🔆 *WིྀAིྀ'YིྀAིྀ KིྀAིྀSིྀHིྀEིྀ ZིྀAིྀHིྀRིྀAིྀ'Uིྀ?*🔆
➿➿➿➿➰➰➿➿➿➿*STΩRΨ ШRITTΣΠ βΨ*✍🏻
*ᴢᴀʜʀᴀ ᴀʙᴅᴜʟ*( *Պ✺Պ⑂ℵ ᾰℏℓᾰℵ*)
_my wattpad_@Fateemah0
*marubuciyar*
*H̸͟͞A̸͟͞L̸͟͞I̸͟͞T̸͟͞T̸͟͞A̸͟͞ D̸͟͞A̸͟͞G̸͟͞A̸͟͞ A̸͟͞L̸͟͞L̸͟͞A̸͟͞H̸͟͞ N̸͟͞E̸͟͞*
*G̸͟͞U̸͟͞D̸͟͞U̸͟͞ A̸͟͞ J̸͟͞E̸͟͞J̸͟͞I͟͞*
*S̸͟͞H̸͟͞U̸͟͞H̸͟͞A̸͟͞D̸͟͞A̸͟͞*
*N̸͟͞I̸͟͞D̸͟͞A̸͟͞ K̸͟͞A̸͟͞N̸͟͞N̸͟͞A̸͟͞N̸͟͞ M̸͟͞I̸͟͞J̸͟͞I̸͟͞N̸͟͞A̸͟͞*A̸͟͞n̸͟͞d̸͟͞
N̸͟͞o̸͟͞w̸͟͞*w̲̅a̲̅y̲̅a̲̅ k̲̅a̲̅s̲̅h̲̅e̲̅ z̲̅a̲̅h̲̅r̲̅a̲̅'u̲̅*
____________________
_sadaukarwan wannan littafi ga jarumai masu yi mana posting wanda nasani da sanda ban sani ba *YAYA HAYAT, HASSAN ATK,HUSAIN 80K, MU'AZ* kuna dayawa amma gdy da jinjina Allah ya biya_________________
_wannan book din ba free bane ga mai buqata zai biya #200 sai ya tuntube ni ta numb kamar haka_*_Maman ahlan_*
🤳🏻 08165550116
*__________________**بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________**FREE PAGE ONE&TWO*
Kwance take idanunta a lumshe fuskarta fayau,fara ce amma ba za ka ce mata sol ba, eyelashes ɗinta zara zara kwance luf a saman idonta dake lumshe, hannuwanta da kafafunta sun sha ƙunshi red&black Wanda da ka gani kasan na amarya ne ko ba a fada maka ba.
Gefe daya kuwa mahaifinta ne zaune dirshin a kasan tiles sai kuka ya ke kamar karamin yaro, a dayan gefe mahaifiyarta ce an rirrik'eta tana kuka tana fizge fizge kamar wacce ta kamu da cutar hauka domin ta gama fita hayyacinta! ga jami'an tsaro su na ta bincike, su na ta ɗaukar hoto.
ACP ne ya kalli Alhaji,ya ce.
"Alhaji dan Allah ka daina kukan nan haka,nayi maka alkawari In sha Allah sai inda karfin mu ya ƙare wajen binciko gaskiyar wanda ya shigo har gidan ka yayi maka wannan aika-aikan, ya kashe maka y'arka i promise."Cikin kuka ya fara magana.
"wa'ya kashe ki zahra'u!!? waye ya shigo har cikin gidana ya yi min wannan ta'addancin? duk camera da Securities da bodyguards din gidan nan, ya kashe min ke? dan Allah ACP ka taimaka min zan iya kashe ko nawa ne akan wannan case din,y'ata daya tilo,kuma a rasa ranar da za a kashe ki sai ranar auren ki!!?" Ya kuma sakin kuka har yana sharbe majina.Hajiya tana ihu tana fizge fizge domin
mata sun kai kusan goma waɗanda suka rirriƙeta.
"Wallahi karya ne!! karya ku ke yi munafukan banza munafukan wofi!! Alhaji karka yarda dasu Zahra'u bata mutu ba, jiya mun jima da daddare muna hira da ita har wajen 2:00pm sannan yanzu ku ce min ta mutu!!? daga kawai zuwa tashinta ta shirya, Dan Allah babyna ki tashi kinji?,Dan Allah ki tashi ban san ki da nauyin bacci ba, ga dubban jama'a mata da maza sun taro duk saboda ke babyna, har da yaranki na gidan marayu ma duk sun zo tayaki murna aure, ki tashi kinji lokaci yana k'urewa, dan Allah ku barni na tashi ƴata!" ta ci gaba da kokuwa ita da matan da suka rik'eta, sai kukan tausayin Umma suke yi, shi ke nan yanzu daga zuwa hidimar aure za a zarce da zaman makoki.Bincike sosai jami'ai ke yi, wuyanta ya yi jan shati bisa alama dai shek'eta da wayar wuta aka yi, kuma an nemi wayar wutan an rasa, ga kaya duk sun hargitse bisa alamu wanda ya kasheta sun sha dambe da shi, domin azabar fitan rai, ga shi shi makashin bai bar wata alama ba.
Waya ACP ya ɗaga ya yi dealing number , ringing biyu aka yi picking, wanda ya ɗauki wayar cike da girmamawa ya sara masa,kamar yana ganin sa,ya ce.
"yes Sir"
ACP ya ce.
" *DSP SARDAUNA* ka shirya yanzu ka taho gidan *ALHAJI ALIYU IBRAHIM MD."*DSP SARDAUNA, ya ce.
