Chapter 8

1 0 0
                                    

Karfe 7:10pm ahmad drive alhaji hannafi yafara horn a bakin gate din gidan, shalolo maigadi yayi hanzarin bude gate suka shigo yakulle gate, driver ya parker mota a parking space, alhaji yafito suka gaisa da ma'aikatan dake harabar gidan a lokacin, sannan ya shige falon gidan da sallama, bayan ya zaunane suka gaisa da hajiya, ya kalli hajiyan yace "yau ina yaran suka shige kuma??" tace "kowa na part dinsu, tunda suka shiga sallan magriba basu dawo falon ba" alhaji yace "akwai abunda yafaru Kenan? don basa kin zaman falon nan Sai da wani dalili" hajiya tace "hmnn! kai dai bari alhaji, wallahi yarinyar nan ce luba, narasa meke damun tunaninta", nan ta labartamai abunda yafaru. alhaji ranshi idan yayi dubu, to yabaci da luban akan abunda ta aikata, yasha yimata fada akan kyarar haydar din amma taki dainawa, don haka yau tafi ko yaushe bashi haushi da batamai rai...............!

Tashi alhajin yayi yanufi bedroom, ya sauya kayan dake jikinshi zuwa marasa nauyi na zaman gida cikin iyali, dawowa falon yayi ya zauna kan 2 seater, sannan yacema hajiyan takiramai luban, hajiya tace "to" tatashi tanufi dakinsu luban, tayi sallama sannan tashiga, ta fadamata sakon abban nasu tajuya tafita.......................


Salamun Alaikum!!! lubabatu tayi sallama cikin falon, aka Amsa tashiga tanemi guri ta rakube tana zare idanu don jin sautin muryan abban nasu mai cike da fushi da bacin rai ya firgitata, don tasan karo da kwai da dutse ba sauran labari..............
Alhaji yasoma tambayarta abunda yafaru tsakaninta da haydar din, tafadamai, aikuwa dawa Allah yahadashi inba da luba ba, tashi yayi ya janyo wayar AV kusa da TV stand yafara zaneta da iya karfinshi, Kuka take tana ihun neman ceto, Domin alhajin Bai iya dukan yaroba idan ya zuciya ranshi yabaci, Sai da yayi mata duka son ranshi Tukunna ya kyaleta, wayar AV din ya jefar yana huci yabar falon yanufi bedroom dinsu, ciki ya tarar da hajiya zaune bakin gado, bawanda yacema wani Kala, yanemi waje a bakin gadon shima ya zauna yana maida numfashi , itama luban tashi tayi ta rarrafa tanufi dakinsu, tashiga ta fada kan gadonta ruf da ciki, tacigaba da rera kukanta ma'ishi, bilkisu kuwa ko kallo bata ishetaba, balle tacemata ci kanki, duk da dai ta tausayama yayar tata cikin ranta,...........


Lokacin sallan isha nayi, kowa yayi alwala ya gabatar da farali, bayan idarwa aja hallara a babban falo don cin abincin dare kamar yanda aka saba, yau dai zaman dinning table din babu wani armashi da walwala, kowa ranshi babu dadi, musamman alhajin da luba da haydar, don su abun yafi shafa, haka dai aka gama cin abincin aka tashi kowa ya koma part dinsu, yau babu zaman hira ko kadan, abun sai dai muce Allah ya kyauta nagaba, Ameeeen...............!


Wannan Kenan,,...........
kubiyo ni don jin mai zai faru daga nan, wasa farin girki, yanzu novel din zai Kara dadi da armashi, don yanzu wasan zai fara........ku dai kubiyoni Sannu a hankali don jin cigaban Labarin *ALMAJIRI'DA KAMAR KOWA*, Shin wai ya abun yakene ??? Zakuji yanda zata kaya a next update dina in Sha Allah, ayi hakuri da Wannan short chapter din


Don't 4get 2 Vote, Share & Comments @ Wattpad

Taku Har Kullum :
Maymunatu Abubakar
Mai Fadakar Da Mata
Marubuciyar Al'umma !

🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

ALMAJIRI 'DA KAMAR KOWAWhere stories live. Discover now