo tana Zaune Afalo Tana Zare ido Domin gama wayarsu kenan da Umma tana Tambayanta ya Wajen masu jego tace suna lafiya tanama Asibitin ne Tafito amsa waya ne,Umma taji Dadi tace mata suna nan Zuwa Cikin Satin nan Ita da Abbanta......

Daga Tahir har ya"yansa Babu Wanda ya Tankata Kowannensu Dakinsa ya Nufi Haka Shima Tahir ya Haura sama ya Fada Dakinsa A matukar gajiye yake Shiyasa yafada wanka,Iya ce kadai ta iya tsayawa tana gaida Faridan wacce Tabi su Basma da kallon Mamaki,Tahir ta Daina Damuwa dashi Domin baya Shiga Harkanta Tuni.

Bayan ta amsa gaisuwan Iya ne ta kalleta tana Fadin"Wai iya da gaske ne Mufeeda yan biyu ta Haifa...? Gyada mata kai Iya Tayi Lokaci Daya tana Washe baki tace"Eh Hajiya mace da Namiji yara nan kamar su Basma suna Jarirai inji innaro.."Harara Farida ta Zabgamata Lokaci Daya Tana Fadin"Kul kar na sake ji...Ni ya"yana na Sunnah ne karki kara Hadasu da Shegu wanda ba ya"yan Sunnah ba.."Cike da mamaki Iya ke kallonta bata samu Zarafin mgana sai ma gyada kai Datayi ta juya Zuwa Daki bayan ta kalli Naila dake barci kan kujera tagaji da kuka Barci ya kwasheta.

Da Harara Farida ta Bita kafin ta koma ta Zauna tana karkaɗa ƙafa, Iya tana Komawa ɗaki ta Fito ta Shiga kichen domin sama musu saukakkan Abinci da zasu ci Shiko Tahir Bayan ya Fito Wanka yayi sallar Isha'i da Shafa'i da Wuturi ya koma ya kwanta domin Haka kurum yaji Cikinsa ya Cika baya Sha'awan Cin komai kwance yake kawai yana Tunanin Wai shi yanzu mijin Mufeeda ne, Lalle Allah ne mai Tsara komai kuma ya aiwatar yana Fatan Allah yasanya alheri yabashi ikon kwatanta Adalci Domin baya ta Farida Ita yanzu bazai ƙara Ɗaukan Wani Iskancinta ba, Itama ta sani.

Da Iya ta gama Dafa musu macaroni da Kifi, Su Basma kaɗai Suka ci sai Iya ko Farida bata ci ba ɗaki ta koma tana kukan Bakin ciki da Takaichin Wai Mufeeda Ta haihu har 'ya'ya biyu lalle ma wato zata Haɗa kafaɗa da ita, ba wanda yabi ta kanta Har Washegari da Safe Tahir ya Tafi Office Su kuma Iya da Basma da Bassam da Naila data saka Rigimar sai ta tafi Tahir baima sani ba Ya bari sai zuwa yammah su koma Tunda ya tafi musu da Abun karyawan da Iya tayi musu Ashe su kuma suna Gama Dafa na Rana suka tafi dashi Keke Napep Suka Shiga Zuwa Asibitin Suka bar Farida agida tana kallon ikon Allah.

Sanda suka isa asibitin ma Sun Iske Zahra matar Ishaq itama ta kawo Abinci Mufeeda na Zaune Innaro na bata Tea abaki Taji Sauƙi ba kamar jiya ba, Namijin ne ke Hannun Zahra Shine mai Rigima macen na kwance Tana barci Naila Haka ta saka Rigiman sai an bata Ta Ɗauka ganin Su Basma Sun Ɗauka harda kukanta Su Iya na mata Dariya, cikin ikon Allah Ruwan Nonon Mufeeda ya Fara Zuwa ba laifi Tunda Dukkansu suna samu Suna Sha Duk da baya isarsu Da Safe ma da Tahir yazo Likita yamai maganar za'a Haɗa musu da madara saboda kada yunwa ta kamasu.

Kumburin Jikin Mufeeda ya Ragu amma ba Sosai ba, Sunyi Waya da Baba Hakimi da Goggo Abu Awayar Innaro Kunya Mufeeda keyi Jin Suna Tambayanta Ya Jikinta bata magana sai dai Murmushi Suna nan har Dare nan Ishaq da Tahir suka samesa bayan Sun Dubata Suka Wuce gida Gaba ɗayansu bayan ya kawo musu Kayan marmari da Nama gashasshe saboda Mufeeda Ta maida Jikinta.

Haka Suka Din gayi Har Tsawon Kwana Biyar, amma Farida bata taka Asibiti ba sai Ranar da Mufeeda ta cika kwana Shida taji Sauki ma, har ta fara Zuwa Bayi da kanta aikin ya fara Bushewa, Farida kunya taji Yasa ta Shirya taje Asibitin Aikwai Tayi Nadama Sosai Domin ba wanda ma yabi Ta kanta Bata Raina kanta ba sai da Yammah Bayan Tahir ya Shigo Asibitin yana Shigowa Ɗakin Su Basma da Iya da Innaro Suka Fice Suka barshi amma ita sai ma gyara zama Datayi kuma Abun Haushi ko Yaran bata Ɗauka ba Daga Cikin gidansu ta leƙasu Idanuwanta na kawo ƙwallah ganin Tsabar kama da Tahir da yaran Suke ko Mufeeda Da ƙyar ta iya gaisheta ta amsa itama ta kauda kai saboda Nauyi Itako Hararanta kaɗai take Acikin Ranta tana Faɗin "Kin kusa bar min gida makira.."

NANNY Where stories live. Discover now