Chapter 10

1 0 0
                                    

Bismillahir Rahmanir Raheem !


Adaidai wannan gabar nake rokon masoyana makaranta novel dina da suyi hakuri na rashin jina Kwana 2, kunsan lamuran rayuwa balle idan akace mace magidanciya mai aure, kunsan hidindimun gida dana rayuwama, don Allah ayi hakuri da ni, indai kukajini shiru to tabbas akwai dalili da uzuri mai karfine, ina matukar godiya gareku, ina alfahari daku, Allah yabar zumunci Ameen Thumma Ameen 👏👏👏

Ina muku kyakkyawan albishir cewa yanzu novel din zaifi dadi, don yanzune akazo gundarin labarin, kuma daga wannan gabar ne makaranta zasu tsinci sakon fadakarwan da novel din yakeso ya tunatar kuma ya ilmantar da al'umma baki daya, anan JIGON LABARIN yake in Sha Allah, kuma inada tabbacin makarantana 'yan albarka zasu tsinci abubuwa dayawa na Karuwa, Allah ka yafemana kurakurenmu, abunda mukayi daidai kabamu lada akanshi 🤲🤲🤲



               🅿️AGE TEN



Yau takasance asabar ce, wato ranar hutun karshen mako, wanda yawancin ma'aikatan gwamnati ke samun damar hutawa cikin iyalansu, hakance takasance a gidan malam hannafi, inda suke zaune bisa carpet a babban falon gidan suna cin abincin safe cikin natsuwa, bayan sun kammalane yaran suka kwashe kwanukan suka gyara wajen, alhajin ne ya umurcesu da Kowa yadawo ya zauna don yanada magana da su, suka zazzauna don sauraren abunda mahaifin nasu zai fada musu...


Alhajinne yafara magana da cewa "bismillahir rahmanir raheem, yayi salatin Annabi, yabude taro da addu'a, sannan yacigaba da cewa "na yanke shawaran Zama daku don nabaku labarin tarihin rayuwata domin kusan abubuwanda naci Karo dasu da kalubalen dana fuskanta acikin rayuwata, watakila ku dau wasu muhimman darusan rayuwa, musamman ke luba dama dukanku baki daya, don haka nake son ku natsu kubani hankulanku nan, zan fara baku labarina yanzu"


*WANENE MALAM HANNAFI DA RAYUWARSA TA BAYA ???*

Innalillahi wa'inna Ilaihi raji'un ! yanzu malam bazaka hakura da tura yaron nan almajiranci ba ? naga ko cikin kauyen nan akwai makarantar allo da tsangayun almajirai, ga makarantar malam sadi kasashi anan mana...

Halima kifita idona narufe, shin kece zaki fadamin yanda zanyi da rayuwar yarona ? to bari kiji, zuwa almajiranci dolene na tura hannafi birnin zaria yabido ilimin addini, domin inaso yazama babban malami yadawo gida yadinga koyama mutanen kauyen nan ilimi, don haka tafiya babu fashi, yanzu haka mungama magana da shamsu drive kafin yagama lodi na kaimai hannafi suwuce birnin zaria, inda zai kaishi makarantar dazaiyi karatu.............

"Hannafi ? hannafi ?? wai wai bazaka fito narakaka tashar ba sai mun makara yagama lodi yatafi" ?, hannafi yafito rungume da bakar ledar kayan sawansa a kirjinsa yana mai shashekar kuka  yana shan majinar dake fitowa daga hancinsa, rabe-rabe yake ajikin garun dakin domin shima bayason tafiyar don dai bayanda ya iyane kawai, tunda bai iya ja da mahaifinnasa, malam idi ya finciko hannun hannafin yace "maza sa takalmanka mutafi" hannafi yasa takalmin, malam idi yasake cewa "idanma zaka daina wannan koke-koken gwara kadaina, domin tafiya birnin zaria almajiranci babu fashi"

Malam idi yasake cewa "halima mikomin ledar kayan abincinsa kada ya manta mutafi, lokaci yana kurewa" nan ta shiga daki ta dauko ta mikomai ya amsa yaja hannun hannafin suka fice daga gidan cikin sauri da hanzari, yayinda hannafi yana tafe yana waiwayen mahaifiyar tasa yana mai Jin zafin rabuwa da ita ..........

Halima kuwa zama tayi dirshan a kasa tana mai kukan takaicin rabata da tilon danta guda 1 tak, wanda shine farincikinta acikin gidan, domin hannafi yarone mai ladabi da biyayya, ga natsuwa, don haka shine mai temakamata da komai acikin gida da wasu aikace - aikacen nata......................

Da fitar malam idi da hannafi basu zame ko'inaba sai tashar motar garin, layin inda ake lodin zaria yanufa rike da hannun hannafin, yaje har inda shamsu drive yake lodi, suka gaisa ya damkamai hannfin, yabiya mai kudin zaman maleji, sannan yaba hannafi dubu 1 yace yarike idan yaje ko zai siya wani abu, ya amsa yasa kudin cikin aljihun wandonsa, malam idi yayima shamsu drive da hannafi sallama yajuya yatafi don komawa gida, hannafi kuwa cigaba yayi da shashekar kukansa, mota tacika aka dau hanya sai birnin zaria mai dumbin ilimi, (sai muce matafiya Allah ya saukesu lafiya, Ameen Thumma Ameen).....

Bayan isarsu zaria, shamsu drive yagama sauke fasinjoji a bus stop na roundabout din Kofar doka, nan yacema hannafi yazauna zasu tafi yakaishi makarantarsu, nan yaja mota basu zame ko'inaba sai CIKIN UNGUWAR KAYA, inda sukayima kofar gidan malam na dauri mai almajirai, nan yayi sallama da malan na daurin suka gaisa ya damkamasa hannafin yamai sallama yajuya yatafi abinsa, wannan kenan..............

Malam na dauri yaja hannun hannafin suka shiga cikin gidansa wajen iyalansa, ya shaida musu ga sabon yaro ankawo karatu daga sokoto, suka amsheshi aka bashi ruwa da abinci yaci yasha, uwargidan malam takira wasu yara almajirai dasuke ta wasansu a tsakar gidan, almajiran basasu wuce sa'an hannafinba, tace ga aboki tayi musu, sutafi Kofar gida suyi wasa, kuma su nunamasa dakinsu na kofar gida inda suke kwana, sukace to, nan yaran su 2 masu suna yusuf da lirwanu sukaja hannun hannafin sabon abokin nasu, suka fice daga gidan zuwa waje tare......................


RAYUWAR HANNAFI.......

Turkashi, wannan shine wasa farin girki, yanzu game din yafara, kada kubari abaku labarin next chapter don jin ya rayuwa a birnin zaria zata kasance da hannafi almajiri, kudai kubiyoni kuji yanda labarin zai kaya, kada kubari abaku labari........................

Don't 4get 2 Vote, Share & Commentnts

Taku Har Kullum :
Maymunatu Abubakar
Mai Fadakar Da Mata
Marubuciyar Al'umma !


🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 12, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ALMAJIRI 'DA KAMAR KOWAWhere stories live. Discover now