7&8

619 61 9
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

😭 *TSANTSAR BUTULCI*😭
                  2020
    
*Written By:-*
    _Ameera Adam_
                _AmeeraAdam60_
              *@Wattpad*

☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
   FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*

*SADAUKARWA GA MAHAIFIYATA ALLAH YA KARA NISAN KWANA AMEEN.*

              7&8

A sanyaye farida ta kalli mahaifiyar tata cikin tausayawa tace, " Inna bakin gada fa, acen zamu kare rayuwar mu kenan? "
      Farida bamuda wata mafita da ta wuce wannan, sanin kanki ne rayuwa tayi tsada, taimako yayi wuya, afadin garin nan ki gayamun ina zamuje mu tsugunna daya wuce bakin gada, cen ne zamu yi rayuwar mu bame tashinmu bamuda fargabar kudin haya sai dai mu dinga neman na Abinci, kinsan bakin da Allah ya tsaga baya hanashi abinci " Inna ta fada.
    " To Inna Allah ya kawo Mana dauki" cewar farida.

     Tafiya sukai sosai sannan suka karaso titi, Dan sahu suka tara ya karaso dasu gyadi-gyadi, a gadar lado suka yada zango, agajiye suka zauna suna karewa titi da mutanen dake rayuwa agurin kallo, wata Mata suka samu azaune da alama gurguwa ce ta sa robarta agaba, duk Wanda yazo wucewa da irin rokon da take Masa.
     Tashi sukayi suka karasa gurinta.

     Da sallama Inna suka karasa gurinta, cikin sakin fuska ta amsa musu, bayan sun gaisa tsohuwar ta Fara roko kamar haka, " Ataimaka sadaka fisabilillahi sadaka saboda Allah da Annabi ku bamu na Annabi bayin Allah, yan Mata Allah ya kawo miji nagari kinji "
     Sororo su farida sukayi suna sauraronta, Inna ce ta danyi murmushi tace, " iya nidai sunana sadiya wannan kuma 'yata ce mahallin da muke ciki ne aka tashe mu, Kuma Bamu da gurin zuwa shine muka zo nan Dan mu zauna har Allah ya kawo Mana mafita......."
      Tun kafin Inna ta rufe Baki tsohuwar ta Fara sababi, " wato kuce zuwa kukayi ku samun Rani ko? Dan abin alherin da nake samu kukewa bakin ciki, shine kuka tarkato kuka dawo nan Kai duniya Allah ka rabamu da Dan bakin ciki "
     Farida ce ta cewa mahaifiyar ta, " Inna Dan Allah mu bar gurin tsohuwar nan, ga guri cen muje mu zauna inba haka ba wallahi sai ta Tara Mana jama'a "
   Hakan kuwa sukayi cen gefe suka koma suka zauna, zamansu keda wuya farida taga mahaifiyar ta ta fashe da kuka mara sauti hawaye na zuba, babu dadi taji cikin zuciyarta daurewa tayi ta Fara lallashin mahaifiyar tata.
  
   Cikin kuka Inna tace, " farida Wai yau mune zaune abakin gada, Allah ya jikan malam nasan da Yana raye da haka baza ta taba faruwa damu ba, tabbas Allah baya barin wani Dan wani yaji dadi, Allah ya gafarta maka malam halinka na gari ya bika " Inna ta karasa magana tana goge hawayen fuskarta.
    Yar tsohuwa lokaci-lokaci take kallan su Inna tana watsa musu harara, ganin haka yasa suka juya Mata baya.
      Dan kullin kayansu Inna ta bude ta dakko musu daddumar sallah, purewater ta sai musu sukayi alwala sannan suka gabatar da sallar la'asar.

   Suna nan zaune sun zubawa sarautar Allah ido har magariba ta kawo Kai, Yar tsohuwa ce ta hada Dan buhunta da sandarta tazo wucewa ta kusa da su Inna zata tafi, harara take watsa musu sannan tace, " to yan bakin ciki na bar muku gurin zuwa safiya sai ku tara bankin najeriya gaba daya "
        Da ido suka bita ba Wanda ya tanka Mata har ta samu ta tsallaka ta hau mota.
        Bayan sallar magriba Inna ce ta bawa farida kudi ta tsallaka titi gurin wata me shinkafa da wake wacce ta gefen gidan man AA. RANO abinci ta siyo musu ta kawo musu sukaci sukayi kat suka kora da ruwa.
      Suna nan zaune zuru suna kallan yanda mutane suke gudanar da al'amura har dare ya farayi, farida gajiya tayi da zama ta kunce kullin kayansu wani tsumman zanin gadonsu ta zaro ta shinfid'a ta kwanta ba jimawa bacci yayi gaba da ita.

      Inna tana nan zaune har kafa ta Fara daukewa, sai manyan motoci da suke wucewa, tuna irin rayuwar da tayi abaya tayi, da irin gatan da tasamu wajen mahaifiyanta har zuwa aurenta da malam, hawaye ta share ta jingina tana nazarin rayuwa.
    Inna na nan zaune har bacci barawo yayi awon gaba da ita.

