💖💖💖💖💖💖💖💖
💖💖💖💖💖💖💖
💖💖💖💖💖💖
💖💖💖💖💖
💖💖💖💖
💖💖💖
💖💖
💖*QADDARA TAH*
_(Destiny)_*TAMBARI WRITER'S* *ASSOCIATION*
🔱 (( Home of Expart and talented writers, da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umma.))*Na*
*Khadeejah lawan usman*
_(Deejerleen)_*Follow me on Wattpad*
*@deejerleen**Didicated to my sweet* *mom janafty and sis* *fatnoor* 🥰🥰❤️❤️
_True life story_ 💖
_Bissmillahir rahmanir_ _raheeem,da sunan allah_ _mai rahma mai jin kai_ .
_Page 7_8
****
"Abangaren aysher kuwa shiga gidan tayi bakinta dauke da sallama, aunty mufee ce tafito daga kitchen zatashiga falo taji sallama hakan yasa tadakata dashiga falon, jin muryar eeesha yasa ta washe baki tana dariya, da fara'arta ta karaso gun aunty mufee ta rungumeta, "sai yau zakizo eeesha, tace"wlh aunty mufee aiki nakeyi ne shiysa bana fita amma zanna zuwa yanzu komai yayimin normal.Qarasawa cikin falon sukayi, suka shiga firar yaushe gamo "duk da gari daya suke amma aysher a lokacin bata fita" suna firar ne aysher ta karbi girkin da aunty mufee keyi taqarsa, bayan tahaɗane akayi kiran sallar la'asar, wucewa tayi bedroom din aunty mufee, tanashiga bathroom tawuce taɗauro alwala, fitowa tayi tanemi darduma ta kabbarta sallah.
Bayan ta idarne saita fito falon nan ta iske anty mufee zaune tana kallo, "yawwa eeesha jeki zuba abinci kici ni sai abban waleed yazo sai muci inji aunty mufee, wucewa kitchen aysher tayi, debowa tayi daidai yadda zai mata, tuwon semo ne da miyar kuɓaiwa da tasha kayan lambu da naman rago, sosai miyar tayi kyau da dadi.
Falo tadawo tazauna tanaci tana kallon wani series da akeyi a Bollywood mai suna "sharqat zaujeey" sosai takejin dadin abincin dakuma series ɗin da akeyi.
Bayan ta kammala ne tawuce kitchen ta ajiye komai ta gyara ko'ina sannan tafito, falon ta koma dan qarasa kallon series ɗin da akeyi...
Tana cikin kallone abban waleed yadawo, aunty mufee tashi tayi ta tarbeshi, shigowa falon yayi, ina yini inji eeesha, yace" lafiya qlw yauwa nake gani kamar aysher, tace" eh nice, cewa yayi " yaukam antuna damu haka ziyara, aunty mufee cewa tayi aiyanzuna ummee ce ta aikota shiyasa kaganta dabazata zoba, murmushi yayi yace " nifah nace hakanan dai nasan baza'a kawomana ziyara ba, eeesha da duk kunya yakamata tace " aa wlh dama inason zuwa allah ne baiyiba sai ya.
Murmushi yasakeyi yace" shikenan ai yasu hajiya dasu ummee da mama da ummah tace" lafiyar su qlw, agaidadu tace" toh" wucewa yayi aunty mufee tabishi zuwa bangarensa.
Maida kanta tayi wurin tv tacigaba da kallonta cikin kwanciyar hankali, can kamar an mintsineta tajanyo wayarta, Instagram tashiga nan tafara chatting ta ista.
****
Bangaren naxeer kuwa, bayan yagama shan ruwanne ya dubi fa'iza ƴace " inajinki kinyi kirana, sauke ajiyar zuciya tayi sannan tace" alfarma nakeso kamin kuma kaima zakasamu naka kason, cikin rashin fahimta yace"bangane mi kike nufi ba, wani abu zanmiki fadi inaji inzan iya, qara sauke ajiyar zuciya tayi sannan tace "inasone kasace zuciyar aysher domin cinma buqata tah yace " wata buqata kenan, tasowa tayi zuwa inda yake tamai raɗa akenne, wanda nima banji mitace masa ba, nan naga ya washe baki yana dariya yace " kamar kinshiga zuciyata wallahi, komawa inda take da zama tayi, sannan tace " shiyasa nane meka dannasan zakayi.Cigaba da tattauna yadda tsarin su zaikasance sukayi, bayan sun gama ne take qara jaddada masa karyayi wasa kuma intaqi aminta dashi tamasa magana akwai hanyarda zasubi saita amince dashi, dawannan ne ta rakoshi har qofar gida sannan sukayi sallama akan zasuyi waya, komawa ciki tayi shikuma ya qara sa wajen motarsa ya mata key yabar unguwar.
oda yabar unguwar wucewa yayi wurin gidan mamansa, parking yayi a kofar gidannasu yafito ya shiga cikin gida, kai tsaye dakin aunty amarya yashigo suka gaisa bayan nan yawuce dakin mahaifiyar sa, iske tah yayi tana kishin giɗe akan carpet ɗin dake malele adakin, durkusawa yayi ya gaisheta, amsawa tayi cikin sakin fuska da maraba dazuwan ɗannata, nan suka shiga fira tskanin ɗa da uwa.
****
Bangaren fa'iza kuwa naxeer nafita takoma ciki, cikeda farin cikin zatayi nasara akansu, tana cikin hakane mijinta yadawo, tarbansa tayi ta kawo masa abinci da ruwa, abinda yabashi mamaki, yau tana cikin farin ciki shiyasa yasamu wannan tarban, shiru yayi baice komai ba ya biye mata.Yana cin abinci tana masa fira shidai ido kawai yazuba mata sakamakon ganin abinda bata taba masa ba saidai intanason wani abu wurinsa, shima din tarba kawai yake samu banda fira kamar ta yau, hakadai yakecin abincin yanata sake-sake, dawannan ne yagama ci sannan yasha ruwa takwashe kayan tagyara wurin.
****
Aysher kuwa bata tashiba saida takira ya yaseer tashaida mishi bayan sallar magrib zata tafi yace " to saiyazo, tace" to sannan takashe wayar, tashi tayi dan shiryawa da tayi sallah sai gida, aunty mufee ce tashigo tasameta, kasancewar abbansu waleed yafice zuwa Masallaci kuma sae dare zai dawo.Kardai tafiya zakiyi inji aunty mufee, eh tafiya zanyi amma yanzu sallah zanyi kafinnan ya yaseer din yazo inji aysher, mikewa tayi danyin alwala........
Bedroom dinta tashiga taɗauro alwala, sannan tafito shimfida darduma tayi takabbarta sallah, bayan ta idarne tashirya ta fito falon, fitowar ta keda wuya saiga ya yaseer yashigo gidan, gaisawa sukayi shida anti mufee sannan yace " yawwa aysher yashi mutafi dare nayi, tashi tayi suka fice, anti mufee ce ta dauko mata saqon ummeen suka fice
Vote
Comment
ShareAllah kasa mudace......... ameeeen
Alqalamin deejerleen.......✍️
YOU ARE READING
QADDARA TAH
Non-FictionLabari ne akan wani hargitsetstsen family tareda wata yarinya mai suna aysher...? Wanda taga jarrabawa kala kala, tsangwama, tsana, sanadiyar yayanta da kuma yan uwanta da suke uwa daya uba daya.......yan uwanta basu sonta sbd abin duniya ya rufemu...