11&12

553 38 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

😭 *TSANTSAR BUTULCI*😭
                  2020
    
*Written By:-*
    _Ameera Adam_
                _AmeeraAdam60_
              *@Wattpad*

☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
   FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*

*SADAUKARWA GA MAHAIFIYATA ALLAH YA KARA NISAN KWANA AMEEN.*

              11&12

Da sallama ya shiga cikin gidansu, Kai tsaye dakinsa ya wuce ya je ya rage kayan jikiinsa ya fito, d'akin mahaifiyar sa ya shiga ya sameta akwance kan daddumar da tayi sallah, da alama bacci ne yayi gaba da ita bayan ta idar da sallah.
           Sadiq tunda ya zauna yake tunanin hanyar da zai bullowa mahaifiyarsa Dan ganin ta fahimce shi, nepa aka kawo musu hasken d'akin ne ya tashi umma daga bacci, tashi zaune tayi tana kallan Sadiq dake Kan kujera ya hada Kai da gwiwa, kiransa ta farayi shiru bai amsa ba harsai da ta kirashi sau uku sannan yayi firgigit yace, " na'am umma barka da dare "

  Kallan sa take ba tare da ta amsa ba, tsarguwa yayi ya Fara sosai Kai Yana sunkuyar da Kai k'asa.
   "  SADIQ " umma ta kirashi da babbar murya har sai da gabansa ya fadi.
   A hankali ya amsa, "na'am umma"
     " Na lura kana cikin damuwa na tambayeka kaki gayamun, Wai shin Sadiq ko kana da wacce zaka gayawa da ta wuce ni, duk kauce-kaucen da kake yi ina lura da Kai kana tunanin zakamun wayo ne, nifa na haifeka duk wata dabara da zaka mun ay saidai inkalleka " umma ta karasa fad'a tana kallan Sadiq.
      " Dama umma ina Shirin sanar Miki ne sai Kika tambayeni, wallahi wasu bayin Allah ne suke bukatar taimako, basu da hali ko kadan akarkashin gadar wajen aikin mu fa suke kwana ita da yarta, umma sitirar kirki basu da ita abincin da zasuci ma bara sukeyi, shine dama nace zan sameki inroki alfarma Dan Allah umma ki bari inkawosu gidan nan su cigaba da zama " cewar Sadiq.

    "  Toooo too to, wato Abinda yasa ka tunani kenan ba dare ba Rana, to idan ka kawo su nan yaushe zasu tafi, Wai ma intambayeka basu da dangi ne su? Ko su biyu kawai suka rage aduniya ? Sadiq shifa mutum ba abin yarda bane kaje ka janyo mutum daga Rana Kai ya turaka wuta, gaskiya bazai yuwu ka dauko mutanen da Bamu sansu ba bamusan asalinsu ba ka kawo su mu dinga kwana dasu ba, azo awayi gari su yanyanke Mana kawuna su tafi dashi Sam ka bazai yuwu ba, kama cire wannan tunanin daga zuciyarka" umma ta fad'a cikin bada umarni.
      Sadiq kamar zaiyi kuka ya Fara magana, " umma Dan Allah ki fahimci manufata karki musu mummmunan fahimta, duk Wanda ya taimaki wani Allah zai taimakeshi, wallahi umma bazasu cutar damu ba Kuma..........."
      Katse shi umma tayi, " Kuma me? Ni fa na gama magana karka cikani da surutan banza idan wannan maganar zaka cigaba da mun ka tashi ka bani guri " ta karasa fad'a cikin tsukewar fuska.

   Tashi yayi Kai tsaye dakinsa ya wuce Kan katifarsa ya fad'a, wani Abu nayi Masa d'aci a makogaronsa, kwana yayi Yana tunanin halin da su farida suke ciki musamman yanda yaga take jin jiki, kusan baccin Daren da yayi rabi da rabi ne, har Allah-Allah yake gari ya waye yaje yaga halin da take ciki.

