💖💖💖💖💖💖💖💖
💖💖💖💖💖💖💖
💖💖💖💖💖💖
💖💖💖💖💖
💖💖💖💖
💖💖💖
💖💖
💖QADDARA TAH
(Destiny)T
AMBARI WRITER'S ASSOCIATION
🔱(( Home of Expart and talented writers, da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umma.))T.W.A
Na
Khadeejah lawan usman
(Deejerleen)Follow me on Wattpad
@deejerleenDidicated to my sweet uncl captain, abban faty and 6star of j.i.k family. 💃💃 🥰🥰❤️❤️
Wannan shafin nakune kuyi yadda kukeso dashiSADAUKAR WA GA MOM JANAFTY AND GRANNY FATNOOR.❤️❤️
"Taqabbalallahu minna waminkum, allahumma taqabbal siyamana wa du'a anah wa ibadanah ya arhamar rahimeeen,,,,, happy eid al-mubarak.
True life story 💖
Bissmillahir rahmanir raheeem, da sunan allah mai rahma mai jin kai.
Page 9_10
Shigarta gida kenan ta iska uncl yazo shi, qarasawa tayi cikin dakin na ummee ta gaidashi, sannan ta ajiye saqon ummee tafice zuwa dakin hajiya.
Washegari yakasance ranar saunday ne shima ba aiki haka tazauna acikin gida ba inda taje, amma yaukam tatashi da sha'awar yin wani abu na kayan makulashe taci, hakan yasa tace zatayi meat pie da snaks,
Bayan tagama ne ƴaƴan yayunta suka zo gidan, dan yau gidan acike yakeda ƴaƴa da jikoki, jikokin dakin mama sunyi sabo da aysher sosai duk da kasancewar bayar dakin iyayensu bace amma akwai kyakkyawar fahimta da alaqa atsakaninsu sosai.
Aunty aysher haka suke fada mata, dakin unmee suka shiga nemanta sunkwa yi Sa'a tana nan, karasawa sukayi, suka fada jikinta suna murnar ganinta itama cewa take " ƴaƴanta sannunku da zuwa, nan fira ta barke bakama hannun yaro suna tafira tsakani uwa da ƴaƴanta🤪, dakin oummah suka tafi don acan suka fiya zama.
Sallan magrib ne yadatasu, kowa yaje yayi Sallah, bayan kowa yagama sallah suka dawo falon don kallon shirinnan na arewa 24 mai suna raghav, haka har sallar isha kana kowa yaje yayi sannan suka fara shirin tafiya gida, rakiya tayiwa ƴaƴan nata har parking lot sannan tadawo ciki, tana zuwa shirin bacci tayi tabi lafiyar gado.
Washegari yakasance monday kamar yadda kowani ɗan matakaranta yayi niyya masu aikin office haka takasance wa aysher, bayan ta kammala gyare-gyaren daki da falo, wucewa bathroom tayi don yin wanka, koda tafito daga wanka shiryawa tayi cikin shigarta ta atamfah riga da skate, atamfar green ne da adon baki anwa dinki ado da pattern din rigar stone work ne hakan yasa riga da skate din sunyi matuqar kyau, lotion dinta tashafa mai kamshi domin itadai aysher akwai son kamshi sosai koda kyauta zaka mata to kabata turare dan tafisonsa, zura rigar tayi sannan tasa skate din wanda yafito da hips dinta sosai, simple make-up tayi tafeshe jikinta da turarukanta masu qamshin da sanya nutsuwa, fitowa tayi falo ummee tace " kije kici abinci ankawo "toh aysher tace sannan ta wuce zuwa yin breakfast.
Koda tagama wucewa tayi dakin matan gidan kowacce taje tagaisheta sannan tadawo daki, kiran ya haruna tayi " ce masa tayi yau zataje ta karbo ATM din daga can bangaren haruna yace" toh kishirya zuwa karfe 12 sai muje cike da murna tace" toh ya haruna ashirye ma nake yace" toh kijirani daga haka yakashe wayar, dakin hajiya tawuce, da sallama tashiga ta tarar da mahaifiyar tata zaune akan gado karasawa tayi tazauna kusa da ita tace" hajiyata sannu kintashi lafiya hajiya tace" lafiya qlw aysher yanzu nake nemanki ai hafsa matar sulaiman tace infada miki inkin dawo daga banki kije, aysher tace" eh dama inason zuwa gidan, firarsu suka cigaba na ƴa da mahaifiya.
