💧💧 *RAMUWAR GAYYA.!*
©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*
Home of expert & perfect writers*FEEDOHM.💞*
Wattpad@Feedohm.*06*
**Kamar yadda Jafar ya alƙawaranta, haka wanshekare da hantsi sai ga iyayen shi a gidan mu, cikin shiga ta kamala da mutunci, ko wannen su sanye da babbar riga, kallo ɗaya zaka masu ka tabbatar da mutuncin su, Baffa na da kanshi ya yaba da dattakon su, bare da suka ce Jafar ɗan gidan ladan Sani ne, kuma su yayyen sa ne, shine ya turo su da kanshi, nan take yayi na'am da batun su, sannan ya ƙara da cewa "Na ji dadi sosai da naga ɗan gidan mutunci ne ke neman auren ƴata, amma duk da haka zamu binciki halin yaron ku, domin ba halin uba bane ke fassara ɗan sa, halin uba kawai gida yake fassarawa.!
Ya sanya aka kawo masu abun sha da ci, suka sha suka tumbatsa, sannan suka yi sallama bayan sun bashi naira dubu ashirin kuɗin neman aure, a take ya fitar da dubu sha ɗaya ya maida masu, ya ce ba dukiya suke buƙata ba, albarkar suke nema, ya ƙara da cewa idan ba matsala yana buƙatar ganin yaron da marece, suka yi sallama cike da mutun ta juna suka tafi.
Da marece Jafar ya zo shima cikin shigar sa ta kamala, yayin da ya tattare natsuwar shi guri guda, baffa ya sanya aka shinfiɗa masu tabarma a zaure na biyu, yayin da aka kawo mashi lemu da ruwan sha na roba bisa tire aka dire.
Baffa ya ɗaga kai yana nazari Jafar, yadda ya sadda kai ƙasa cikin natsuwa da alkunya, a take ya yaba da tarbiyyar sa, don tunda ya zauna ko ƙwaƙwaran motsi ya kasa yi, ya gayar da Baffan ciki ladabi yana kallon ƙasa,yayin da ya bashi hannu su gaisa amma Jafar ya noƙe hannu sai dai ya ƙara rusunawa.
Cikin zolaya Baffa ya ce "Ka ɗago idon ka mu kallo juna tunda ban kai ga baka ƴar ba tukun, kuma banda abun ka ai Auta ce zan baka ba yar fari ba, kaga kuwa kai ɗa na ne ba siriki ba."
Jafar yayi murmushin jin kunya, yana ƙara ƙasa da kanshi.
Baffan ya kuma murmusawa ya ce "Da alama ka fi autar tawa kunya, tubarkallah masha Allah, dole bakin Auta yaƙi rufa wa, ashe ba ƙaramin kamu tayi ba mu, sai dai na san Aminatu ƙyawun hali ta bi ba ƙyawun fuska ba, domin mu shi muke buƙata.
Shi dai Jafar kan sa na ƙasa har Baffa ya kuma tambayar sa "Sunan ka Jafar ne ko.?
Ya ɗan rusuna yana faɗin "Hakane alaramma."
"Masha Allah, Jafar menene sana'ar ka.? Baffa ya tambaya
Ya gyara zama da niyyar sharo mashi ƙarya kamar yadda Faisal ya sanar dashi, a natse ya ce "Babana yana...!
Baffa ya katse shi "Kai kan ka nake tambaya ba baban ka ba..!
Ya sadda kai ƙasa yana faɗin "Kasuwanci."
"Wane kala.?
"Muna shigo da kayan masarufi, sannan ina lecturing a..!
"Dakata yaro, wannan ma ya isa, fatana ka san yadda zaka mayar da biyar ta koma goma, ya batun ɓangaren addini fa.?
"Nayi sauka tun ina shekara goma, sannan na karanta littafai da dama, kuma har yanzu ina neman ilmi.! Ya faɗa cikin dake wa, kuma wallahi ƙarya yake, ko hizub ɗaya bai haɗa ba, maganar littafi kuma, arba'una hadith ya taɓa karantawa shima, daga hadisi na biyu bai ƙara sanin komai ba, kuma shima fassarar ya sani bai iya baƙin ba.
Baffa ya ce "Masha Allah.!
Duk wata tambaya da Baffan ya mashi ya amsa ta dai dai gwargwado cikin kuma natsuwa da kamala, ta yadda a take Baffan ya aminta da shi, sun jima suna tattauna wa sannan Baffa ya ce "Na yarje maka ka nemi ƴata, amma bisa sharaɗi, idan har na bincika na ji ƙarya a zancen da muka yi yau, to wallahil Azim ba zan aura maka Aminatu ba, duk yadda ta kai ga sonka, don ba'a taɓa aure da ƙarya a ciki.!