MARYAMA MARYAM 9.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.Lokacin da ƙiranta ya samesa yana zaune abin duniya duk yabi ya ishesa.
Bayan ta faɗa masa cewa ta amince za ayi auren amma kuma ya jawa Maryama kunne dan ta rainata kuma a fara ɗaura aurensa da Maryama daga baya ayi nata.Hakuri ya bata ya kuma mata alkawarin zai jawa Maryama kunne kuma ana yin wata biyu da aurensa da ita za'a yi nasu, kafin ta samu hankalinta ya kwanta ko wannan kaɗai ya bata tabbacin itace a zuciyarshi ba wata Maryama ba.
Bayan gama wayarsu ya duba agogo yaga bakwai da rabi na dare yana da isasshen lokacin magana da ita kafin sallar isha'i.
Fita yayi ya nufi part ɗinsu bayan ya shiga ya zauna Mami ta fito a kitchen.
"Umar kaine dama ka shigo na zata waɗannan yaranne."
Kunyar matarne ya kamasa ya sunkuyar da kansa ƙasa.
"Mami nine ya gidan.""Lafiya lau tun safe shuru har cigayarka nayi gurin Ammi nace ko ta kwace ka."
"A'a wallahi ban samu fita ba kwata kwata, Maryama fa?"
"Bata nan tana gurin Kaku tun safe, na rasa mai take bata haka gaba ɗaya ta ƙauracewa zaman nan kwanan nan."
Tashi yayi ya nufi waje yace.
"Bari in sameta a can."..
A ƙofar falon yayi sallama yana shiga tun da taji muryarsa ta tashi zaune daga kwanciyar da take bayan gama sallar magriba.
"Ina wuni Yaya."
Tace kanta ƙasa tana mamakin dama yana nan tsammaninta duk ya koma dan ta masa text ta ƙira sau biyu bai ɗauka ba ta ɗauka ya tafi aiki ya masa yawa.Zama yayi kusa da ita a kan kujeran da take ya zuba mata ido bai iya amsa gaisuwarta ba dan bashi yake buƙata ba yace.
"Magana nazo muyi Maryama ina so ki buɗe kunnuwanki da kyau ki jini.Shuru tayi zuciyarta na bugawa ta kasa magana ya cigaba da cewa
"Umar Faruq da kika sani yace miki yana sonki bashi bane wannan, wancan Umar Faruq ɗin daban, ina son kiyi ƙoƙarin cireshi a ranki in har kin sakashi, sannan ki goge shafin rayuwar da kuka gudanar dashi cikin wata ɗaya daya wuce, domin Umar Faruq Maryam yake so ba Maryama ba, Abba da Abbi sun yanke hukuncin haɗamu aure bayan samun labarin wai Umar Faruq yana son Maryama a rashin sani, sai dai na nuna musu cewa Maryam ce zaɓina wanda ya jawo fushin Abba a kaina, amma sun bani dama, damar kuwa shine in haɗaku ku biyun, na yarda na amince za'a fara ɗaura aurena da naki daga baya sai in auri zaɓin raina fatan kinji mai nace."Maganganunsa shigarta suke ɗaya bayan ɗaya wanda ko wani harafi yana samun gurbi cikin zuciyarta yana maye wannan soyayyar da take masa zuwa tsana da jin zafinsa tare da haushin kanta da ta kasa fahimtarsa lokacin da ya fara nuna mata yana sonta cewa dama shi ɗin ba zai taɓa sonta ba bayan abubuwan da suka faru a baya.
"Maryama!"
Ya faɗa da ɗan tsawar daya sata ɗago ido ta kalleshi tana kawarwa gefe tace.
"Kayi gaggawa Ya Faruq daka fara sanar dani cewa wancan marar kunyar kake so da baka sha wahala ba, da ni da kaina zanje na samu Abba na sanar dashi, ko da yake yanzu ma bata ɓaci ba zan iya sanar dashi dan nima Maryama bana son wannan haɗin."Sauƙar mari taji saman fuskarta yayin da ya tashi tsaye.
"Naji labari dama kin rainata to gargaɗina gareki wallahi daga rana irin ta yau bake ba Maryam dan ita ɗin ta fiki aji da sanin girmama na gaba da ita banza fitsararriya kawai."
YOU ARE READING
MARYAMA MARYAM
RomanceThe story about two beautiful ladies. It's all about limitless and intensely love. MARYAMA da MARYAM matasan ƴan mata biyu kyawawa da suka yi tarayya kan son ɗan uwansu Umar Faruq. Tun lokacin da ya tabbatar MARYAMA ce ba MARYAM ba zuciyarsa ta kas...