Tana nan dakin hajiya har 12 tayi saiga ya haruna ya shigo dakin, gaida hajiyartasa yayi sannan yanemi wuri yazauna, aysher fita tayi zuwa dakin hajiya taje tadauko black veil da takalmi sa jakarta, samun ummee tayi afalo tace mata" zataje banki daga can zata wuce gidan hafsa "toh ummee tace adawo lfy, dawowa dakin hajiya tayi suka mata sallama suka fice zuwa parking lot, wurin da motar sulaiman take yajeshi budewa qofar driveprp yayi yashiga ita kuma qofar mai zaman banza tashiga tazauna, key yayiwa motar suka fice.
Wai waye
Naxeer yanada aure, matarsa daya da yaro daya, bayan rasuwar mahaifinsa da waɗannsu shekaru yayi aure, wanda uncl dinsa ne ya nema masa auren, kuma alokacin dayake yayan nasa babban mutum ne ansan shi shiyasa basuyi wani binciken yaya naxeer din yake ba, wanda babban qalubale yake garemu Iyaye dan mutun dan babban gida ne yakamata abinciki halayyarsa bakawai a aurar da yarinya ba alhalin wannan wanda zata aura yanada wata dabi'a mai kyau ko marar kyau allah kasa mudace....ameeen👏****
Naxeer koda yakoma gidansa haka ranar yawuni ya sake-saken mafita can yayanke shawara acikin ransa wanda niba banji mi yayankeba sai nan gaba, matarsa mai suna nabeelah data shigo dakin haka tasameshi cikin tunani, tambayarsa meke damunsa tayi amma yace " mata bakomai hakadai tayita yi amma yayi shiru, hakan yasa ta kyaleshi tayi shirin bacci takwanta gefensa, cikin ransa yana allah-allah gobe tayi yaje office.Washegari dawuri yatashi yashirya cikin shigarsa ta ma'aikacin banki wato black suit, agurguje yashirya ko breakfast batsaya yiba, itadai nabeelah sai mamaki take me yasa yau yake sauri, duk da tasaba haka yake fita dawuri kasancewar duk wani ma'aikcin banki 6 suke fita aiki.
Koda ya isa bankin office dinsa kaitsaye ya wuce, aiki yafara yi na wasu takardu har wajen qarfe 8 sannan yafito yasamu wani security na wurin ya karban masa abu, cikin girmamawa security ɗin yakarba yawuce.
Bayan yakoma office dinne ya zauna, ajiyar zuciya yasauke tareda yin shiru alamar akwai abinda yake nazari, can saiga wannan security ɗin yashigo hannunsa dauke da food flask yamika masa sannan ya fice, janyowa wani madaidaicin table yayi sannan ya dora flask din akai tashi yayi ya shiga bathroom din office din ya wanke hannunsa da bakin sa, fitowa yayi sannan yasamu wuri yazauna bude kular yayi wanda ciki, dan wakene dayasha yaji da kayan hadi sai gefe kuma lemo ne maisanyi dakuma ruwa, dayake office dinnasa akwai wani mini show glass mai dauke da food flask, plate da spoon, spoon din set ne shida plate din, daukowa spoon din yayi, dawowa yayi ya zauna ahankali yafara cin abincin, lokaci zuwa lokaci yana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa.
Bayan yagama cine yashiga bathroom yawanke hannayensa yafito, wani drower yabude yadauko wani turare sannan yafesa ajikinsa miyarwa yayi yarufe.
****
Aysher ko suna barin gidan banki suka nufa, aqofar bankin yayi parkin wurin da aka tanada donyin parking, fitowa sukayi suka nufi shiga cinkin bank din na UBA, suna shiga office dinsa kaitsaye suka wuce, nocking ya haruna yayi daga ciki akace" yes come in" tura kofar yayi yashiga aysher da bayansa itama shiga tayi..........Vote
Comment
ShareAllah kasa mudace........ ameeeen
Alqalamin deejerleen....✍️
YOU ARE READING
QADDARA TAH
Non-FictionLabari ne akan wani hargitsetstsen family tareda wata yarinya mai suna aysher...? Wanda taga jarrabawa kala kala, tsangwama, tsana, sanadiyar yayanta da kuma yan uwanta da suke uwa daya uba daya.......yan uwanta basu sonta sbd abin duniya ya rufemu...