14.

392 54 2
                                    

MARYAMA MARYAM 14.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

Tashi tayi ta shiga bathroom ta wanke fuskarta ta fito ta gyara da powder ta ɗauki mayafinta ta dawo ta zauna tace.
"Na gama mu tafi."

D'ayan takeaway ɗin ya tura gabanta yace."Kici zai mu tafi."
Ya cigaba da cin abincinsa.

Har ya gama bata gama ba, taci sosai kafin tace ta koshi ya tashi suka fito ya kulle ɗakin su ka fita har gurin motarsa kafin su shiga yaja suna barin harabar gurin.

Yawo kawai yake da ita ƙarshe ya ɗauki wani hanyar ta kalleshi ba tace komai ba har ya yayi parking kofar wani gida yana fita yace.
"Fito."

Da idanunta manya ta tsareshi taki fita kuma taki masa magana yace.
"Gidan abokina ne zaku gaisa da matarshi ba zamu jima ba."

Sai lokacin ta fito ya rufe motar suka shiga cikin gidan har entrance ya danna door bell aka buɗe masa suka shiga suka zauna kafin mai akin tace bari ta ƙira matar gidan.

Tare suka sauƙo da mijinta yana ganin Ya Faruq yace.
"Dr dama kai ne lallai yau za'a yi ruwa da ƙanƙara."

Murmushi kawai yayi ya amsa gaisuwar matarshi data zauna kusa da Maryama.

Bayan sun gaisa mazan suka fita balcony matar Dr Ibraheem abokin Ya Faruq ta kalli Maryama da kanta ƙasa tace.
"Ni sunana Safiyya matar Dr Ibraheem abokin Dr, gashi bai taɓa haɗamu ba har aka yi aurenku duk da Dadyn Nuriyya ya dameshi da hakan."

Kan Maryama ƙasa tace.
"Kin san anyi abun a gaggawane."

"Gaskiya kam gashi gari ba ɗaya ba fatan dai ba matsala zaman aure sai hakuri."

"Ba komai wallahi yanzu ma gida za muje mu gaishesu."

"Yayi kyau bari in kawo miki abun sha."
Safiyya ta faɗa tana tashi ta nufi kitchen.

Ganin an ɗauki lokacin da yake buƙata su ɗauka ya cika yasa yace Dr Ibraheem za su koma sai wani lokaci zai zo mishi.

Ciki suka koma Safiyya na fitowa kitchen ta ga Maryama ta tashi.

"Ba dai tafiya ba." Ta tambaya tana ajiye abin hannunta.

"Zamu tafi wani lokaci zamu dawo." Ya Faruq ya faɗa mata.

"Gaskiya baka kyauta mini ba Dr ni da na ɗauka sai dare."

"Wani lokaci zamu dawo muku."

Har baƙin mota suka rakasu bayan Safiyya ta cika Maryama da tsara ba kafin su bar gidan.

Tafiya suke taga ya sake canza hanya ta dubeshi tace.
"Ya Faruq gidan fa yamma yanayi fa."

"Ai can za muje sai mun musu tsaraba ko haka za kije musu hannu empty."
Yace yaci gaba da tuƙinsa taga ya tsaya wani babban shagon ice cream da chocolate yace ta fito.

Fita tayi suka shiga yace ta ɗauki abu, rasa me zata dauka tayi gida ba yara ba amma ya sata, tsintar abubuwa kaɗan tayi wanda tasan in taje ma sai dai ta dawo dasu.

Da ta gama ya biya kuɗin suka koma mota yaja suna barin gurin maimakon taga ya nufi hanyar gida taga yabi hanyar da su bi suka zo ta buɗe baki tace.
"Ya Faruq.."

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now