11

184 7 0
                                    

💧💧 *RAMUWAR GAYYA.!*

©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*
Home of expert & perfect writers

*FEEDOHM. 💞*
Wattpad@Feedohm.

   _ASSALAMU ALAIKUM, ƘWANA BIYU SHIRU KO? AYI HAƘURI JIKI DA JINI..!_

*011*

     ***A ɓangaren Jafar kam farin ciki fal a ransa ya ƙarasa shagon Faisal, wanda dama ba shi da gurin zuwa da ya wuce can, tun da aka ƙore shi makaranta, yayin da ya kira mai lemu ya siya ya haɗa har da pancake, saboda yadda yunwa ta fara nuƙurƙusar sa, sannan ya tsallaka cikin shagon ya miƙe ƙafafu bisa tabarmar yana faɗin "Mutumina, yau fa na buge boss.!

Faisal ya zaro ido waje yana faɗin "Haba? Kai dallah! Yaushe zamu shana.?

Ya ƙyalƙyale da dariya "Ina faɗa maka na mata kaca kaca kana tambayar yaushe? Kai wallahi ɗan bunsurun nan ya iya haihuwa, ina faɗa mata yarinyar ta haɗu ƙololuwa,wallah fil take a leda lumtsum kamar kankana..!"

Faisal ya ce "Amma kai shege ne, alaramman ne bunsuru.?

Ya kuma kecewa da dariya "Yo uban wa ke aje gemu irin shi, ai ina faɗa maka ban ƙara tabbatar da wannan tsohon sakarai ba ne sai yau da ƴar sa ta shigo hannu na, na gama raina sa, yadda ake faɗin gidan tarbiyya ne, gidan mutunci ai na ɗauka ya liƙawa ƴar ta sa CCTV camera a ɗuwawu.!

"Kar dai ka ce ka ci banza.? Faisal ya tambaya yana lashe baki kamar tsohon maye.

"Wallahi kuwa, don ma ba wani morewa nayi ba, ƴar wahalar ta isheni da ihu da tsinuwa, bayan armurar itama kayan daɗi ta ke ƙwasa, amma next time ina gaya maka wallahi sai na fanshe, sai na sa ta dinga kawo kanta ɗakina tana roƙan na ƙara..! Ya faɗa yana cin fanken sa.

Faisal ya dalla mashi harara "Amma ya mu kai da kai dan uban ka? Ni zaka yaudara.?

"Haba kai ko, ai shi yasa ma ka ji na ce next time, don ban kore ta ba, asali lallaɓata na yi, wallah so nake na mata ci irin uku huɗu kafin in koma, kaga na fanshe sadaki na har da ƙari.!

"Ta ya ya? Bayan ka rushe komai.?

"Ni fa ne, tunda har ta san na ɓula ta kaga dole ta laɓɓani ni mu samu muyi aure, ni kuma da wannan damar zan bi in yi yadda nake so..!

" Kai Anya? Kamar ba zata aminta ba.!

"Ita ɗin banza, yarinya ce ƙarama, kuma tana masifar sona.!

Faisal ya zabura ya dafe ƙugu yana faɗin "Wayyo! Ka ce aƙwai group discussion."

"Ƙwarai ma kuwa, bara in take ciki na, sai ka aro mani takalmi da hula in je ban gajiya haɗe da ban hakuri.!

"Zaɓi ka darje na waje na, ni wallahi so nayi ka mani video, ko ba komai ya rage mani zafi, kuma kai ma da ka dinga amfani da dashi gurin janyo ta ta ƙarfin tsiya.!

" Kash! Wallahi banyi wannan tunanin ba..!

****

Ni kam ina zaune kamar mutun mutumi ina zubda ƙwallah, ta ware mani ƙafafu ta haske al'aura ta da ta kumbura tayi sumtun ta ƙurawa ido, a take hawayen ta suka zubo saman ƙafa ta, yayin da ta ɗago muka haɗa ido, kamar yadda nake hawaye haka yaya Salima ke fitar dasu ita, tare da aika mani da wani razanannen kallo, babu zato ba tsammani sai jin saukar mari nayi bisa kumci na, ina ƙoƙarin dafe gurin ta kuma aza mani wani a ɗayan ɓangaren, yayin da ta cigaba da jera mani su babu ƙaƙƙautawa, ban san iya adadin marin da mani ba, sai da ta gaji don kan ta sannan ta sulale ƙasa tayi zaman dirshan ta saki kuka tana faɗin "Kin ci amanar iyayen ki Amina, kin ɓata wayau ki a banza? Me kika nema kika rasa da har zaki je ki bawa wani namiji kan ki.?

RAMUWAR GAYYA Where stories live. Discover now