32.

490 70 19
                                    

MARYAMA MARYAM 32.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

Ya Faruq yana nan kwance cikin tunani aka ƙira sallar la'asar ya tashi yayi alwala ya tafi masallaci ya dawo gidan bai tsaya ko ina ba sai falon Abbi da yayi sallama ya shiga ya samu guri ya zauna ganin yana lazimi.

Sai da Abbi ya gama addu'o'insa ya shafa kafin ya juyo yakai dubanshi gurin Ya Faruq yace.
"Umar naji kana nema na lafiya? Ya kuma naga haka kun fasa tafiyan ne?"

Kan Ya Faruq ƙasa yace.
"Eh Abbi dama wani ɗan matsalane.."
Sai kuma yayi shuru ya kasa ƙarasa maganar.

Lura da hakan yasa Abbi cewa.
"Lafiya wani irin matsala kuma Umar."

Shuru yayi sai da Abbi ya sake magana yace.
"Abbi dama akan Maryama ne na mata magana ta shirya ta nuna rashin amincewa shine nace ko za'a mata magana."

"Ita Maryaman?"
Abbi ya tambaya da mamaki Ya Faruq ya ɗaga masa kai.

"Shikenan zan mata magana ku shirya gobe ku wuce tun da yau lokacin ya tafi."

Godiya Ya Faruq yama Abbi ya tashi ya fita Abbi ya bishi da kallo yana murmushi da hamada da Allah da ya kawo masa ranar da Umar Faruq ya nuna damuwarsa akan Maryama.

Fitarshi Mami ta shigo gurin mijinta anan ya sanar da ita ko tana da masaniy.

Da mamaki tace.
"Bai sanar dani ba amma ko lafiyar Maryama bansan yaushe za tayi hankali ba bari in mata magana."
Mami tace tana tashi Abbi ya dakatar da ita.

"Ki ƙirata nan muyi magana da ita."
Yace mata ta fita har ɗakin Maryama ta shiga Maryama na ganin Maminta ta tashi zaune za tayi mata magana Mami tace.
"Ki same ni falon Abbinki."

Daga haka ta fita ta barta jikinta a sanyaye ta tashi ta saka hijab ɗinta ta fita har ƙofar falon ta tsaya sai kuma ta kasa shiga jin motsin mutum yasa Abbi cewa.
"Shigo mana waye haka Auta ce?"

Jin Abbi ya lura da zuwanta ya sata shiga ta samu guri ta zauna Mami ta shigo ta zauna tana kallon Maryama Abbi ya dubi Maryama yace.
"Auta na mai ya faru tsakanin ki da yayanki yace zaku koma kince a'a."

Shuru tayi kanta ƙasa ta kasa magana har sai da Mami ta mata tsawa.
"Ba dake ake ba."

"Ni Mami bana sonshi ya bani takardata."

Da mamaki dukkansu suke dubanta bayan sauraron maganarta Abbi yace.
"Ko mai yasa kika faɗa haka."

Shuru tayi sai kukan da take tayi Abbi yace.
"Shikenan tashi kije."

Bayan fitarta Abbi ya kalli Mami yace.
"Sadeeya kin lura da abinda nake gani yarinyar nan akwai abinda yake damunta."

"Shirita kawai ke damunta ba komai."

"A'a akwai wani abun ta zauna zuwa kwana biyu mu gani."

Mami ba tace komai ba ta miƙe ta fita haka kawai Abbi yaji a jikinshi ƴarshin da damuwa a tattare da ita kuma ba zai barta ta koma ba sai yaga ta ware, tun da shi Umar ɗin ya hakura ya riƙeta ita ma ta zauna tsawon shekaru bai ga abinda zai sa lokaci ɗaya ta ce bata son auren ba.

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now