    Nesa-nesa cikin bacci take jiyo Kiran sallar Asuba, sai alokacin ta tuna da basu tanadi ruwan alwala ba uwa uba kuma gurun da zasu yi tsarki, gefen wuyanta taji ya rike saboda baccin da tayi azaune, Dan shafa gurin tayi ta tofa yan addu'o'i.

Waige-waige Inna ta farayi tana hange ko zata hango wani gurin da zasu samu ruwa, tsallawa tayi ta tana duddubawa, ta dade ahaka Bata samu ruwa ba wasu masallatan har sun Fara sallah, wani tuka-tuka ta hango da sauri ta Kara gurin ta Fara bugashi, Tunowa tayi da babu abinda zasu dibi ruwan dashi suyi alwala.
      Komawa tayi ta taso farida suka koma gurin tuka-tukan, dube-dube suka shiga yi cen nesa suka hango wata leda daukota sukayi suka wanketa, suka Debi ruwa aciki kadan-kadan take zuba ledar, wani lungu suka hango da baya bulla  daga jikin wani shago, farida ce ta Fara karewa Inna tayi fitsari sannan farida ta Kara debo ruwan Inna ta kare Mata itama tayi fitsarin, sannan suka dawo sukayi Alwala suka koma suka gabatar da sallar Asuba.

       Gari ya Fara haske mutane sun Fara gilmawa kowa Yana harkar gabansa, koko da kosai Inna ta aika farida tsallake ta karbo musu gurin wata bayerabiya, hijabai suka shiga suka ci suka sha sannan suka koma gefe suka Dan Fara Hira.
       Zuwa wani lokaci Yar tsohuwa suka hango ta taho da Yar sandarta a hannu, wucewa taxo yi tana watsa musu mugun kallo.
      Yanxun ma ba Wanda ya kulata ta je gurin zamanta ta zauna.

       A kwana atashi ba wuya agurin Allah, sun Inna suna bakin gada har kusan kwana goma, Dan kudin hannun Inna ya kare tas, banda ma Allah yasa musu albarka dasu take musu komai ci da Sha, ga wani gidan wanka da ta roki mutumin suke zuwa, da kyar ya amince saboda yace Mata na maza ne basa barin Mata shiga, alfarma ta roka akan cewar da duku-duk zasu dinga zuwa suyi wanka da duk wani Abu da zai kaisu band'aki, hakan ne yasa ya amince suke biyanshi suyi abinda Zasuyi su koma bakin gada.

       Tun su Inna najin kunyar bara har suka zage duk mutumin da yaxo wucewa zasu fara rok'onsa, duk tsawon Rana baifi su Sami dari biyu zuwa dari biyu da hamsin ba, saboda mutane na ganinsu dakau da lafiya suke bara, hakan ne yasa mutane da dama sai su tsallakesu su bawa Yar tsohuwa sadaka.
         Ranar da suka cika sati biyu tashi sukayi ko na karyawa babu, ga kayan jikinsu kamar basu taba ganin ruwa ba, Inna ce ta cewa farida, " farida me zai hana ki dinga tsallakawa gidan mancen bara ko mafi samun na abinci, ni sai inzauna anan Kinga mun raba kafa ke inbaki samu ba ni ko Yaya ne zan Dan samu "
  
   Amsawa mahaifiyar ta tayi, hakan kuwa sukayi farida take tsallawa gidan mai ita kum Inna na bakin gada, ba laifi sukan dan samu kusan dari hudu dari biyar arana, ahaka-ahaka har suka shafe wata guda suna rayuwa akasan gada.

          SADIQ matashin saurayi ne da bazai wuce shekara Ashirin da bakwai zuwa da takwas ba, Yana aiki ne akarkashin gidan man AA. RANO dake gyadi-gyadi sune masu sayar da petir aciki, tun ranar da farida ta Fara shiga gidan mai ya d'ora idansa akanta, cikin zuciyarsa yake mamakin kyakykywar yarinya me kuruciya kamarta ace tana yawon bara, sai yayi kamar zai Mata magana sai Kuma zuciyarsa ta gargadeshi, abinda yake kara bashi mamaki magariba na karatowa zai nemeta sama ko k'asa ya rasa, sab'abanin mabaratan da suke kaiwa har kusan goman dare.

    Wannan Karan alwashi yaci sai ya sa mata ido yaga sanda take tafiya, idanunsa na Kan farida har ta tsallaka gurin Inna, duk atunaninsa yayi zatan zuwa wani lokaci suke barin gurin, Abinda ya daure mai Kai gani yayi kullin tana tashi saidai ta tsallaka kasan gada ta zauna.
     Yau ma kamar kullin farida ta tsallaka kasan gada, Sadiq ya ayyanawa zuciyarsa cewar ya tsallaka yayi Mata wasu 'yan tambayoyi ko kansa ya bude ya samu Karin haske.
     Bayan ya tashi yaje ya cire uniform din sa ya sako kananan kaya ya tsallako kasan gada gurinsu Inna.

_Da kyau masoya naji dadi kwarai da yanda kuka karbi wannan littafin da hannu dubu-dubu naga ruwan comments dinku inayinku irin sosai din nan ana mugun tare._💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼

_Vote_
_Commets_
_Share_

      _MUM ASLAM Ce_ 😉

TSANTSAR BUTULCI COMPLETEWhere stories live. Discover now