Mamar yaran ta dakama kowa tsawa tace "kowa yawuce falo, antashi wasan tunda harda cin zalin karami"...sum-sum Kowa yawuce ciki, lubabatu dai haushi da takaici sun karu, don haka huci kawai takeyi kamar wata macijiya, hajiya rike da hannun haydar suka shiga falon, haydar dai sai ajiyar zuciya yakeyi don gaskiya yaji bugu bana wasaba..............
Shirune ya wanzu a falon tsahon mintuna 10, sannan hajiya tabuda baki tafara magana "gaskiya lubabatu kin batamin rai, sam banji dadin abunda kikayiba, kece babba fa, wai sai yaushe kiyayya da tsanar aliyu zai shafe ya goge acikin zuciyarki?? bansan me yaron nan yatsare miki ba, tsakaninku sai kyara da hantara, saboda wani dalili? idan aka tambayeki bakida wata kwakwaran hujja balle dalili mai karfi....hhhmmnn!
Abunda zan sanar dake shine "da ke da haydar duk dayane a wajena, banason wannan tsanar dakike nunama yaron nan, gaskiya nagaji da halinki akan haidar, idan nasake Ganin kinshiga harkanshi sai nayi mummunan saba miki"....
"Kowa yatafi yayi alwala ayi sallan la'asar" yaran sukace to suka tashi don ficewa, inbanda lubabatun datayi fam don haushi, wucewa sashinsu sukayi don yin Abunda akasasu..........Hajiya asiyanma dakinta ta wuce, zama tayi bakin gadonta, tagumi tayi Tana Dan tunani da nazari, wai luba wace Irin zuciya da tunani gareta? yarinya Don Ubangiji yarufama iyayenki asiri da arzukinsa, sai ki tsani duk wani talaka ko nakasa dake idan ya rabeku? "Oh! Allah ka shiryamin zuciyar yarinyar nan, kakaramata Hankali da tunani" AMEEN !
sannan tashiga toilet don dauro alwala tayi nata sallan, data idar tadade tana yima yaran addu'an shiriya dana Karin albarkan rayuwa, dama addu'an nemanma Yaran tsari da kariyan Ubangiji.....Bayan lubabatun da bilkisu sun shiga dakinsune, bilkisun take cewa "a gaskiya yaya luba baki kyautawa sam wlh, abunda kikeyima haydar baidace ba, nima banajin dadin hakan, kidinga sassautamai" lubabatu tace "to, uwata yimin fada, sau Nawa nasha fadamiki, kidena shiga harkata irin wannan, ki tsaya iya abunda yashafeki dani".
fuuuuu tashiga toilet ta banko kofar dakarfi jikake garrrammmm! kamar glass din jikin kofar ya tsarwatse...bilkisu Dai Cewa "Allah ya ktauta".......Bayan an Idar da sallan din, 'yan mazanne suke tafe bisa hanyar dawowa gida daga Masallaci, aminu yake ba hyadar hadi dayimai nasiha dacewa " abunda nakeso dakai haydar, kakarayin hakuri da halin yaya luba, komai zai wuce, watarana sai labari in Sha Allah, inaji ajikina, Allah zai rayaka ya daukakaka aduniya fiyeda ita da duk abunda take tunani, kaidai kakara hakuri da Juriya, kaga mu muna tare dakai, Sannan hajiya da alhaji suna sonka sosai, haydar yace "babu komai yaya aminu, in Sha Allah zan cigaba da hakuri, kuma inama yaya luba addu'a Allah yabata hakuri a zuciyarta" sukace "Ameen Thumma Ameen" gabadaya..........
Karfe 7:10pm................,........!!!
Don't 4get 2 Vote, Share & Comments
Taku Har Kullum
Maymunatu Abubakar
Mai Fadakar Da Mata
Marubuciyar Al'umma !Ina Godiya Da Fatan Alkairinku Gareni Masoyana Makaranta Novel Dina, Allah Yabada Ladan Zumunci AMEEN THUMMA AMEEN NAGODE SOSAI !!! 👏👏👏
🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
YOU ARE READING
ALMAJIRI 'DA KAMAR KOWA
General FictionIs A story full of pity and sympathy of an ALMAJIRI boy, how he struggle with life in tsangaya, then he later have opportunity and he went to school up to university level, where he was able to study Mass Communication and finally got married and ha...