*BUTULCI KO HAUKA*
💕💕. 💕💕 💕💕. 💕💕*Written By✍*
*Fateema A.y Umar*
*(Xahrah Farooq)**Gmail*
*xahrahfarooq@gmail.com**Wattpad*
*XahrahFarooq**Twitter*
*Official Xahrah Farooq**Snapchat*
*Official Xahrah Farooq**Instagram*
*Official Xahrah Farooq**Facebook*
*Xahrahh Faroouq**YouTube channel*
*AL'UMMA TV*
بسم الله الرحمن الرحيمhttps://www.facebook.com/groups/227620608315825/
*Not Edited*
*Page*
*56 too 60*........Lado bema kula da yanayin ta daya sanja bah, "Hajiya yanzu dai kar6i wayan nan Alhajin yace na kawo miki zaiyi magana ka da.
Firgigit! ta dawo daga duniyan tinanin da ta fad'a " Lado me kace?"
"Alhaji ne zaiyi waya dake.
"Ohk kawo toh.
Wayan Lado ya mik'awa Hanan jiki na 6ari!, kar6a tayi sannan ta matsa gefa.
"Hello Hanan , ya kike?"
"Ina lafiya ta bashi amsa .
"Ashe wayan naki ya 6aci ne , ai nayi ta Kira baya shiga yanzu dai kafin nace komai turomin account number dinki , zansa kudi saiki sayi waya ko .
Shiru Hanan tayi domin a zahirin gaskiya Hanan bata da account a bank , amma bata son tace bbu gudun karya raina tah, dan haka sai ta dake tace "account d'ina ya samu matsala ne , zan baka account no d'in me wayan nan kasa a ciki .
"Ohk akwai a guna ma bari nasa miki 500k , Hanan bata san nawa yake nufi ba amma tamar godia sosai .
"Kar ki damu ai kin wuce hakan, yanzu dai kina wani gari ne?"
"Ina Gombe ta bashi amsa jiki na 6ari .
"Gombe ?"
"Eh .
"Ahhhh! lallai fad'uwa tazo daidai da zama , wani unguwa?"
Take Hanan tamar kwatance tare da bashi cikakken address , sannan suka yi sallama ya kashe.
Lado ta mik'awa wayan sannan "ta ce yace zai turo 500k cikin wayan ka yanzu .
"500k ? yayi maganan yana girgiza kai , Allah mutumin nan yana da kud'i .
"Zaka cire ka kawo min ne?"
"A'a ai saidai muje banki a cire acan , dubu d'ari biyar ai da yawa, Allah dai ya k'ara arziki , wlhy nima dubu hamsin yaban kyauta .
Hanan sai da taji hantar cikin ta ya juya saboda kad'uwa , amma sai ta dake kamar ba ita .
"Ni zan shiga gida sai muje bankin gobe .
Hanan ta juya zata shiga gida sai ga , sak'o ya shigo wayar Lado , da sauri yace "Hajiya kinga ma ya turo kud'i , kafin ya rufe baki wayan ta fara k'ara sake mik'awa Hanan yayi .
"Hello Hanan kibar wayan a gunki dan ina zuwa yanzu .
"Ohk ba damuwa sai ka zo din , Allah ya kawo ka lafiya.
"Ameen ya amsa , sannan ya ajiye wayan cikin gida Hanan ta shiga da sauri , har tana tuntu6e, gaban Maryama ta zube tana haki duk yanda sukayi ta kwashe labarin ta bawa Maryama .
Mamah dai harda rawa da wak'a , wai daman tasan d'iyar ta mai k'ashin arziki ne , itama takusan fita a k'angin talauci kai ba ita ba har dangin ta zasu fita idan Malam ya ajiye girman kai ya dongwali arziki to idan kuma yak'i yaga bakin cikin dan baza ta zauna da shiba ehe..
Hanan kuwa acikin zuciyar ta cewa tayi , hmmm! "Kema dai kibi a hankali dan wlhy ba abun mamaki bane na sanja ki, wani irin murmushin mugunta Hanan tayi tare da farin cikin ta kusan barin gidan laka da zamah.