          Yana karasa wa gyadi-gyadi Kai tsaye karkashin gada ya wuce, umma na zaune farida na kwance kudundune cikin bargo, da sallama ya karasa gurin Inna, tayi mamaki kwarai da ganin sa sassafe haka, amsa masa tayi ta Fara tambayar jikin farida, " mama ya me jikin ta kwana? "
     " To jiki dai gashi da sauki za'a ce amma zazzabin har yanxu bai sauka ba, ciwo ne ke shiga lokaci daya sauki sai ahankali " cewar Inna.

       Cikin tashin hankali Sadiq yace, " a'a mama baza'a sawa farida ido tana cikin wannan halin ba, bari na tsallaka na dawo ku shirya kafin na xo sai mu kaita asibiti " ya karasa fad'a Yana tashi daga gurin.
      Inna ba karamin Dadi tajiba, ruwa tasa ta wanke kafa da hannunta, ta tashi farida jikinta duk ba kwari ko bude ido Bata iyayi, wani hijabin Inna ta dauko ta sa Mata itama ta cenza wani hijabin suka zauna jiran Sadiq.
        Inna cikin zuciyarta take fadin, " tabbas Allah ya kawo Mana yaron nan ne cikin rayuwarmu Dan ya taimake mu, Allah mungode maka Allah ka Kara rufa Mana asiri.

  Sadiq na karasawa gurin babbansu ya karasa ya dauki permission, ce musu yayi  kanwarsa ba laifiya zai kaita asibiti idan sun gana da wuri zai dawo inbasu gama da wuri ba Kuma sai gobe.
         Yana tsallakowa su inna suka taso, Inna ce ta rike farida har suka shiga adaidaita sahu, wani private hospital ya kaisu dake unguwar zoo road, shigarsu keda wuya likitoci suka karbi farida, ruwa suka Fara sa Mata da allurai sannan suka dauki jininta test kala-kala sukayi Mata zuwa wani lokaci zazzabin har ya sauka, bacci ya dauketa sakamakon alluran bacci da Tasha.

            Lokacin da Sadiq ya shiga dakin umma ta shiga toilet, tsayawa yayi Yana karewa kyakykywar fuskarta kallo, fuskarta tayi wasai ta fad'a tabbas zazzabin ba karamin kamu yayi Mata ba, wayarsa ya Ciro ya Fara daukanta hoto Motsin fitowar Inna yaji ya koma kujerar da ke gefe ya zauna.
      Inna ce tace, " Sadiq har ka shigo"
     Murmushi yayi yace, " eh mama na duba reception ne ay bakyacen shine nace bari na leko nan "
       "Sadiq" ,Inna ta kirashi, " banida bakin da zan gode maka mungode kwarai Allah yayi maka albarka Allah yaja da ran mahaifa........."
     Katseta ta yayi da, " Dan Allah mama ki daina gode mun farida kamar kanwa na dauketa, Abinda zanyiwa kanwata shi zanyiwa farida fatan dai Allah ya Bata lafiya.
     Gaba daya suka amsa da" Aameen"

Sai wajen yamma farida ta tashi ruwan tea Sadiq ya karbo Mata tun bayan da aka sa Mata ruwa flask ya ara agurin wata nurse ya siyo mata aciki, magani Tasha ba laifi jikin nata ya danyi kwari, alwala taje tayi ta gabatar da sallar azahar, tana Kan dadduma taji shigowarsa, tashi tayi zata nad'e daddumar yace, " barta agurin bari na zauna akai "
       Inna na zauna Kan kujera tace, " ga guri man kazo ka zauna "
    " A'a mama nan ma yayi " Sadiq ya fad'a.
       Inna taso ta fahimci wani Abu daga gun Sadiq Amma sai tayi tunanin halin da suke ciki, wata zuciyar ma tace Mata, " yaro Dan gayu kamar wannan me zaiyi da wata farida, kawai dai tausayi ne gareshi da jin Kai.
          Bayan zaman Sadiq Inna duk sai ta kasa sakewa tashi tayi ta fita reception ta zauna.
         Farida sunkuyar da kanta kasa tayi, tana San yi masa magana tana jin wani kwarjininsa azuciyarta.
      " Yah jiki? " Taji ya ce Mata.
        D'ago da kanta tayi karaf suka hada ido, saurin sunkuyar da kanta kasa tayi, ahankali tace, " da sauki " runtse ido yayi saboda wata irin kuwwa da yaji muryarta tayi Masa akunne, bai gama fita daga wancen tunanin ba ya tsinkayi muryarsa tace, " mungode da taimakon da kake mana Allah ya saka da alheri "

