✨ Yarima Fadil✨✨✨

51 4 0
                                    

   Chapter 2

Hmmm kayi kagama abban husnah tacigaba d rawarta..."Allah y shiryaki" cewar Alh.mahdii..

     Alh mahdi..shahararren Dan kasuwa ne yana da shaguna anan kwari cikin garin kano,yana siyar da atamfofi,shaddoji dadai sauransu Kuma yanada ilimi Dan yahada degree dinshi nafarko a jami'ar BUK inda yakaranta business administration Yanxu shekarunshi 35 a duniya..Allah yayiwa iyayenshi rasuwa t hanyar hadarin mota inda Babu Wanda yafita dg ciknsu....Mahaifinshi Alh.ismail yanada Mata 1 da 'ya'ya 3 nafarko shine Adam,yanada Mata 2 da yaya 6,na biyu Kuma Mahdi yanada Mata daya da Diya daya husnah sai Yar autarsu fateemah wacce akecema teemorh ita hr ynxu batayi aure ba..takammala degree dinta nafarko inda ta karanchi Chemistry.tunda Allah yayi ma iyayensu rasuwa sai Mahdi y dauketa takoma gdnshi da xama...wannan shine taqaitaccen labarin familyn Alh.Mahdiiiii

          ***************************
Masarautar katsina masauratace da aka kafata tun xamanin kaka da kakanni.. masauratace da ake tsantsan adalci acikin ta saidae Kuma Daman Shi Dan Adam 9 yke becika 10 ba dole asamu bare gurbi ko ince Wanda Hali ya banbanta..Sarakuna sunyi sarauta da dama Wanda har ynxu Allah ya kawomu zamanin sarki Abdul'aziz Abdussalam Abdul'aziz
Sarki Kenan me adalci me qaunar talakkawanshi.
      Sarki Abdul'aziz yanada Mata 4 ta farko itace mama Fulani tanada Yaya 8 Allah d nashi ikon dukkansu Mata ne kuma ta biyu mama talatu tanada Yaya 5,suma duk Mata ne ta ukku Ummah fadila tanada Yaya 3, Abdussalam (fadil),Umar,Usman.sai Anty Amarya tanada 'ya daya tilo wato gimbiya zakiyyah
      Sarki yashiga damuwa sosai Alokacin da aka Haifa mishi Yaya har 13 duk Yaya Mata Amma dayake yanada tawakkali kuma y yadda d Allah saikawai yayi hqrii alokacinne ya auro Ummah fadila kyakykyawar bafullatana ce tana tallar fura d nono Alokacin sai sarki yanuna yanada interest akanta yasha wahala sosai Alokacin kafi abashshi y aureta inda Allah danashi ikon akayi aure wata Tara cifff bafullatana ta haifamishi sambadeden saurayi fadin murnar da sarki yashiga a wannan lokacin Bata bakine
     Ranar suna yaro yci suna Abdussalam wato sunan mahaifin me martaba Kenan inda akeyimishi inkiya da fadil... YARIMA FADIL kenan
  YARIMA FADIL kyakykywn bafullani Kenan Wanda ayansu shekarunshi 32 yayi karatunshu dg primary hr tertiary a UK inda yakaranci MBBS a Yanxu hk yaxama cikakken likita inda memartaba ya Gina mishi katuwar asi biti anan cikin garin katsina...yarima har ynxu beyi aureba danshi Mata ma basa gabanshi saidai sarki yanaso yaga yaronnashi tilo yayi aure saboda halin yau da gobeee....
  GIMBIYA ZAKIYYAH diyaga Aunty amarya Kenan me ji da izza shekarunta 21 aduniya itace autar memartaba tanada izza da nuna Isa inda tagado mahaifiyarta sbda mahaifiyartata diyace ga sarkin bauchi..Gimbiya zakiyyah takasance mahaifinta bayasan wannan mummunan halinnata amman dayake gado tayi saima abinda yayi gaba tana karatu ne a jami'ar Ummaru Musa yar'adua University Katsina tana 200levl ne a ynxu haka. ...
   Wannan shine taqaitaccen labarin masarautar katsina

    ******************************
  Fitar malam keda wuya yatadda wani kyakykyawan saurayi a tsaye a qofar soron gidan yana jiran Ashnahh  wannan saurayin me suna Ahlan ya durqusa har qasa ya gaishe da mahaifin Ashnah Amma sai ya gallamishi harara yacemishi kaii me nacemaka bance karka qara xuwa gdannan gurin yata ba?? Shidai Ahlam ya duqar dakai yanata bama malan haquri Amma malam bayama jinshi yanata bala'i ta inda yake fita batanan yake shigaba shidai Ahlam haquri kawai yake bashi ya qara gaba.......

    ******************************

  Asalin tarihin Malam namuda wato mahaifin Ashnahh.................

✨ Yarima Fadil✨✨Where stories live. Discover now