1-5

84 9 2
                                    

*BUTULCI KO HAUKA*
         💕💕.      💕💕         💕💕.       💕💕
    *Short story*
*Written By✍*

*FATEEMAH A.Y Umar*
  
  *✍(Zahra Faruk)*

*Gmail*
*xahrahfarooq@gmail.com*

*Wattpad*
*XahrahFarooq*

*Twitter*
*Official Xahrah Farooq*

*Snapchat*
*Official Xahrah Farooq*

*Instagram*
*Official Xahrah Farooq*

*Facebook*
*Xahrahh Faroouq*

*YouTube channel*
*AL'UMMA TV*
بسم الله الرحمن الرحيم

https://www.facebook.com/Xahrah-Farooq-Novel-110638730479676/

https://www.facebook.com/groups/227620608315825/

*Not Edited*

*Page*
*1-5*

......Tsaye suke cirko cirko , kamar wanda aka aiko musu da sak'on mutuwan wani mai mahinmanci a gunsu , Malam Barau yayi shiru kallo daya zaka mar ka gane tsananin tashin hankalin da yake ciki , ya had'a tagumi da hanun sa duka biyu , ba abunda yakeyi sai sauke numfashi lokaci zuwa lokaci cikin rashin sanin tudun dafawa, shidai yasa naira bayi dashi bare ya bawa mai gidan gashi kuma yau ne rana ta k'arshe idan bebayar da kud'in hayan ba mai gidan yace su tattara subar gidan tun kafin ya k'ariso , ina zai shiga shida iyalan sa? , tanbayan da yake yiwa kansa kwnan , ya sani sarai za'a samu wannan kud'in ahannun uwar gidan nasa saidai Sam ko da wasa yasan baza ta bayar ba shiysa ma yayi shiru be nema bah.

Ahankali ya juya yana duban inda Maryama take , hankalin ta a kwanta tana ta faman wak'e! tare da sakan d'iyar ta Hanan bisa cinyoyin ta tana mata lalube cikin gashin kanta, alaman bata da wani damuwa .

Girgiza kai yayi sannan ya juya yana maijin bak'in cikin abunda matar tasa take yi, cikin ransa ya furta Allah ya shirya ki , danma Allah ya ragewa aya zak'i y'ar taki Makahuwace, can kuma ya shiga istigfari a cikin ransa , dan 6acin raine ya sashi fad'an hakan.

Juyawa yayi ya dubi 6angaren da Sadiya take , zaune take ta had'a kai da gwiwwa , gefen ta Unaisa ce tana ta faman shar6an kuka! saboda ganin mahaifan nata a cikin damuwa , Allah sarki ya furta sannan yayi ajiyar zuciya duk da cewa be damu da matar ba , saidai yasan tana tsananin tausaya mar.

Be dawo daga duniyar tinanin da ya fad'a ba sai ji yayi ana watso musu kayan su waje tsakiyar layi , Sadiya ce take ta faman kai kawo tana bada hak'uri tana ihu!.

Da sauri Malam Barau ya dawo cikin haiyacin sa , matsawa yayi wajen yana matsar k'walla! , saboda bak'in cikin hakan ya yanki jiki ya fad'i...

Marmaya dariya! tasa harda shewa, tare da cewa "wallahi ko a jiki na , wai an tsinkari kakkausa , daman ba wani abun kirki kake tsinana minba sai zama cikin talauci wallhai kai da bbu duk daya ne..

Hanan ta lalubo hanun mahaifiyar tata , sannan tace "kai Mamah baki tsawwala ba kuwa?".

"Keh dalla barni , wani tsawwala be , aini na tsani talauci wallahi azamanin nan idan kinga ana haba gaba da miji ai basai nace komai ba kinsan yana da yan canji, Amma mutun yananan duk talauci ya cinye shi yiwa mai ciwon k'anjamau iya zan iya mar biyayya ko lalla6ashi, aikin banza ramar cinnaka , wama yasan ya ramer kekan idan kinji ana honey sweet heart ko mai love to daji babu tanbaya me arziki ne , yanzu ba talauci bane yajawo kike zaune bbu ido bafa hakan aka haifeki ba , a sama kika samu makanta kuma likitoti sun tabbatar da cewa zaki warke indai akwai kud'i, Amma ya kashe zuciya yak'i kaiki Sam ya kasa nemo kud'i ga girman kan tsiya , dalla zamu wuce bazan ma je gunba bare naga bak'in ciki talaka abun gudu ne.....

*Vote*

*Comments*

*Shere*

*Love you all my Fans*
💕💕💕

*Xahrah ceh*🏌🏼‍♀🏌🏼‍♀🏌🏼‍♀🏌🏼‍♀

*Show me love to Subscribe my channel*
*AL'UMMA TV*

BUTULCI KO HAUKAWhere stories live. Discover now