Chapter 4

1 0 0
                                    

12:00 daidai hajiya asiya tashiga madafi domin dafama iyalanta abincin rana, tuwan shinkafa miyar egusi tayi musu, miyar taji nama da kifi cikinta, sai banana smoothie datayi tasa a na'uran Sanyi wato fridge kafin azo cin abinci yayi sanyi, takammala hada komai tajera Kan saman dinning table dake babban falon gidan, domin nan iyalan ke haduwa suci abinci kowane lokaci, takoma kitchen tashare ko'ina tayi moping, ta wanke duk kwanukan data bata
wajen yin girkin nata, dakinta tanufa, toilet tashiga tayi wanka tadauro alwala sannan tafito, kasancewar lokacin sallan zuhr yayi domin karfe 1:30pm ne, shiryawa tayi ta tsala kwalliya mai kyau da kayatarwa, sai zuba kamshi takeyi ciki da waje, sallah tatada tasauke faralin gaida ubangijinmu, tayi Addu'o'inta sannan tadau charbi, tadau wayoyinta tanufi babban falo ta hakince a kujera 3-seater matsayinta na hamshakiya hajiyar gidan, uwar yaran, kuma sarauniya agun maigidan nata,  lazimi tafarayi cikin natsuwa......

2:45pm daidai, habu driver yafara horn a bakin gate din katafaren flat din, shalolo maigadine yabude musu gate din, danno hancin motar habu driver yayi suka shigo cikin harabar gidan, yaran suka bude kofar motar suka shige cikin flat din ta kofar babban falon gidan, habu driver ma yafito yashiga falon yagaida uwar dakinsa hajiya asiya, sannan yakoma dakinsa dake chan kusa da gate din fita.....

Yaran hajiyan suka gaisheta kowa yawuce dakinsu domin aje jaka da cire uniform asa kayan gida, suka gama shiryawa suka fito kowa ya hallara kan dinning table don kwasar girkin mamar tasu mai dadi, kowa yaja plate yazuba iya yanda zai iya cinyewa, sukayi bismillah suka fara ci, shiru kakeji a falon Sai karan cokula da sautin taunan abinci, hajiya asiya tacema haydar yabude frige yadauko musu banana smoothie mai sha yadiba, yaje yadauko cups ya ajiye, kowa yadau cup yazuba yanda zai iya sha, sukayi hamdala ga Ubangiji daya ciyar dasu daga ni'imarsa da arzukinsa, yaran sukayima hajiya sallama suka wuce dakinsu don hutawa kafin lokacin islamiyya yayi su shirya sutafi.....

Karfe 3:30pm yaran sun Kammala shirin islamiyyarsu tsaf, sukayima hajiya sallama, tarakosu sukafito harabar gidan suna jiran habu driver yafito, kusan mintuna 5 sannan yafito, yasake gaida hajiya cikin mutuntawa, yatada mota suka shiga yajasu, shalolo maigadi ya wangale gate suka fice daga gidan zuwa islamiyyar...


A bakin gate din Islamiyyar habu driver yatsaya wato *MADRASATUL ULUMI WAL IRSHAD* dake unguwar sakaba road off dandima roundabout, habu yasauke yaran suka shiga Islamiyyar, yajuya kan motar don komawa gida....sukuwa yaran shiga cikin islamiyyar tasu sukayi, kowa ajinsu yashiga don ajiye jakansa acikin teburin wajen zamansa.....

Karfe 4:00pm malamai da dalibai sun hallara a masallacin dake cikin harabar makarantar, aka gabatar da sallan la'asar, akayi addu'o'i sannan aka watse aka shiga aji domin fara daukan darasin ranar, karatun Al-Qur'ani ake fara biyawa duka ajujuwan, sannan akaranta sauran littafin, Karfe 6:10pm aka tashi islamiyyar, dalibai bata fita suna tafiya gida, yaran suka tadda habu driver  a bakin gate daidai inda yasaba tsayawa da mota idan yazo daukarsu, suka gaisheshi suka shiga mota suka dau hanyar gida....

Kafin dawowar................!!!

Taku Har Kullum
Maymunatu Abubakar
Mai Fadakar Da Mata
Marubuciyar Al'umma !

Inajin Dadin Comments Dinku Masoyana Makaranta Novel Dina, Ana Tare Koda Yaushe !!!

🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

ALMAJIRI 'DA KAMAR KOWAWhere stories live. Discover now