BABI NA ASHIRIN DA UKU

1.6K 94 9
                                    

*NANNY...!*
      (Mai Reno..)

*Alƙaluman:*✍🏻

*AISHA ALTO💞*
*JAMILA UMAR (Janafty💕*

_Don't Forget to Follow us On Wattpad: Janafnancy13 or Aisha Alto Alto_

*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔*
*KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*

      *BABI NA ASHIRIN DA UKU*

Ranar da Innaro ta tafi Farida ta samu Mufeeda a cikin Ɗakinta tana bama Ayman Nono Domin shiyafi Airah rigima, Gefenta ta Zauna Tana Faɗin "Kina nan Ashe..? Ina Airah take ne..?

Mufeeda tace "Wlh Ayman ya tashi Da Rigima ni nagaji da Tsotsan nan nashi Momy.." Hararanta tayi kafin tace "Kin me..? Lallai Awo ki Yarinya don sai sun Shekara 2 zaki yayemin yara.." Shagwaɓe Fuska tayi tana Faɗin "Kai Momy.."

Bata bi ta kanta ba ta fara faɗin "Kinsan Abunda Nake so Dake..? Mufeeda ta girgiza kai Farida ta cigaba da Faɗin "Yau zaki karɓi girki ma'ana Yau kece keda Abban Basma.." Ido Mufeeda ta Zaro gabanta na Faɗuwa Kallonta Farida tayi tana Faɗin "Eh Sai ki Shirya, yanzu tashi zakiyi mu shiga Kichen tare muyi Dinner, kinga ya kamata ace mun gyara komai bai dace ace yana da mata har guda biyu ba amma ace kullum Sai dai Iya ta girka ta bashi yaci ba sai na yanke Shawaran Duk wacce keda miji Ranar toh zamu Shiga kichen tare mu taimakama juna ko ya kika gani..?

Mufeeda ta Sadda kai ƙasa Tana Faɗin "Duk Abunda kika yanke Dai-dai ne Momy.." Kafaɗarta ta Dafa tana Faɗin "A'a karki ce Haka kema fa matar gidan nan ce kina da Hakki kan komai.." Mufeeda batayi magana ba Farida ta cigaba da Faɗin "Iya zata shi ci gaba da taimaka mana wajen kula da Airah da dai Sauransu.." Kai Mufeeda ta gyaɗa tana Faɗin "Hakan yayi Momy.." Sun daɗe suna hira kafin Ayman ya gama shan Nono Farida ta ɗaukeshi su Fito Falo, Su miƙawa Iya wacce ke goye da Airah tayi barci an samu 'yar Rigima Naila an tafi islamiya, Farida ce ta miƙa ma Iya Ayman ta faɗa mata Shawaran da suka yanke taji Daɗi sosai, Ko babu komai yanzu Tahir zai Fara Ɗanɗanan daɗin Aure.

Farida da Mufeeda Haka suka Zage suka Shiga Sukayi girki mai rai da lafiya, Tuwon Shinkafa suka yi miyar Agushi saboda Tahir yana bala'in son Tuwo ga miyar taji man Shanu da naman rago zuƙu-zuƙu, Zobo suka haɗa suka sanyashi cikin Fridge, Dai-dai Dawowarsu Basma Daga Makaranta suka gama komai har gyara kichen ɗin Farida ta Fita ta bar Mufeeda na wanke wanke Abun da suka ɓata, Su kansu yaran sunyi matuƙar mamaki ganin Duka iyayen nasu acikin kichen suma sun Nuna murnansu suna tsalle Cewa yau zasu ci girkin Momy dana Aunty Mufeeda.

Farida ta matsama Mufeeda taje tayi wanka itama Sama ta Haura ta Shiga wankan, Bayan ta Fito tayi sallar Magriba ta Shirya cikin wani ubansun Leshi Riga da zani batayi kwalliya ba amma Tayi kyau sosai Tana Fesa Turare taji Ihun yaran suna Faɗin Daddy oyoyo Murmushi tayi tana Ƙoƙarin Ɓoye Abunda ke Taso mata acikin ƙasan Ranta ta Fito Tun daga saman Steps d'in yake kallonta yana Riƙe da Naila harta ƙaraso tana Faɗin "Sannu da zuwa Abban Basma.."

Murmushi ya sakar mata yana Faɗin "Yauwa Umm Airah ko..? 'yar Dariya tayi Briefcase ɗinsa ya Miƙa mata ta maƙale kafaɗa tana Faɗin "Yau bani keda kai ba Mufeeda ce.." Duk da acikin Ranshi yaji daɗi domin wajen Wata goma kenan yana Fatan sake komawa wannan ƙorama amma sai bai nuna ba yawani Ware ido yana Faɗin "Bangane ba..? Baki ta murguɗa mai tana Faɗin "Baka gane ba ko..? Zaka gane anjima.." Dariya yayi yana kallonta saboda yarda tayi magana su Basma kuwa Tuni sun Wuce ɗakunansu, Farida ce ta Ɗaga Murya tana Faɗin "Mufee...Wai me kikeyi ne Haka bakiji Shigowar Megidan naki bane...? Ta faɗa tana Murmushi..

Mufeeda Dake laɓe Tun Ɗazu ta kasa Fitowa saboda kunya ta Fito kanta Sunkuye tana Faɗin "Gani Momy sallah na idar..." Ajiyar Zuciya Tahir ya sauke yana kallonta ƙasa ƙasa Tana Sanye cikin Riga da Siket na wata atamfa wanda yasan Mufeeda abaya ba wanda zai ce itace yanzu domin Mufeeda yanzu haihuwa da Namiji Sun Buɗata tayi kiɓa kamar ba ita ba hips da nonuwa kuwa sun cika ko'ina, ƙarasowan tayi ta ranƙwafa tana faɗin "Sannu da zuwa Daddy." Amsawa yayi yana kallon Fuskarta ido cikin ido Farida Dataga Haka sai ta wuce kichen tana Faɗin "Ki bishi Sama ki Taimaka mai yayi wanka Mufee, kafin ku Fito na Shirya Tebur.." Ta faɗa tana Shigewa kichen da Sauri kamar zata faɗi Domin bazata iya jurar irin wannan kallon Sha'awan da Tahir ke bin Mufeeda dashi ba.

NANNY Where stories live. Discover now