💧💧 *RAMUWAR GAYYA.!*
©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*
Home of expert & perfect writers*FEEDOHM. 💞*
Wattpad@Feedohm.*08*
***Na sake gyara ƙwanciya tare da cusa kaina ƙasan pillow ina murmushi, yayin da ƙaunar sa ke ratsa kowanne lungu da saƙo na jikina, mun jima muna ɗumama juna da kalaman soyayya, masu rikitar da zuciyar masoya, sannan ya roƙe ni alfarma in kai ma Ummi wayar su gaisa, don basu taɓa magana ba, na miƙe tsam na fita tsakar gida, cikin sa'a na iske ta, ita kaɗai tana cin tuwo, na kanga mata wayar a kunne.
Ta ɗago ta kalle ni tana tambayar "Wanene.?
Shirun da nayi ina murmushi tare da wulla hannuwa na baya, ya bayyana mata kowanene, don haka ta sakar mani harara, lokacin da yake gaida ita, ta amsa kamar wanda ta riga ta saba da shi , har da su tambayar shi ya maman shi, duk da ba wani daɗewa suka yi suna magana ba, amma yadda kasan waɗanda suka shekara da sanin juna haka suke magana, ni kam ina gefe sai murmushi nake, sannan ta miƙo mani wayar bayan sun yi sallama, na koma ɗaki na shige cikin bargo.
Tun daga ranar muka koma fiye da baya, domin yanzu ya fi nuna mani kulawa da ƙauna, sannan ya ɗauke idon sa kacokam a kai na, ko yawan kallon surata ma ya daina, iyaka ta da shi muyi fira yana kallo fuska ta, ga wani wa'azin da ya koma yi mani duk lokacin da zai zo gurina, sannan ya mani alƙwarin da mu yi aure shine malamina, babu wata islamiyyar da zanje..
Baffa da kan shi ya taka har unguwar da aka ce suke, cikin dubara da hikima yayi bincike akan Jafar ɗan gidan ladan sani, kuma ya samu shaidar kirki daga mutanen unguwar, don wancan Jafar ɗin mutumin kirki ne, ya dawo gida sai yabon sa yake, kuma a ɗan datsin Jafar ya takura akan lallai sai ya aiko da sadakina a gidan mu, idan ya so sai a sanya rana bayan an kawo, Baffa ya aminta, tare da yanka masu naira dubu sha biyar a matsayin sadaki, sannan ya sanya wata huɗu ayi biki, shima dan ya cije ba zai rage ba, don kuwa a yadda Jafar ya buƙata wai a sanya wata ɗaya , zai mani komai da komai na hidima, kayan ɗaki , da kayan kitchen da duk ma wani abun amfani.
Baffa ya sanar da shi, ai ba shine ke da alhakin wannan hidimar ba, zai yi komai a matsayin sa na mahaifina, idan lokacin ya masa tsawo sai dai ya haƙura ya nemi wata, don abun bana sauri bane, kuma ma yana buƙatar ƙara bincike sosai, sannan hatta lefe Baffa ya ce bama buƙata, ya bari duk abunda yayi niyyar bani idan an kaini gidan sa ya ɗauka ya ba ni.Haka ya haƙura aka sanya wata huɗun, sai dai tun daga ranar ya fara janye jiki daga gare ni, ya dai na zuwa fira guri na, ya kuma dai na kirana a waya sosai..
Idan na tambaye shi dalili sai ya ce "Idan ina tare dake Aminatu, na kan ji tamkar ina tare da matata, ina jin shauƙi mara iyaka, kuma ni bana so wani abu ya sake faruwa, shiyasa nake nesa nesa dake, amma babu abunda ya rage daga ƙaunar ki."
Har a raina nake karɓar uzurin sa, tare da ƙara ƙaunar sa har cikin zuciya ta.
Yau kam banyi zato ba, sai ga yaro an aiko wai ana kiran Amina.
Na kalli Ummi dake yanke farce tsakar gida lokacin da ta ke tambayar "Wa ke kiran ta.?
Yaron ya ce "Jafar aka ce."
Na zabura na miƙe zumbur na nufi ɗaki, na zuro hijab dogo har ƙasa na fito har ina tuntube.
Ummi ta dalla mani harara tana faɗin "Aji kam anan ya samu targaɗe.!
"Kai Ummi.!" Na faɗa ina ƙoƙarin zagaye tabarmar da ke zaune, in fice.
Ta dalla mani harara "A haka zaki fita?
Na zunɓuri baki ina faɗin "Me nayi.?
Ta zubawa kafafuna ido, na ƙara zumɓurar baki ganin kafafun nawa duk jirwayen omo, a cikin maƙoshi na ce "Ai ba jikina ya ke so ba, kuma ya ce baya so ina ƙwallah idan zan fita wurin sa, kuma ya ce a haka ma na fi ƙyau."