SAMU DA RASHI...!
A kan ce ana iya sabawa da komai, akance yau da gobe bata bar komai ba, shin ana iya sabawa da bak'ar k'addara? Kowacce dak'ik'a data harba a agogo tana harbawa ne da rubutun wata k'addara a rayuwarmu, k'addarar da zata iya zama shafi cikin littafin rayuwarmu, Lokaci baya jira, duk dakikar da ta wuce ba zata dawo ba...