💖💖💖💖💖💖💖💖
💖💖💖💖💖💖💖
💖💖💖💖💖💖
💖💖💖💖💖
💖💖💖💖
💖💖💖
💖💖
💖*QADDARA TAH*
_(Destiny)_TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION
(( Home of Expart and talented writers, da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umma.))*Na*
*Khadeejah lawan* *Usman*
_(Deejerleen)_
Fallow me on Wattpad@deejerleen
*Didicated to my sweet* *mom janafty and sis* *fatnoor* 🥰🥰❤️❤️
_True life story_ 💖
Assalamu alaikum yan uwana masu karanta littafin nan ina gaisuwa a gareku, wannan shine littafi nafarko dazan rubuta, ina fatan zakumin uzuri abisa kuskuren da zanyi, Allah yabamu ikon daukan darasin dake ciki.
*Wannan labarin yafarune* *dagaske, labarine mai cike da* *cin* *amana da kuncin rayuwa, tausayi,* *ƙaddara, danasani, dason abin duniya. Duk wanda* *labarin yayi daidai da rayuwar tah* *tayi hakuri* ._Bissmillahir rahmanir raheeem_ da sunan allah mai rahma mai jin qai.
_Page 1_2_
,,,,,,,,,,,,Tafe suke cikin mota suna fira itada yayanta, daidai sunkaraso wani banki sukayi parking motar su wurin, suka fito suna tafiya suna fira izuwa cikin banki din, shigarsu keda wuya saiga manager na bank din yafito yazo wurinsu cikin fara'arsa ya tarbesu zuwa cikin office dinsa bayan sunshiga yanuna musu kujera suzauna.
Bayan sunzauna ne yake cewa yayan nata mai suna haruna da itace wanda za'a budewa account din, yace eh itace, yace ok biyoni muje suka fice shida ita yakai ta wurin wani daya daga cikin ma'aikatan bankin yamasa umarni daya bude mata sabon account, yace tazauna wurin shikuma yakoma office dinsa wurin yayanta Haruna.
********
Yasunan ki mutumin yatamba yeta? cikin siririyar muryarta mai dadi tadago dakanta tace masa sunana aisha Muhammad naseer sai yace wow.... nice name sannan yace ina takardun daza'a bude mata dasu, tamiqa masa nanda nan yashiga aikinsa na bude mata account, yana gamawa yace zata iya tafiya zuwa gobe saiki dawo tace dashi toh, nan ta nufi inda zai sadata da office din manager din bankin.Knocking tayi a qofar aka bata izinin shiga, tura qofar tayi tashiga ciki, manager din yace sannu da zuwa, yagama miki komai, tace eh ok bakomai zuwa gobe inkinga massage yashigo wayarki kidawo abaki ATM card dinki da account number, nan sukayi musabiha da yayanta suka nufi gida.
Suna tafiya yake cemata aysher, kinga kiyi a hankali karnaji kintsaya kina maganah dawani acikin bankin nan saboda yanzu duniyar tabaci, na allah sunyi karanci, ta amsa masa da to yaya haruna zan kiyaye insha allahu, shiru yabiyo baya har suka iso bawanda ya qara maganah.
Hon yakeyi awani babban gida daya cinye layin gabadayansa, gidane mai dogayen katangu wanda ya qawatu da furanni masu kyau da burgewa mai dauke da sashe daban daban.
Baban sashen mai gidan sai na matan gidan dana yara maza da mata sai bangaren masu aiki, daga bayan gidan kuma lambu ne wurin dauke da bishiyoyin mangwaro,goba, kashuu, fasadabur dabino,ayaba lemon fata dana tsami sai gefe shukan inibi dadai sauransu.
Sashen mai gidan yana dauke da six bedroom da falo guda uku, kowani bedroom yandauke da bathroom, falo daya da bedroom hudu asama, falo biyu da bedroom shida akasa, tareda wurin dani a sama da kasa, sai kujeru da'aka qawata kowani falo, danashi kalar kujerun, bedroom din anqawata da manyan furnitures na zamani, Sannan aka qawata farfajiyar sashen da flowers masu kyau da daukar ido gwanin sha'awa.
YOU ARE READING
QADDARA TAH
Non-FictionLabari ne akan wani hargitsetstsen family tareda wata yarinya mai suna aysher...? Wanda taga jarrabawa kala kala, tsangwama, tsana, sanadiyar yayanta da kuma yan uwanta da suke uwa daya uba daya.......yan uwanta basu sonta sbd abin duniya ya rufemu...