43.

838 81 26
                                    

MARYAMA MARYAM 43.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

KARSHE KENAN.

Tura ƙofar ɗakin akayi aka shigo ya sata cire hannunta da sauri su kayi ido biyu da kaku da ta sake kunun hannunta ta nufo ta tana cewa.

"Yanzu ke Saleema rashin imaninki ya kai haka, kasheta za kiyi, muguwa azzaluma dangin mugaye ajiyeta kuma wallahi sai kin bar gidan nan tunda kisa kika fara."

Cikin rawar jiki Momy ta ajiye babyn bata taɓa tsammani wani zai sameta haka ba ko Maryama da take bathroom bata tsamman zata ganta ba sai wannan tsohuwar.

Cikin sauri Momy zata fita Kaku ta saka mata kafa ta faɗi ta hau jibgarta tana zaginta da hakan shi ya jawo hankalin ƴan gidan da Maryama su kayi gurinsu da kyar Mami ta hana kaku, Kaku tana cewa.
"Ki barni Sadeeya kafin ta kashe min mai sunata gwara ni na fara kasheta kuma bari Haruna ya dawo sai ya mata saki uku a gabana."

Dakyar Mami ta samu kaku ta hakura Momy ta samu ta fita da sauri tana shiga part ɗinta ta rufe dan gudun azo a sameta duk ta ruɗe kayanta ta fara haɗawa ta san dai karshenta in Abba yazo Kaku ta sakashi ya mata saki kafin ya saketa gwara ta bar musu gidan.

Kowa da yaji abinda Momy tayi sai da ya girgiza musamman Maryama data tsorata da lamarinsu.
Ƙin faɗa Ya Faruq aka yi gudun fitina.

Har dare kaku tana part ɗin Ammi dan jiran Abba yana dawowa ta tareshi tana faɗa masa tace kuma yanzu suje a gabanta ya rubuta mata takardarta.

Ranar da yake jira kenan ya hau sama ya dawo ya samu Kaku yace suje.

A ƙofar falon Momy suka tsaya ya ƙwanƙwasa ta tsaya bakin kofar tace.
"Waye?"

"Ki buɗe mana ki gani kin san baki da gaskiya kika rufe kanki ai."
Kaku tace tana buga kofar.

Abba ne ya hanata yace.
"Ki buɗe Saleema magana za muyi."

A hankali ta buɗe kofar falon Abba bai shiga ba ya kuma hana Kaku shiga ya ciro papern aljihunsa ya wulla mata.

"Ga sakamonki ban taɓa cutarki ba sai ke da kika cuceni kika rabani da wacce zan aura, duk hanyar da zan bi na rabu dake dama nake nema gashi yau kin kawo ranar da kan ki, na baki mintuna ashirin ki fitar min a gida."

Daga haka yaja Kaku tace.
"Sai aje aci gaba da zawarci."

Daskarewa Momy tayi a gurin dama ta sa a ranta sakin zai mata amma bata taɓa tsammani haka da wuri ba.
Ɗakinta ta koma kayanta data har haɗa ta ɗauka ta sauƙa ta fita a gidan sai gidansu.

Mahaifiyarta na ganinta tace.
"Ke lafiya da dare haka zaki zomin?"

"Ya sakeni saki biyu, ki taimaka min Mama."

"In taimaka miki wanda zai taimaka mana ba kinje kin mishi rashin kunya ba to sai ki zauna muci gaba da zawarci ni dake da ƴarki."

"Ban yafe miki ba kin cuceni kin cutar dani kin ɗaurani hanya marar kyau na ɗaura ƴata gashi yanzu duk mun shiga wani hali dalilinki ƴata ta gujeni dan mugun halina."

Duka Mama ta kaiwa Momy ta kauce ta hau zaginta.

...

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now