CANJIN MUHALLI
Ana kiranta Jidda Sufi, ƴar auta ga Governor Sufi Adam. Duk da jindadi haɗe da tsaron da suke dashi a matsayinsu na iyalan Governor bai hana wani mummunar al'amari faruwa da zuriyarsu ba. Cikin son nisanta kanta da mahaifinta wanda take ganin laifinshi ne sanadiyyar rugujewar farin cikinsu yasa Jidda ta ƙaura daga...