QADDARA TAH

11 0 0
                                    

💖💖💖💖💖💖💖💖
💖💖💖💖💖💖💖
💖💖💖💖💖💖
💖💖💖💖💖
💖💖💖💖
💖💖💖
💖💖
💖

QADDARA TAH
(Destiny)

TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION
🔱(( Home of Expart and talented writers, da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umma.))

T.W.A


Na
Khadeejah lawan usman
         (Deejerleen)

Follow me on Wattpad
         @deejerleen


Didicated to my sweet mom janafty and sis fatnoor 🥰🥰❤️❤️

"Ina yiwa daukacin al'ummar musulmi barka da sallah, Allah ya maimaita mana......👏👏

True life story 💖

Bissmillahir rahmanir raheeem, dasunan Allah mai rahama mai jin kai.


NOT EDITED ⚒️

Page 11_12


Shiga office din tayi bakinta dauke da sallama, amsawa yayi idonsa akanta itakwa kanta na qasa tashiga office din, kujera ya nuna mata yace "have a sit, zaunawa tayi a kujerar daya nuna mata, kasa sakewa tayi da kallon daya mata, duk abinda akeyi ya haruna bai lura da suba hakan yasa baice komaiba yace " yawwa munzo karban ATM da sauran abunda yakamata kubata, naxeer yace" eh yanzu zamu bata amma zata dan jira tukun,


Ana cikin hakanne wayar ya haruna tayi kara, dubawa yayi yaga sulaiman ne cikin sauri yadauka tareda karawa a kunnensa banji abinda ake fada daga dayan bangarenba amma naji yace toh! Gani nan zuwa, yana kashe wayar tasa atare yana meqewa tsaye, duban aysher yayi yace nizan wuce ana jirana inkingama saiki hau napep kitafi cewa tayi "toh" juyawa yayi ya kalli naxeer dayake kallonsu yace masa nizan tafi ana kirana ne pls kagama mata komai dawuri kar asamu matsala, naxeer cewa yayi " toh, musabiha sukayi sannan ya fice cikin sassarfa,,,

Ajiyar zuciya tasauqe, dagowa kanta tayi daniyar yimasa magana karaf idanunsu ya sarke, kasa jurar hada ido dashi tayi kawar wa da kanta gefe tayi cikin can kasan maqoshinta tace " banza maye kawai, cewa yayi " magana kikeyine, cewa tayi " a'a daman sonake kabani foam din ATM din nacike sai naje nakarɓa, kura mata ido yayi yanda take maganar ma abin burgewa, jin shirune yasa eesha dagowa da kanta taga ita yake kallo cikin kunkuni tace "wannan yacika kallo wallahi, afili kuwa cewa tayi "kayi shiru, ajiyar zuciya yasauke sannan yamiqo mata wata paper da biro,,,,

Cewa yayi tadawo wata kujera nan kusa dashi bamusu tamatsa tazauna a kujerar daya nuna mata, bayani yamata sannan yace abinda bata ganeba ta tambayeshi, karba tayi cikin nutsuwa tafara duba paper ɗin tana cike duk inda yakamata ta cike, duk abinda takeyi yana kallonta yana binta dawani mayen kallo yana haɗiyar yawu, aransa yana cewa " aidole nabi duk wata hanyar da nasan zan ɗanɗani zumar aysher dagani zatayi daɗi sosae,

Ɗagowa da kanta tayi kamashi tayi yana kallonta harara tamaka masa tace" wai kai dan Allah saikai ta kallon mutum baka ganiyane pls kadaina kallona banaso, kunya ce takamashi amma da yake dan duniya ne saiya basar yace "waya fada miki kallonki nakeyi,,,,,,,

Yamutsa fuska tayi tace "daban kamaka kana kallona bane saikace haka dariya yayi cikin nishaɗi sannan yace " yawwa nibaki bani amsan abinda mukayi dake awaya ba, wani kallon bakada wayau tamasa sannan tace ni aibazan auri mai mata ba impact ma sam nibakamin ba kabar wannan maganar mima zanyi dakai tayi tsuka, shiko kalamanta da furucinta baqaramin daga masa da hankali yayi ba amma dayake ɗan duniya neshi basarwa yayi yace mata " nibanga aibun mai mataba kuma banga aibuna bah, cewa tayi " dama ina zaka gani da kanka kamar dambu tafada cikin kunkuni danbaiji mitace akarshe ba,,,,,,,

