21 too 25

16 1 0
                                    

*BUTULCI KO HAUKA*
         💕💕.      💕💕         💕💕.       💕💕

*Written By✍*

*Fateema A.y Umar*

  *(Xahrah Farooq)*

*Gmail*
*xahrahfarooq@gmail.com*

*Wattpad*
*XahrahFarooq*

*Twitter*
*Official Xahrah Farooq*

*Snapchat*
*Official Xahrah Farooq*

*Instagram*
*Official Xahrah Farooq*

*Facebook*
*Xahrahh Faroouq*

*YouTube channel*
*AL'UMMA TV*
بسم الله الرحمن الرحيم

https://www.facebook.com/Xahrah-Farooq-Novel-110638730479676/

https://www.facebook.com/groups/227620608315825/

*Not Edited*

*Page*
*21 too 25*

......"Keh Maryama , kina da hankali kuwa?", kinsan me kike fad'a , ni ne nake da k'anjamau d'in?".

"A'a kai dai wlhy Malam ka cika d'aukan zafi , bafa da kai nake ba.

"Toh dawa kike bayan dagani sai ke kuma ni kikacewa nabar ta6aki karna sa miki k'anjamau, ya k'arisa maganan yana had'e rai.

"Wlhy tsoron fad'ama nake yi Kar kace na had'aka da matar ka .

"Fad'a min , ina jinki me tayi.

"Daman wlhy naso fad'a ma tun kwanakin baya duk sanda ka fita akwai wanda yake zuwa gunta su shige d'aki saidai kaji shiru suna kwashe awanni a tare , sai kuma wani gurnani da nishi da zaka ji yana tashi daga d'akin .

Malam Barau ya fiddo ido waje , ga gumi da yake had'awa " keh Maryama ki ji tsoron Allah , dan nasan halin munafurci irin naki.

"Wlhy da gske nake yi , idan baka yarda ba gobe ka dawo da rana zakaga ikon Allah.

"Tom shikenan Allah ya kaimu, yayi maganan yana dafe kansa dake sara mar.

"Karfa ka d'aga hankalin ka , shiysa tun farko ban fad'a maba, dan banason ganin ka cikin damuwa.

"To ai wannan ba maganan da za ayi shiru bane , ko dan gaba kinji ko.

"Toh shikenan hakan bazai saike faruwa ba, shiysa nace ina tsoron karta ya6a mana K'anjamau , yanzu madai gobe sai muje gwaji ko?"

"Ai dole muje indai hakan ne da gake.

Washe gari Malam Barau nasa k'afa ya fita itama ficewa tayi zuwa gidan aminiyar ta , ta kwashe duk labarin yanda suka yi da Malam Barau ta fad'a mata , tafawa suka yi hrda shewa sannan tad'au waya takira wani number ba jimawa aka dau wayan cewa tayi tanason ganin sa ynzu bbu 6ata lokaci , sannan ta kashe waye ta ajiye

Ba'ad'au lokaci ba sai gashi yazo gidan , nan Hajia Batulu tamar bayanin abunda takeson ayi , cikin yanayi na buguwa yace wannan ai mai sauqi ne .

"Yauwa yaro gsky na gode , zaka ko samu kud'i dadai da aikin ka kayi k'ak'ari kar asamu matsala.

"Ai Hajia ba wani matsaln da za a samu , ba yau muka fara bah .

Maryama sallama tayiwa k'awata akan zata wuce kafin Baban Hannatu ya dawo saboda tamar al'k'arin ya dawo yaga abun mamaki yanda Sadiya take kawo mar kwarto har cikin gida, bata wuce ba saida ta kar6i number din Bala akan da yaji kira yazo kawai.

Bayan ta koma gida tayi kiran Unaisa wai zata je mata aika , waje me nisa ta aiki Unaisa kuma a k'afa bbu yanda ta iya dole ta kar6i aikan ta wuce , dan inda sabo ta sabo wannan ba sabon Abu bane aikanta nisan duniya da k'afa , saidai idan mahaifiyar ta nada kud'i ta bata tahau mota.

Bayan fitan Unaisa bbu jimawa ta lek'a d'akin Sadiya taga tana bacci , fitowa tayi da sauri takira Bala akan yazo ba wani 6ata lokaci sai gashi kuwa , nanfa ya shige d'akin Sadiya ya kwa6e riga ya zaina bakin gado , duk wannan abunda akeyi Sadiya bata sani ba tana bacci dan ita akwai ta da nauyin bacci.

Ba'a d'au lokaci ba Malam ya dawo gidan , da hanu Maryama tamar nuni alaman ya shiga hakan ko akayi ya shiga d'akin , Bala ne ya fara k'ok'arin sauk'a daga gadon jiki na 6ari , tare da jijjiga Sadiya .

"Madam ki tashi ga Oga ya dawoo, cewar Bala

Azabure Sadiya ta farka tana goge ido , da sauri ta mik'e ta zauna tana zare ido cikin rashin fahinta .

"Innalillahi wa'inna'ilaihir raji'um, me zan gani haka , lallai yau Allah ya toni asirin ki muna fukar banza kin cuceni Allah ya isa.

Cikin rashin fahinta Sadiya tace "Malam me nayi?".

"Uw bakima San me kikayi bah?", to zaki sani yanzu .

Waje ya fita d'auko i'ce , yayin da tinin Bala ya gudu, afusace ya dawo d'akin ya fara dukan ta ihu take tana bashi hak'uri amma a banza , Maryama ce ta shigo d'akin "na shiga uku me zan gani Baban Hannatu kabari kar kayi kisa , i'cen ta kar6a shiko sai haki yakeyi , dak'er yace kije na sakeki saki d'aya....

*Vote*

*Comments*

*Shere*

*Love you all my Fans*
💕💕💕

*Xahrah ceh*🏌🏼‍♀🏌🏼‍♀🏌🏼‍♀🏌🏼‍♀

*Show me love to Subscribe my channel*
*AL'UMMA TV*

BUTULCI KO HAUKAWhere stories live. Discover now