BABI NA GOMA SHA BAKWAI

939 97 10
                                    

*NANNY...!*
      (Mai Reno..)

*Alƙaluman:*✍🏻

*AISHA ALTO💞*
*JAMILA UMAR (Janafty💕*

_Don't Forget to Follow us On Wattpad: Janafnancy13 or Aisha Alto Alto_

*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔*
*KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

      *BABI NA GOMA SHA BAKWAI*

""""Riƙe ƙugu Tahir yayi yana Sauke Ajiyar Zuciya, gefe Ɗaya kuma Zuciyarsa na Gudu Sosai Saboda Damuwa, Ashe ce Dake gefe Ta ƙarasa Kusa da Goggo Abu Ta Zauna Kusa da Ita Kafin Tace "Goggo..."

Ta faɗa Tana kallonta Innaro Dake Tsaye Ta Ɗora Hannu Bisa Haɓa Tana Faɗin "Wai Hakimi meke Damunshi ne..?Tunda nake Dashi ban taɓa ganin yayi irin Wannan Fushin ba.." Tahir ya waigo ya Fara Taku Zuwa Kusa da Goggo Yana Faɗin "Ranshi yana ɓace...Dole a saurara mai Har ya Sauko Da kanshi.."

Ya faɗa yana Zama gefen Ashe, Dayan Hannun ya kama yana Faɗin "Goggo Don Allah Kiyi Haƙuri kibar kukan nan Haka nan Nayi miki alƙawarin Komai zai Daidaita Insha Allahu..." Ya faɗa yana Kallonta Goggo Ta Murmusa Tana kallon Tahir da Ashe kafin tace "Bakomai...Allah yayi muku albarka Ku Tashi ku Tafi kubi Umarnin Mahaifinku.." Ta faɗa Tana ƙoƙarin Ɓoye Hawayen Da Suka Taru acikin ƙwayan Idanuwanta.

Innaro ta saki Numfashi Tana Faɗin "Shine kawai magana Don Rashin Tafiyar Naku ma Matsala ne, ku Tashi ku Tafi Insha Allah komai zai zo da Sauƙi, maganar Mufeeda kuma Iya ta Dinga Kula da Ita Saboda yarinya ce..ko Goggo ya kika gani..?" Hannunta Ta zare cikin na Tahir kafin ta saka Hannun ta Share Ƙwallarta Tana Faɗin "Eh Hakan ma yayi Innaro, Allah ya Sauketa lafiya kabiya ka gaida Fuleran karka manta.."

Gyaɗa kai yayi kafin yace "Insha Allahu.." Har ya Miƙe Innaro Tace "Ya ita Faridan...? Ina Fatan ba Wata matsala...?" Jinjina kai Yayi kafin yace "Eh Innaro ba Wata Matsala..."

Sauke Numfashi Tayi kafin tace "Masha Allah...Ko jiya naji Mahaifinta suna Waya da Hakimi kan mganar ne, Allah Ubangiji ya kawo mana Komai Da Sauƙi..."..

Gaba ɗaya Suka amsa da Ameen Kafin Ashe da Tahir suyima su Goggo Sallama Suka Fice Suka barta Tana Share Ƙwallah Fita Sukayi Inda yabama Garzali Umarnin ya Shiga da kayan Abinci Zuwa Cikin Gidan Hakimi, A ƙasa Suka Taka Shida Ashe Har Zuwa Gidan Inna Fulera, Wanda Suna Tafe Tahir na Faɗama Ashe Abunda ya Faru da Wanda yake Faruwa yana gaya mata kamar ya Zubar mata Da Hawaye, Cikin Tausayin Ɗan'uwanta Take Lallashinsa Take bashi Shawaran karya Damu, kuma ya ƙyale Farida Duk inda Zataje Zata Dawo ne bayan Duniya ta koya mata Hankali ya yarda Da Shawaran Ashe Duk da A lokacin Farida bata da wani Fari Acikin Zuciyarsa.

A haka suka isa Gidan Inna Fulera, Ashe ce Ta fara shiga Suka Gaisa da Inna Fulera da Maman Lantana kafin tace musu Tahir zai Shigo Cikin Sauri Maman Lantana ta gyara Tabarma Tahir ya Shigo ganin Maman Lantana ne Awajen yasaka Daga Ashe Har Tahir ba Wanda ya Tada maganar Illah Sunkuyar da kai Da Tahir Yayi kunyar kansa na Ƙara kamashi ganin yadda Inna Fulera ta Rame Lokaci bayan Lokaci Tana Share Ƙwallah...

Basu Wani Daɗe ba Tahir ya Miƙe zai Tafi bayan ya bama Ashe 30k yace Tabama Inna Fulera, Ashe na Bata taƙi karɓa Sai Ta Fashe da Kuka Lokaci Ɗaya Ta Ɗago ido Tana kallon Tahir bayan ta Ɗago Daga Kwancen Datake Maman Lantana Tana gyara Mata Filon Kanta Saboda Taji Daɗin Zaman Sosai.

Cikin Muryan Ciwo da Kuka Inna Fulera tace "Alhaji....."Ta faɗa Muryanta na Sarƙewa, cikin Sanyin Jiki Tahir ya Tsaya cak kafin ya Waigo Zuciyarsa na Tsinkewa Sosai Cikin Muryan Sanyi da Roƙo tace "Bana Buƙatar Kuɗinka Alhaji Abu Ɗaya Nake da Buƙata Awajenka.." jikinsa na Rawa ya Dawo ya Duƙe agaban Inna Fulera yana Faɗin "Ki Faɗi Abunda Kike Buƙata komai kike Buƙata matuƙar na Mallakeshi zan baki Shi Inna.." Ya faɗa Cikin Karaya..

NANNY Where stories live. Discover now