🔥🔥 *RANAR*🔥🔥
*BIRTHDAY DINA*
~Gajeren labari~*Story*
*And*
*Written by*
*Lashminzy**MARUBUCIYAR..........*
*Rayuwar ummiey*
*Rud'ani*
*Muneerah Muneer*
*Hukunci*
*Rayuwata Ce*
*Auren fansa*
And Now
*Zuciyar dan adam*
*Ranar birthday dina*________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com~Wannan shafin na kune yan kungiyata arewa writers asso, ina kaunarki sosai💔~
*PAGE* 7️⃣
"Gudu yake tsalawa babu sassauci kamar zai tashi sama, idonshi ya rufe bakidaya ko ganin hanya bayayi sosai, bishi bishi yake gani tsabar gudun da yakeyi, dukda dare neh hakan bai hanashi tsala gudu ba dan yadda zuciyarshi ke tafarfasa yasa gabadaya ya manta inda yake burinshi kawai ya ganshi gabanta.
"Cikin ikon Allah ya iso hadadden hotel din, tun daga nufatowarka zaka dinga jin sautin kida na tashi, dake kuma dare ya tsala ababen hawa sun rage tafiya da hanyaniyar jama'a, ko'ina yayi shuru sai daidai kun ababen hawa da mutanen da baza'a rasa ba, hakan yasa karan kidan fitowa sosai yadda ko nesa kake da wurin zaka dinga jin duma na tashi.
"A hasale ya ida isowa bakin gate din wanda a wangale yake kana ganin farfajiyar wurin, sai masu gadi guda biyu, dukansu sanye suke da uniform babbaku da huluna yellow, daya na bangaren fita daya bangaren shiga,
"Dake ba'a hayyacinshi yake ba baiko lura da rubutun dake kofar ba wanda yake radorado an rubuta IN & OUT waton hanyar shiga da hanyar fita kenan, Saboda rikicewa hanyar OUT ya nupa,
"Megadi na ganinshi ya karaso hannunshi rike da scanner, fuskarshi a daure, cike da kwarewa a aikinsa yace "Malam daga ina haka kamar an koroka? Zuciyarsa na masa wani irin suya yana fidda huci mai zafi yace "Ciki zan shiga ana party ko?
"Batareda tunanin komai ba yace eh Amma ba wannan gate din ake bi idan za'a shigo ba, ka koma wancan, ya fada yana pointing daya gate din dake kusa dashi.
"Bai wata wata ba ya nupi gate din aka bude masa, megadi yayi scanning dinsa saboda tsaro kafin ya bashi izinin shiga,,
"A tsakiyar farfajiyar wurin ya paka mashin din nashi da ko pakuwa dakyau baiyi ba,
Kaitsaye inda yaji sautin kida na tashi ya nupa."A bakin kofar shiga hall din yaci karo da megadi wanda zaune yake shima saye da uniform irin na masu gadin bakin gate,,
Ba'a bashi izinin barin kowa ya shiga ba saida gate pass, dan *Zaheerah* harda kati ta yanka yafi dari duk wanda zai shigo sai yaje reception ya anso kafin a bashi izinin shiga."Hannu ya mika masa, yadda ya gansa dan dattijo yasa cikin girmamawa bayan ya gaida shi yace "Baba ina katin ka?
"Cikin dacin rai da haushi yace "katin gidan ubanka? Toh dakai da kati kunci gidanku ya karasa maganar hade da masa dakuwa da hannuwanshi, ya raba gefenshi zai wuce, megadin yayi saurin taroshi yana fadin gaskiya bazaka shiga wurin nan ba saida kati.
"Malam muhammadu kuwa tuni ranshi ya gama baci, yana kokarin hankadeshi zai shiga ciki Amma sam yaki bashi dama,, cecekuce neh ya kaure a tsakanin su, tsabar dumar dake tashi yasa duk jama'ar wurin basuji hayaniyar su ba, wani wawan naushi yakaiwa megadin wanda yasashi zubewa kasa yana dafe cikinshi.