09

51 4 0
                                    

💧💧 *RAMUWAR GAYYA.!*

©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*
Home of expert & perfect writers

*FEEDOHM. 💞*
Wattpad@Feedohm.

*09*

         ***Sai na ke jin fushin nasa babu ɗadi ko kaɗan a raina, yayin da na ɗauki alhakin accident ɗin na ɗaura wa kaina, saboda ta dalili na na ta zo ƙasar har hakan ta faru, kamar idan na ce ba zan je ganin ba banyi ma kai na adalci ba! Sai dai ya zanyi? Sam ba ɗabi'ar gidan mu bace zuwa gidan ƴan uwan saurayi bare gidan su saurayi kanshi, komai munin abunda ya faru, idan har ban manta ba, sauran sati biyu ayi bikin yaya Salim, surukar ta rasu (Uwar mijin ta) amma ba'a bar ta taje gaisuwa ba, sai da Ummi da Baffa kawai suka je, a madadin ta, na sanya gefen hijab na goge hawayen da ke silalowa, yayin da kaina ya toshe, na gagara hango aibun da ke tattare da faɗa wa su Ummi? Me yasa dole sai ni zan je? Ban sani ba, don haka na ja ƙafa ta na koma cikin gida, yayin da zuciya ta ta haɗu ta jagule.

  Abun mamaki sai da muka share ƙwana shidda ba tare da Jafar ya kirani ba, tun ina ma shi flashing tare da yaƙinin zai kira, yayin da nake bashi uzurin rashin lafiyar mahaifiyarshi ta sha gaban shi, har na fara jera mashi gangariyar kira tare da saƙonnin ban hakura, amma ko sau ɗaya bai waiwaye ni ba, na shiga damuwa matuƙa, da tashin hankali, kullun ka kalli fuskata ba zaka rasa busassun hawaye ba, yayin da na rame nayi baƙi yadda kasan wadda tayi ciwon wata ɗaya , abinci ma ba kasafai na cika cin sa ba, ko na fara sai dai na tattara ma mayar kitchen ba rufe, na koma ɗaki na cigaba da rusa kuka, wanda Ummi ta yi laƙani da sabuwar ibada, kuma ko sau ɗaya Ummi bata taɓa tambayar musabbabin damuwar tawa ba, asali idan ta ga ina kuka sai da ta kawar da kai kamar bata san da Allah ya aje ni ba, domin tun baya ta riga ta ɗauki alwashin tunda har na fara mata ƴan ɓoye ɓoye ita kam ba zata taɓa buɗe baki ta tambaye ni ba damuwa ta ba, idan gumi ta gumi kai da kaina zan buɗe baki na faɗa mata, Sai dai bata sani ba, na ri ga na ma Jafar alƙawarin zan killace sirrin mu, duk runtsi duk wuya ba zan taɓa faɗa wa wani tsakanin mu ba.

A ƙwana na baƙwai ne na shirya da marece na ce ma Ummi zan je gidan yaya.

"A dawo lafiya.! Ta faɗa ba tare da ta kalli inda nake ba.

Wani takaici ya rufe ni, tana fa ganin yadda nake kuka amma ko a jikin ta, na fashe da kuka ina kallon ta, tayi watsi da ni ta cigaba da abunda take, ina tsaye har ta ƙare sannan ta miƙe, ganin tana niyyar barin wajen ya sanya na riƙo rigar ta ina faɗin "Ai ace ma mutun yi hakuri daɗi gare shi.!

Ta ja tsaki haɗe da murmushi tana girgiza kai, babu yabo ba fallasa ta ce "Akan me za'a baki haƙuri Aminatu?

  Cikin kuka na ce "Ai dai kina ganin kullun ina kuka.!

Ta ce "Waya saki kukan?

Kai tsaye na ce "Jafar.!

   Ta taɓe baki tana faɗin "Sai ki bari ya baki haƙurin da kan shi, don ni bazan kama baki haƙuri ba ba tare da sanin dalili ba, kuma ko na tambaye ki dalilin ba faɗa mani zaki yi ba, kin ga kam babu buƙatar bayar da hakurin daga gare ni.!

Na turo baki, gaskiya ta faɗa, ba zan faɗi mata matsalar ba, nima yanzu ina da sirrikan da nake son na killace kamar yadda ya faɗa mani, a hankali na ce "Hakuri ko daga wanene ai daɗi gare sa.!

Ta murmusa "To Allah ya baki hakuri Auta.!

Na zunɓuri baki hawaye na zuba daga idona, na nufi gidan Yaya, itama ko gaishe ta banyi ba, na suri wayar ta na faɗa toilet har da gudu na, a take na sanya lambar Jafar na kira shi, kuma cikin sa'a ya ɗauki kiran, don ban taɓa kiran sa da layin ta ba.

Murya ta na rawa na yi mashi sallama.

Ya ce "Amin waalaikassalam da wa nake magana.?

Hawaye suka gangaro saman kumatu na, kar dai ace har ya manta murya ta, cikin rauni na ce "Aminatu ce. !

RAMUWAR GAYYA Where stories live. Discover now