        Shiru ne ya biyo baya taji bai Bata amsa ba, dagowa tayi taga Yana dan Danna waya kamar bai ji Abinda tace ba, sai yanxu ta tab'a kare Masa kallo cikin zuciyarta take fadin, " tsarki ya tabbata ga Wanda yayi wannan kyakykywar halittar, gashi  black beauty Amma kyakykywa ne, nasan dai duk kyansa ba Abinda zai nuna mun " ta fada cikin zuciyarta.

        Duk kallan da farida take Masa Yana kalle da ita ta gefen ido, dariya yake cikin ransa afili Kuma ya tsuke fuska yace,  " yan Mata wannan kallan fa "

      A kunyace farida ta kunyar da kanta kasa Bata bashi amsa ba, cikin zuciyarta tace, " au dama Yana kallona, kema me ya kaiki Kika wani kare Masa kallo kamar yau Kika Fara ganinsa, haba farida karki bada mata Mana " dayar zuciyar tace Mata, " to ke wane bada Mata zakiyi bayan mutumin Nan yasan sana'arku ya Kuma San makwancinku, to Wai ma duk wannan tunanin da kikeyi na meye taimakonki kawai yayi fa ......... "
       Ringtone din wayarsa ce ta katsewa farida tunanin da take yi, daukar wayar yayi da murya  kasa-kasa yace, " Assalamu alaikum, ranki ya dade barka da wannan lokacin "
      Daga daya bangaren umma ce ta amsa da, " barkanka dai Dan Albarka ya aikin? "
         Ya amsa da, "wallahi alhamdulillah, kashe bari na kiraki kar kudin wayar taki ya kare "
   Kashe wayar umma tayi.

     Wani kululun bakin ciki ne ya tokare farida jin yanda yake waya kasa-kasa cikin zuciyarta tace, " da alama da budurwarsa yake waya har yana cewa Wai ta kashe wayar zai Kira " guduntun tsaki ne ya subuce mata Wanda batasan itama kanta tayi shi ba.

    D'agowa yayi ya kalleta, aykuwa ta tsuke fuskar kamar ba ita tayi ba, murmushin gefen baki yayi sannan ya Danna number umma, tana dauka ya tashi zai fita Yana cewa, " yau tun safe kinji ban kiraki ba wallahi abubuwa ne suka Sha mun Kai " yana gama fada yasa Kai ya fice.
        Da idanu farida ta bishi tanajin wani haushinsa azuciyarta, komawa tayi ta kwanta ta rufe idanta kamar me bacci, Amma kamannin Sadiq ne keyi Mata gizo a  idanta, uwa uba kuma sautin muryarsa da yanda taji Yana magana kamar bayaso, sai Kuma haushi ya kamata tunowar da tayi da budurwarsa yake waya, Kuma ga dukkan alamu yanaji da ita.
      Motsin kofa taji tana bude ido taga ya dawo, Kara rufe idanta tayi kamar wacce bacci ya dauketa.
    Sadiq zama yayi ya dau wayarsa ya cigaba da yan danne-dannensa.

_Vote_
_Comments_
_Share_

      _MUM ASLAM Ce_😉

TSANTSAR BUTULCI COMPLETEDonde viven las historias. Descúbrelo ahora