"Eh Sir, gani nan ina shirin zuwa wajen ɗaurin auren nema,na ga ya kusa shi ya sa nake sauri.""Dsp, idan ma shirin zuwa wajen ɗaurin aure kayi to ka canza, ka saka uniform din aiki ka taho yanzu-yanzun nan" ya katse wayar.
ACP, ya ce.
"Alhaji, pls ka daina kukan nan haka, ka kwantar wa da Madam hankali, wai ma duk ba wannan ba, shi angon ya sani kuwa?" girgiza kai Alhaji Aliyu ya yi ba tare da ya yi magana ba, ACP ya ce.
"to gsky ya kamata a sanar da shi, tun da auren karfe 2:00 za a ɗaura, ga shi saura yan lokaci qalilan"ɗaga waya Alhaji Aliyu MD ya yi yana neman layin *ZAYYAN* yana tunanin kalar tashin hankalin da Zayyan zai shiga ,to ma me zai ce masa ka zo gida yanzu amadadin zuwa wajan daurin aure an *kashe zahra'u?*
ya sake goge hawaye da majina.************
*ZAYYAN* tsaye a jikin drees'mirror
Yana shiryawa abokansa su na zaune su na hira ,sai tsokanarsa suke yi, yasha babbar riga fara sol da ita sai baza kamshin angonci yake yi,kansa ya kalla a mirror din ya hau murmushi "wow gaskiya yau ji nake babu wanda ya kaini farin ciki,zan mallaki abin da zuciyata ta ɗaɗe tana muradi kuma take so wato *Zahra'u"*
Daya daga cikin abokansa mai suna Salisu ya ce "wai irin wannan zumuɗi haka Zayyan? sai wani rawan kai ka ke yi."Kamal ya ce.
" a'a fa Salisu barsa ya yi,wlh Zayyan kayi dacen mata,da badin ba da sai na ce ka ɗauki ta karshe,dan Zahra'u
akwai ilmi, hakuri, hankali,natsuwa, daraja mutane, uwa uba kuma ga ta kyakkyawa,gasky ina tayaka murna abokina."Zayyan ya yi ihun dadi da murna gami da jujjuyawa a cikin babbar rigarsa ya ce.
"kai dai bari kawai, nan da awa daya da rabi,zan angwance, ka bari sai a lkcn ka ji dadin min murna, wani abu ma sai ance *an ɗaura auren Zayyan da sahibarsa Zahra'u* wayyo dadi barni da raina!!"
Suka kwashe da dry, ya ce "wai ina su Adam da Kabeer ne kam?" Salisu ya ce
"Su na parlour tun dazu" ya ce.
"okay Dsp Sardauna bai ƙaraso ba?"
Kamal ya yi dry ya ce.
"kasan fa shirin manya sai a hankali" Zayyan ya ce.
"dan Allah ku tashi ku gama shiryawa kun ga
lkc ya kusa wlh, bana so mu makara, yanzu saura awa daya da rabi a ɗaura aure,amma gamu cikin gida, plss ku tashi ina wayoyina suke ne?"Kamal ya ce.
" su na hannun Adam dazu kana wanka ya shigo ya ɗauka wai zai yi wani abu da shi ne"
"okay" kawai ya faɗa ya dauki rolex dinsa ya ɗaura dama already,sun gama yi masa wanka da turare ,ya zura takalminsa ,ya ce.
"ku tashi mu tafi" mik'ewa suka yi,har sun iso bakin kofa, Zayyan shi ne a gaba sai buga sauri yake yi kamar zai tashi sama,karo suka yi dasu Adam da Kabeer gabaki daya basu cikin hankalin su.Zayyan ya ce.
"Lpy dai ko? yana gan'ku haka wujiga-wujiga meya faru?" sun kasa mgn dan basu san me zasu
ce masa ba,illa zazzare idanu,da sukebyi cike da tashin hankali marar misaltuwa."Mtsww?! kun ga malamai idan ba za ku yi magana, ba ku wuce mu tafi plss lkc yana tafiya ga shi yanzu har 1:00, ga shi yau friday ne kar mu rasa sallah, ga kuma ɗaurin aurena" ya faɗa yana sakin murmushi yana neman hanyar da zai rab'a ta gefensu ya wuce, amma sun tsaye k'ik'am.
Kamal ya ce.
"wai Adam miye haka ne kam dan Allah ku wuce mu tafi mana"Adam ya ce.
" *AN KASHE ZAHRA'U*"da karfi Zayyan ya ce.
"whatt!!!!!?
Hahah haba Adam,ko dai ka fara shaye-shaye ne kam?"
Salisu ya dafa kafaɗar Zayyan ya ce.
"muma yanzu Abba ya kira yake gaya mana,wai an kashe zahra'u."Zayyan bai san lkcn da ya ban gaje su Adam da Salisu ba ya fita a sukwane , ko gani da kyau ma ba ya yi ,da lalube ya shige motarsa ya tayar da ita sannan ya figeta da mugun gudun gaske.
__________________
Alhamdulillah Allah yabani ikon rubuta dai-dai sannan muyi amfani da ita ,Allah yaqara mana soyayar shugaba S,A,W
________________
Ga mai bukatar cigaban buk din nan zai tuntubeni ta my phone numb*_MAMAN AHLAN_*
08165550116IDAN ACCT NE KO KATI SAINA JIKU
COMMENTS
&
SHARE
YOU ARE READING
WA'YA KASHE ZAHRA'U?
FantasyWA'YA KASHE ZAHRA'U? ABUN DA KOWA KE TAMBAYA KE NAN, AN KASHETA! A DAREN RANAR AURENTA, TO WA YA KASHE ZAHRA'U? KU BIBIYI LABARIN DAN JIN KALAR CAKWAKIYAR DAKE CIKI, ZA KU SAMI CMPLT DINSA A KAN NAIRA200 KACAL. vote comments and follow me pls