Chapter 3✨
Sorry for the typn error no Editing
✨✨✨✨✨✨
Malan Tanimu me gwanjo shine
asalin sunan mahaifin mamuda..malan Tanimu yana sana'ar gwanjo inda yke kaiwa gari gari Kuma ba laifi yana samu daidai gwargwado
Yanada Mata 1 da 'ya'ya 4, lamido,jafaru,hajara,mamuda....
Malan tanimu sudin Yan Asalin jahar katsina nee wani qauye da akecema K'afur...Allah yayiwa malan Tanimu me gwanjo Alokacin da mamuda ykeda shekaru 10 aduniya daga matanshi har yaranshi sunji mutuwarshi amman haka suka dangana..Mamuda yataso tun Yana yaro bayajin magana ga shegen son kudin tsiya Kuma sudin ba wasuba Yana biyema abokan banxa anan cikin qauyen..to Allah da nashi ikon da Adduar Uwa da yayyenshiiii sai yadan fara natsuwa sudin bawani arziqi garesuba Dan har qara ma lamido yayi gadan Mahaifinshi yakan saro gwanjo yasaida...
Lamido yanada Mata 1 hanne da yaya 4. Suna zamansu cikin rufin asirin Allah.Jafaru ma yanada Mata 1 da yaya 2 Shima dai Yana Yan kabu kabunshi yasamu kudi dayake a wannan xamanin baa damu da ilimin Boko ba shys acikinsu Babu Wanda yayi..saidai sunada na islama daidai gwargwado...Hajara itakuma tana auren dandan megari jazuli suna zaune cikin rufin asirin Allah tanada Diya 1 .
Mamuda Alokacin Yana shekara ashirin yanuna shifa aure ykeso yayi to dayake anaso ya shiryu sai aka aura mishi salame wata Yar uwarsu anan cikin qauyen.Salame salihar mace Babu ruwanta abin duniya be dametaba, Sai Shi lamido ya Dora Mamuda a sana'ar gwanjo yaxama kaman yaranshi sbda yau d gobe ...ataqaice dai Shima Mamuda sana'ar gwanjo ykyi...Mamuda saida suka shekara 4 Allah bebasu haihuwa ba dayake duk family dayane shys hanne batayi facing wani challenging ba saidai itama tanaso taga gudan jinita .. yakumbo wato mahaifiyar Mamuda tashiga damuwa sosai sbd tanaso taga jinin autanta Mamuda...
Cikin Ikon Allah acikin shekara ta 5 Allah yabama salame ciki, zo kaga murna a wajen salame,Mamuda d yakumbo dama sauran yan'uwa...haka akaita renon ciki har Allah ya sauketa lfya akasamu 'ya mace kyakykywr gaske gata fara Sol da itaa me sunan yakumbo wato Fadila ana yimata inkiya da ( Ashnah) hartakai shekaru hudu inda Allah ya qara bama salame ciki aka haifi Yan 2 duka maza...
Ashnahh tataso tana qaunar iyayenta da Yan tagwayen qannenta...Saidai Ashnahh tun tana yarinya Allah yasa tanasan ilimin Boko dayake anan unguwar akwai yaran maqwbtansu sune take gani suna tafiya makaranta wato Ahlan da Fatima..to Allah da nashi ikon ita salame tanuna tanasan karatun Amma Shi Mamuda ba hakan take ba da qyal dai akayi convincing dnshi ya yarda amman deep down bawai so ykeyiba sbd yakumbo tasa bakine..
Cikin Ikon Allah tafara xuwa makaranta akasata a nursery 1 inda shikuma Ahlan yke primary 6 Fatima Kuma primary 1 tare suke tafiya makarantar..... Ashnah da Ahlan sun shaqu sosai.. Ashnah Allah yayita da basira da saurin fahimtar Abu ta Sha cin kyaututtuka daga wurare dama sbda kwaxonta...suma Yan biyo sun girma ansasu a makaranta babudai yanda Mamuda ya iya sbda yakumbo tace tunda su basuyi ilimin zamani ba gwnda su jikoki suyi..
A Yanxu haka Ashnahh takammalla secondary..shikuma Ahlam Yana N.C.E dinshi anan cikin garin katsina Yana shekarar Shi taqarshe ne aynxu, itakuma Fatima tayi aure...shaquwa sosai ta shiga tsakanin Ahlan da Ashnah Wanda har daga baya suka gane soyayyace tsakaninsu..
Ammanshi Mamuda bayasan tarayyarsu,inkanaso kaga fushinshi to kayi maganar Ahlam.Kuma wannan tsanar tasamo asaline tun lokacinda mahaifin Ahlam suka taba samun sabani dashi Mamuda to shikenan yqi jinin Malan Armaya'u...dayake Shi Mamuda yanada riqoo.
Wannan Kenan....*****************************
Yarima Fadil.............
Don't forget to vote
Comments
&
Share..😍😍
YOU ARE READING
✨ Yarima Fadil✨✨
Krótkie OpowiadaniaAkwai wasu masoya biyu sun shaqu d juna suna mutuwar qaunar junansu amman dayake Rai da Buri yke kudi yaxo yayi yankan qauna ku biyo Ni danjin yacce xata kaya....