💧💧 *RAMUWAR GAYYA.!*
©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*
Home of expert & perfect writers*FEEDOHM.💞*
Wattpad@Feedohm.*07*
***Ran sa a matuƙar ɓace ya ƙarasa shagon Faisal, ya tsallaka cikin shagon kai tsaye, tare da ƙwanta bisa ƴar tabarmar da ke a yashe ƙasa, yayin da ya rumtse idon shi gam yana fitar da wata irin iska mai zafi daga bakin sa, a nashi tunanin tunda har ya tura manyan a gidan mu, to ya gama me wuyar, zai samu abunda ya ke buƙata cikin sauƙi da ƙwanciyar hankali, sai dai kaf na gama ƙwance mashi zani a kasuwa..
"Abokina wai ya ne? Tun ɗazu kake huci sai kace tsohon zaki.? Faisal ya tambaya bayan ya gama sallamar mutanen dake siyayya a gurin.
Jafar ya ɗago ya kalle shi da rinannun idanun shi, tare da jan dogon tsaki yana faɗin "Wannan jakar yarinyar ce wallahi, na ɗauka na gama da wannan matsalar, ashe aƙwai sauran aiki a gabana. "
"Me ya faru.?
"Mtss bar ƴar wahalar, daga riƙe mata hannu shine zata faɗa man wai zata gaya ma Ummi? To ko Uwar ta ta kama bana ci shegiya ba? Mtss aikin banza da wofi, wallahi na ƙosa in yi a wuce gurin, don ko ganin ta bana son yi wallahi, haka nan fa nake daurewa, gashi sai asarar kuɗin card nake, da yake matsiyaci ya ce babu abunda ta iya sai flashing..!"Ya ƙarashe maganar zuciyar sa na tuƙuƙi.
Me Faisal zai yi in ba dariya ba, ya kuwa ƙyalƙyale da dariya yana faɗin "Shine ranka ya ɓaci har haka? Haba JB, kamar ba namiji ba.?
A fusace ya ce "Ba dole raina ya ɓaci ba? Kana fa ganin bai fi saura wata biyu ba in koma gida, ni dai gaskiya ba zan iya ba wallahi, na gaji Faisal, kawai ina ga fyaɗe zan ma shegiya.!"
"Ta yaya? Yarinyar da ka ce idan ba gidan yayar ta ba ko ƙofar gida bata fita? Ina zaka ganta? Ko a zauren gidan su zaka murƙushe ta.?
" Mtss! Kuma haka ne."
"Ni dai shawarar da zan baka, kayi hakuri muddun kana son biyan buƙatar ka, idan ba haka ba duk abunda kayi ya tashi a banza, ka shiga jikin ta sosai, ka aika masu da sadaki, na san babanta uztaz ne, ba zai karɓa da yawa ba, kaga wannan sadakin zai sanya ta ƙara aminta haɗi da sakin jiki da kai, idan aka yi wannan, ni na san dibarar da zanyi ta fito, sannan har zuwa lokacin da zaka aika sadakin kar ka kuskura ka ƙara nuna zalamar ka fili, ka bata hakuri ka nuna kayi kuskure."
Yayi shiru yana nazarin maganganun sa, kafin ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Amma dai kasan banda kuɗin da zan aika ko.?
"Sai in ranta maka kafin a turo maka na registration, na tabbatar ubanta ba zai ƙarɓi sama da dubu ashirin ba, don naji ance da auren yayar ta dubu sha uku ya amsa..!
Jafar ya faɗaɗa fara'ar sa yana faɗin"Da gaske abokina.?
" Da gaske mana, ai duk moriyar mu ce, ko ka manta nima zaka sammani.? Faisal ya faɗa yana lashe manyan laɓɓan sa, tare da riƙe hantsar wandon sa.
Suka ƙwashe da dariya haɗe da tafawa..
Jafar kam a ran sa yake faɗin "Kaima zaka ci uban ka wallahi, ka ranta mani kuɗin, muddun na samu abunda nake so ba zaka ƙara gani na ba, bare har na biyaka, baƙauyen shashasha."
****
Ni kam kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki haka na ja ƙafata na koma cikin gida, har ga Allah banyi tunanin bin bayan shi ba, bare na bashi hakuri ba, domin na san yadda Jafar ke ƙauna ta, to nan da zuwa anjima kaɗan zai huce ya kira ni don ba zai iya fushi da ni mai tsawo ba, na gifta Ummi tsakar gida tana alwala, ko inda take ban kalla ba, sai dai ita ce da ta bini kallon mamaki sauyin yanayi na, don ba haka ba fita ba, har na shige ɗaki abina, sai da ta gama abinda take a waje, sannan ta shigo ta same ni ƙwance bisa katifa, nayi rufta ciki ina kuka ƙasa ƙasa, ta zaune bakin katifar haɗe da dafa bayana, cikin sigar lallashi ta ce "Waya taɓa mani Auta.?