*BUTULCI KO HAUKA*
💕💕. 💕💕 💕💕. 💕💕*Written By✍*
*Fateema A.y Umar*
*(Xahrah Farooq)**Gmail*
*xahrahfarooq@gmail.com**Wattpad*
*XahrahFarooq**Twitter*
*Official Xahrah Farooq**Snapchat*
*Official Xahrah Farooq**Instagram*
*Official Xahrah Farooq**Facebook*
*Xahrahh Faroouq**YouTube channel*
*AL'UMMA TV*
بسم الله الرحمن الرحيمhttps://www.facebook.com/Xahrah-Farooq-Novel-110638730479676/
https://www.facebook.com/groups/227620608315825/
*Dedicated too*
*Hassan 80k*
*Muhammad Kareem*
*Mu'az**Not Edited*
*Page*
*16 too 20*........Jin ihun! Hanan , ya sata mik'ewa bbu shiri dan tasan Hanan ba k'aramar yarinya bace bare tayi ihun! ba tare da wani k'wakk'waran da liliba.
Shiga d'akin tayi tana cewa "yaya dai Hannatu ?" Me ya faru?".
Hanan cikin ihu! take magana ,"Mamah ido na wayyo Allah na wlhy bana ganin komai .
"To me ya fad'a idon naki ?" .
"Ba komai kwalli kawai nasa....
"Na shiga uku wani kwallin?".
"Ni dai a saman mirror na ganshi.
"Na shiga uku , kwalline na kar6o a can hayi akan zansawa d'iyar shegiyar nan , Unaisa gashi Hanan tasa yau ina zansa raina..
Daidai lokacin da take maganan Sadiya kuma tazo zata shiga d'akin , dan lokacin da taji kukan yarinyan tana wanka, wani rass! rass! taji zuciyan ta na bugawa , kawai sai hawaye!, mutuwan tsaye tayi agun saboda mamaki da kuma tsananin tashin hankali.
Agun Malam Barau yazo ya same ta.
"Keh Halima meye kikeyi anan?" , Kina jin y'ar abokiyar zaman ki na kuka baza ki duba ko lpy bah.
Sadiya kasa magana tayi sai kuka! .
"Ki min magana mana meyake faruwa?".
Dak'ar Sadiya ta bud'e baki ta fad'amar abunda ke faruwa.
"Subhanallahi , abunda yake faruwa kenan?" , Wannan shine k'aik'ayi koma kan mashek'iya , lallai duk wanda Allah ya bawa ni'ima amma ya butulce masa zaiga Aya, Allah ya kyauta , maza goge idanunki kizo muje d'aki muga halin da yarinyan take ciki.
Hawayen ta goge sannan suka nufi d'akin , cikin tashin hankali suka tarar da ita , takar wata mai ta6in hankali sai faman juyi takeyi a d'akin .
"Lafiya Maryama ?" , Cewar Malam.
"Yauwa Baban Hannatu gara da Allah ya kawo ka , daman kai nake jira mukai Hannatu asibiti.
"Meya same tah ?".
"Ina kitchen sai ihunta naji , abune ya shiga idon kuma tace bata gani .
"Bata gani kuma?".
"Eh bata gani .
"Keh Hanan zonan meye a idan naki ?" , Maza bud'e na gani kinji ga sweet na sayo miki kinji.
Hanan k'ok'arin bud'e idon ta fara amma abu yaci tura, kawai sai tasa kuka!, Abba ido na ya daina gani, Mamah ta cuceni bata sona.
"Mamah kuma?", Me Maman ta yi miki?".
"Tace min can hayi taje ta , gun wani Malam ya bata zata rufewa Unaisa ido dashi.
Kafin takai k'arshen maganan Uwar tayi maza ta doke bakin saiga jini, dan ubanki ni zaki yiwa sharri ?".
Mik'ewa yayi bece komai ba , kama hanun Hanan yayi akan su tafi saidai Maryama ta rik'e hanun yarinyan , ganin ana neman jimata ciwo yasa shi sakin hanun shid'in , kuma hanun Sadiya yayi suka fice daga d'akin.
Maryama hijab tasa tare da kama hanun Hanan suka bar gidan, kai tsaye asibiti suka je , an duba yarinyan an bata magani sannan suka koma gida saidai ba wani ci gaba da aka samu , tun daga wannan lokacin take neman magani har zuwa yanzu da Hanan take da 18yrs a duniya, ance su gawo 150 k , za'a yiwa Hanan aiki zata samu lafiya cikin yardar Allah shine yanzu take tara kud'in saidai har zuwa yanzu bbu ko dubu hamsin .
*Ci gaban labari*
Yanzu satin su guda da koma wa sabon gidan da aka basu su zauna, kullun sai ta cakali Sadiya da fad'a ganin tak'i kulata yasa tace zata sanja taku yanzu.
Yau kasan cewan Malam a d'akin ta yake da kwana , sunan kwance saida ta gama duk wani dabaran da zata samu Hajiya babba ta mik'e ,saita matsa nesa dashi bud'e ido yayi yana dubanta da mamaki , murmushin mugunta tayi ta girgiza masa kai.
"Haba Halima kina son ki had'u da tsinuwan mala'ikune?" .
"Uhm duk yanda kace danni bazan bari ka ya6amin k'anjamau bah....
Smile emotion
kisamu lalle mai kyau ki kwabashi ki hada da zuma ki saka farjinki sai ki samu man zaitun da beby oil ki dauko auduga ki rinka dangwalowa kina sakawa a farjinki wannan shine asalin matsi mai saka mai gida kyauta bayan haka sai kisamu kankana ki markadata ki hada da madara peak,hmm!👌🏼
*Vote*
*Comments*
*Shere*
*Love you all my Fans*
💕💕💕*Xahrah ceh*🏌🏼♀🏌🏼♀🏌🏼♀🏌🏼♀
*Show me love to Subscribe my channel*
*AL'UMMA TV*
YOU ARE READING
BUTULCI KO HAUKA
Non-FictionTirk'ashi Butulci ko hauka , littafi me cike da darusa...