Sosai Hanan ta shirya cikin kwalliya me d'aukan hankali , tayi kyau sosai ita kanta dataje gaban madubi tasha mamakin ganin kyan suran jikin ta , Allah Saleem yaso nakasa jini wannan kyau din nata daya tafi a banza indai a gida zai kulleta , amma da ya cuce ta gaskiya matsiyacin banza.
Tsakar gida ta fito ta zauna isowan Yazid kawai take jira , Unaisa na zaune ta had'a uban tagumi ga yunwa ga azaban ciwo duban Hanan tayi sannan ta juyar da kyau cikin ranta tace Allah dai ya k'ara shiryamu dan naga kin d'ibo da zafi , shiysa akace idan kaga wata nakasa a jikin ka to karka d'aga hankalin ka k'ila shine mafi alkairi a gareka kuma sonka yake shiysa hakan ya faru dakai .
Hanan ce ta watsa mata harara! "lafiya kika samin ido haka kaman zaki cinye ni?"
"Kiyi hak'uri bake nake duba bah.
Tsaki kawai Hanan taja .
Tad'au lokaci agun sannan wayan hanun ta ya hau k'ara tana d'agawa yace gashi a layin data mar kwatancen yana jiran ta .
Jiki na 6ari Hanan tabar gidan , Yazid daga d'an nesa da layin ya tsaya cikin wata dank'ararriyar mota , har gaban motan tazo amma bata gane shi bane kasancewan motan bak'in glass ne .
Yazid wani mugun yawu ya had'iye , duk yabi ya kid'ime wayan sa ya d'auka ya sake danna mata kira da sauri ta d'auka .
"Yazid bangnka ba , inata dubawa .
"Ai ni na ganki danko ina gaban ki.
Glass din motan ya shiga sauk'ewa , a hankali Hanan ta tako har gaban motan , shine ya bud'e mata ta shiga.
Bakin Hanan ya k'i rufuwa sai dariya takeyi kamar wani gonan auduga
Abun harya bawa Yazid mamaki , ya kuma k'ara raina mata wayo , yamata tanbaya sosai kuma duka ta bashi amsa harda abunda bai tanbayeta ba ta fad'amar, dan har zancen gidan da suke ciki saida tayi mar akan saurinta ne ya basu su zauna a ciki zuwa wani lokaci.
Yazid yaji dadin hakan danshi kudi ba matsalar sa bane, kuma zai taimaka musu Hanan taji dadin hakan sosai harta fara hango rayuwan ta nan gaba yanda zai canza nan ba jimawa.
Waya ya ciro a kwali ya bata tare da wasu sugerfree Cookie's, shoppings ne leda biyu damin kud'i na hundred thousand , ya mik'a mata bbu ko jan aji Hanan tasa hanu ta amshe.
Hanan zata fita Yazid ya rik'o hanunta , juyowa tayi tana dubansa marairaicewa yayi tare da langa6ar da kai pls kiss mie.
Hanan cikin rashin fahinta ta dubesa kai ya d'aga mata , bata wani damu ba ta ajiye ledan ta k'ara matsowa tamar kiss, a kumatu rugumota yayi alaman godia itama rungumesan tayi alaman jin dadi.Cikin ranta kuma sak'an zuci take yi yau itane namijin mekyau da kudi kaman wannan Wanda kake jinshi a cikin novels yau shine a gabanta kuma kwance a jikin sa, gaskiya ko yanzu ta mutu ta godewa Allah.....
*Not edited ignore the all mistake please*
*Vote*
*Comments*
*Shere*
*Love you all my Fans*
💕💕💕*Xahrah ceh*🏌🏼♀🏌🏼♀🏌🏼♀🏌🏼♀
*Show me love to Subscribe my channel*
*AL'UMMA TV*
YOU ARE READING
BUTULCI KO HAUKA
Non-FictionTirk'ashi Butulci ko hauka , littafi me cike da darusa...