Miqewa yayi yace ta biyoshi bamusu tabishi suka karasa main office ɗin ma'aikatan gaba daya, wani wuri suka nufa inda ananne akeyin katin atm ɗin, layine wurin sosai, magana yayiwa wani mai suna ahmad da cewa, ga qanwata nan kamata yanzu danzata wuce gidane, wanda yakira da ahmad ya amsa da toh , wuri ya nuna mata tazauna cikin qanqanin lokaci yagama mata komai sannan yabata card ɗin, komawa office ɗin naxeer tayi, cemasa tayi angama komai, nandai sukayi sallama yafito har compound ɗin bankin yarakota, saida tatafi sannan ya koma office ɗinsa cike da damuwa......


***
Emir road zaka kaini inji aysher, mai napep yace toh, unguwa ce tamasu kudi gidajene ajere agun masu gini iri daya, dan zasukai ashirin gidajen duk iri daya ne, akofar wani gida naga suntsaya wanda shima irin su daya dasauran, sauka tayi daga adaidai tan dayake dazun naxeer yabawa mai adaidaita ɗin kuɗinsa yasa tana sauqa kotakan mai adaidaita batabiba ta nufi katon gate din gidan mai dauke da coffee nd milk color, nocking tashiga yi can akazo aka bude mata,


Shiga cikin compound ɗin gidan tayi, wata hanya naga tanufa dazai sadata da falon matar gidan, shiga tayi falon bakinta dauke da sallama, bakowa afalon hakan yasa tanemi wuri tazauna tareda yin rigingine fuskar tana kallon sama, lumshe kyawawan idanunta tayi tanamai jin dadin kamshin dake ratsa habcinta har zuciyarta, dama aysher akwai son kamshi,,,,,,


Tana zaune ne saiga hafsa matar sulaiman tafito, toh badai laifi hafsa irin matan nance sirara batada jiki sosai, saidai tanada shape daidai gwargwado, qarasowa tayi cikin fara'arta tana cewa "saiyau akane memu kodai kodai, dayake in aysher kaga taje gidan dawani saurayinta zasu hadu shiyasa take zuwa hakanne yasa hafsa ke cewa kodai², itadai eesha batace komaiba, miqewa tayi tace mata nifa yunwa nakeji kisamamin wani abu naci, hanyar dazai sadaka da kitchen hafsa ta nunawa aysher tace ga hanya nan aikinsani.

Miqewa aysher tayi tana cewa "yanzu fisabilillahi mutum yayi baqo amma bazai tarbeshiba itadai hafsa dariya take mata tana cewa "kekaɗai dai ajiyeni kikai dazan miki abinci kuma indebo miki? Aibazai yiwuba namiki ciki harda uwar daki...? Fitowa tayi hannunta dauke da plates guda biyu ɗaya shinkafa ce da miyar jajjage dataji naman rago da bushasshen kifi dayan plate ɗin kwa haɗin cabbage ne da carrot bama sai waken gwangwani, cream slade, da kuma dafaffen kwai..

Karasowa tayi tazauna akan carpet ɗin dayake malale afalon ta ajiye plate ɗin sannan tazauna, hafsa cewa tayi bazaki je dining kiciba, cewa tayi nan yafi can dadi, haka suka zauna suna ta fira itada aysher harta gama cin abincin tattare plate ɗin tayi tagyara wurin sannan tadawo suka cigaba da firarsu wanda duk akan kasuwanci sukeyinta, Domin dai hafsa yar kasuwace tana saida atamfofi, lessuka, material dadai sauransu harsu takalmi, hijab, da sarka mai dan Kunni, aysher koh yanzu ba abinda keburgeta saitaga tafara sana'a wanda hakanne yasa ta qudurta aranta saitayi,,,

Haka dai suka cigaba da firar tasu duk akan kasuwanci da kuma yadda aysher zata karbi kudinta wurin uncle bee dan tayi nata kasuwancin.......

****
Bangaren naxeer kuwa......................?






Vote
Comment
Share

Allah kasa mudace........ ameeeen
Alqalamin deejerleen.......✍️



  QADDARA TAHWhere stories live. Discover now