🔥🔥 *RANAR*🔥🔥
*BIRTHDAY DINA*
~Gajeren labari~*Story*
*And*
*Written by*
*Lashminzy**MARUBUCIYAR..........*
*Rayuwar ummiey*
*Rud'ani*
*Muneerah Muneer*
*Hukunci*
*Rayuwata Ce*
*Auren fansa*
And Now
*Zuciyar dan adam*
*Ranar birthday dina*________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com*PAGE* 4️⃣
"Tafiyar tasu bata wuci minti talatin ba suka iso anguwar tasu me cike da jama'a,, daidai kofar gidan me napep ya tsaya ta fito ta sallameshi sannan ta shiga dan madaidaicin plat dinsu mekyau da tsari, plat neh mai dauke da dakuna uku da palour biyu hade da kitchen sai kuma farfajiyar gidan mai dan girma, gidan dai ba laifi.
"A farfajiyar gidan ta hadu da ihsan diyar aunty ummi yar shekaru goma sha biyu da haihuwa, kamaninta daya da *Zaheerah* dan mahaifiyarta aunty ummi ta dauko hakama *Zaheerah* da ita take kama Amma kyawunta yafi nasu fitowa dukda suma ba laifi farfaru neh sunada kyau.
"Sanye take da kayan makaranta riga iya gwiwa da wando da hijabi har kaza, tana ganinta ta karaso wurinta fuskarta dauke da murmushi tana fadin "oyoyo aunty *Zaheerah*,,
Rungume juna sukayi *Zaheerah* na fadin ihsan yammata daga islamiya kike neh, Ina sauran kannanki?"Da murmushi dauke a fuskarta tace "Eh mundawo break neh yanxu zamu koma, ta karasa maganar tana mai kwalawa kannanta kira. Suna fitowa suma suka ganta saida suka gaisa ta zaro nera dari ta basu, suka wuce cike da murna suna gode mata.
"Cikin gidan ta karasa shiga, ta tarar da aunty ummi a Palo tana cin abinci, gaisawa sukayi suka dan soma hira, aunty ummi ke fadin tafiya zasuyi itada mijinta zasuje gombe wurin biki kuma ana zuwa makaranta bazai yiwu suje da yara ba shine takeson tazo ta zauna da yaranta kwana biyu zasuyi su dawo,, yadda tayi da fuskarta yasata fadin yaya habiba bata gayamaki bane?
Girgiza kai tayi alama eh, ta cigaba da cewa "Tadai ceh kina nemana na dauka maganar makaranta neh ince nima naji an fara registration jamb harma nayi magana da layla tace min daddynta yace ta jira ya dawo, ina tunanin kasar waje zataje ta cigaba da karatu.
"Aunty ummi tace "toh ai ni banma san an fara registration ba, bari abbansu ihsan ya dawo in mashi magana ki bar batun layla su daban suke ba'a gasar su, karatu karatu neh duk inda kaje in Allah ya nupi ka zama wani abu ba makawa sai ka zama sai kiga keda kika zauna anan kin fita zama wani abu kirki, Allah dai ya kyauta.
"Can ciki *Zaheerah* ta amsa da ameen sannan ta amsa kiran daya shigo wayanta, wata kewarsu ce ke tambayarta lafiya kwana biyu bata ganta online ba, shuru tayi kamar bataji ta dinga fadin hello hello kamar da gaske ba'a ji dinnan.
"Tana ganin tashin aunty ummi ta maida kira take fadin Aysher dazu bana jinki sosai.
Aysher tace "Eh matsalar network neh, daman cewa nayi banganki online ba kwana biyu ina fatan lafiya?
"Lafiya kalau Eeeshert,
Shirye shiryen birthday yasa na rage chatting, kullum mutum up and down, gashi su mommy basu nan abubuwa sunyi yawa yanxu haka bana gida ina Oasis bakery muna maganar cake."Cike da murna Aysher tace woww! Am so happy na matsu ranar batayi ba kullum sai nayi mafarkin na ganki wallahi, dake basu taba haduwa ba shiyaasa take mazarin ganinta.
Dariya *Zaheerah* tayi wacce taji kanta ya kara fasuwa ta cigaba da zukaka mata karya son ranta hadda fadin tace mommy tazo ma kawayenta da tsaraba, aikuwa Aysher tayi ta murna hadda shiga group dinsu na *Fashion ladies* ta fesa musu labari da dumi dumin shi...