IDAN KIN GYÃRU

1 0 0
                                    

*🌴IDAN KIN GYÃRU🌴*
                *To dukkan al’umma*
                                 *🌴TÃ GYÃRU🌴*

*Laifi na goma sha shida (16): ƙin riƙo da hijãbi na shari’a da kula da sharaɗan hijabi wanda suka haɗa da:*

👉🏼 1-Ya rufe dukkan jiki bãki ɗaya.
👉🏼 2-Kada ya zama na kwalliya da ado.
👉🏼 3-Ya zama mai kauri ba mai shara-shara ba.
👉🏼 4-Ya zama yalwatacce ba matsattse ƙuntatacce ba.
👉🏼 5-Kada ya zama yana kama da tufãfin maza.
👉🏼 6-Kada ya zama wanda aka/ake sanyãwa turãre musamman yayin fita waje.
👉🏼 7-Kada yayi kama da hijãbin/tufãfin arnã kãfirai.
👉🏼 8-Kada ya zama na shuhura wato mai tsãdar gaske ko mai arhar ