QADDARA TAH

18 1 0
                                    

💖💖💖💖💖💖💖💖
💖💖💖💖💖💖💖
💖💖💖💖💖💖
💖💖💖💖💖
💖💖💖💖
💖💖💖
💖💖
💖

        *QADDARA TAH*
             _(Destiny)_

TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION
🔱 (Home of Expart and talented writers, da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umma.)

*Na*
*Khadeejah lawan Usman*
      _(Deejerleen)_

*Follow me on Wattpad*

*@deejerleen*

*Didicated to my sweet* *mom janafty and sis* *fatnoor* 🥰🥰❤️❤️

  *_True life story_* 💖

_Bissmillahir rahmanir_ _raheeem, da sunan allah_ _mai rahma mai jin_ _qai._

_Page 3_4_

Sulaiman yakasance shine babban ɗan hajiya a maza, mutum ne mai son mata, fasiqi ma zinaci, mai son abin duniya bashi da kyauta ga munafurci, har yayi aure baidaina bin matan banza ba, matarsa data sani ba qaramin baqin ciki tayiba jin cewar mijinta na biye biyen mata.

Kasancewar ita batabin maza saidai bin malamai, acikin ƴaƴan da Alhaji Muhammad naseer yake riqonsu,  ƴaƴane ga kaninsa mai suna Abdullahi allah ya masa rasuwa, cikin ƴaƴan nasa akwai wanda sulaiman yayiwa ciki babbar yar alhj Abdullahi kenan mai suna fa'iza.

Lokacin da labarin ya riski kunnen alhj Muhammad naseer baqaramin kaduwa yayiba, dama cikin ƴaƴansa za'asamu mazinaci..? Sulaiman dayaji alhj nanemansa saiya bar garinma, alhji yayita bawa fa'iza hakuri yace itama yarsa ce, yanzu abar maganar nan har saita haihu inji alhj Muhammad.

Amma na yanke hukuncin zan kaita gidan Fatima dake jihar Bauchi ƴace agun mamah, acan zata zauna harta haihu, fatima batayiwa baban nata butulci ba takarbeta suka zauna harta haifi yarta mace mai kama da uban ta sak.

Bayan anyi suna lfy ƴa taci sunan mahaifiyar sulaiman, ana kiranta da tasleem, mashallah tasleem ansha kyau tareda mai jego kamar ba cikin shegeba, amma anyi taron cikin sirri yan gidane kawai suka sani.

Fa'iza ƴace a gun alhj Abdullahi kamar yadda nafada, tataso cikin gata da tarbiyya, saidai babanta ya rasu lokacin da take shekara 18 aduniya, tana da qanne mata biyu maza uku sai babban wanta namiji mai suna Waleed.

Bayan rasuwar mahaifinta, shine alhji Muhammad yadaukesu itada ƴan uwanta,  dalilin sulaiman kanta ya waye suke soyayya harta amince masa ya keta mata budurcinta.

****
Bada jimawaba auren sulaiman yataso inda tashiga bin malamai lallai saita aureshi (matar mutum kabarinsa) Allah baibata dama ba, har'akayi auren, amma saida aka shiga kotu dan tayi kararsa gaban alqali.

Anyi zaman farko inda aka nemi mijin fatima daya halarci taron don bada shaidar agidan sa ta haihu, mijin fatima ɗane shima awurin alhj Muhammad naseer, ɗan wansa ne mai suna faruq, Fatima da faruq hadin gidane.

Court
Shiru kotun yadauka sakamakon mijin fatima na bada shaidar abinda aka tambayeshi, cikin nutsuwa yafara da cewa, eh ya mai girma mai shari'a a gidana fa'iza tahaihu, alqali ya qara tambayarsa shin ko sulaiman yana kaimata ziyara lokacin da take gidan ka.

Ya amsa da cewa! Gaskiyar magana baya zuwa saboda marigayi alokacin yahanashi zuwa, nan fa'iza tashiga zagin mijin fatima tana cewa karya yake, harda jamasa Allah ya isah, alqali ya tsawa tarmata tayi shiru, aranta kuwa cewa take sainaga bayan ahalin alhj Muhammad naseer baki daya.

Alqali yace wa faruq zaka iya komawa, alqali ya kara kiran falmata wanda qanwa ce a wurin alhj Muhammad naseer ubansu daya uwa kowa tasa, tafito alqali yace mizakice gameda abinda fa'iza tace, nacewa kekike rakata wurin boka don ayiwa mahaifiyar sulaiman da sulaiman din asiri, falmata ta fara kuka tana cewa sharri zakimin fa'iza, tsakanina dake Allah zai sakamin, alqali yatsawatar mata da nan kotune bawurin fada ba.

Alqali yasa abata qur'ani tayi rantsuwa dashi, dataga dagaske rantsuwar zatayi yasa tace, inada magana yamai girma mai shari'a, yace muna saurarenki, gaskiyar magana bani kadai bace harda wasu daga cikin qannen alhj Muhammad da kuma ƴan dakin hajiya, amma subasu san da mahaifiyar su acikin kullin da mukeyiba.

Hankulan ƴaƴan alhj Muhammad yatashi jin cewa harda na gida, dominko allurace zata tono garma, suka nemi alqali da ayi watsi da shari'ar zasu sasanta, alqali da yaki amincewa, amma dayaji hujjar su mai karfice saiya kori qarar daga kotuns, yareda cewa insunason daukaka qara zasu iya aka watse, amma kowa cikin ransa da abinda kesaqawa.

Musamman fa'iza dataci alwashin ruguza iyalin alhj Muhammad naseer, inda falmata ta dora da gaba da mutane dadama tareda alwashin sai ƴan dakin hajiya da mama sun gane kuransu kuma yanzu tafara zuwa wurin boka.

Wacece falmata
Ƴace a wurin goggo daso, mahaifinsu daya da alhj Muhammad naseer, alhj naseer ne mahaifinsu, matansa hudu shima, falmata tataso da halayyar mahaifiyarta na riqo da abu.

Falmata takasance matace mai bin malamai da bokaye, mai kwadayin abin duniya, gata da rigima da fada ga gulma da kuma baqar zuciya, tanada ƴaƴa guda shida mata uku maza uku, ƴarta tafarko tayi aure, inda yakasance ƴarta ta biyu autan dakin mamane kesonta, sai ta uku inda ɗan dakin hajiya kesonta haruna kenan.

Haruna da Muhammad wanda sunan alhj Muhammad naseer yaci, sunka sance mutanene masu kashewa mace kudi indai zata sosu tsakani ga Allah hakance ta faru ga falmata suna kashewa ƴaƴan ta kudi, itakuma abinda takeso kenan.

Yayinda akasamu wannan hatsaniyar ne haruna da Muhammad suka janye wanda saida yan uwansu sukayi dagaske don sunkamasu da asiri, takaitaccen labarin falmata kenan.

****

Bayan andawo daga zaman kotune manyan ƴaƴansa suka shirya meeting a gobe misalin qarfe goma na safe, inda aka buqaci duka iyalansa da ƴaƴansa su halarci wurin

Washe gari yakasance ranar asabat da misalin qarfe goma daidai, kowa ya hallara a babban falon alhj Muhammad naseer, uncl ya bude taro da addu'a,,,,,,

Abubakar yafara magana kamar haka" kunsan abinda yatara mu gameda karar da fa'iza takai kotu, hakan baimana dadi ba yanzu ace baran alhj ashe bazamu iya zama tsintsiya madaurinta daya ba, gaskiyar magana wannan abin kunya ne agaremu! Yakamata mugyara zumuncinmu muzama daya.

Haba hajiya keda yakamata kiyiwa su salma fada, abinda sukayi sam baidaceba, dan Allah kikarasa idanu akansu domin duk abinda mukayi idon mutane na kanmu,

Mama tace wannan hakane fatan zamu gyara, Hajiya da cikin ranta cewa take! Toh mai kinibibi hakadai zaku kyalemu nida yayana musarara.

Haka akagama tattaunawa tareda raba wasu kaya na alhj wanda aka kawosu daga gidajensa na abuja, kano, kaduna dana Kazaure, kowa yadauki abinda yakeso, aka rufe da addu'ar zaman lfy taro ya watse...........

*Vote*
*Comment*
*Share*

_Allah kasa mudace_ _ameeeen_ ..........
Alqalamin  deejerleen.....✍️

  QADDARA TAHWhere stories live. Discover now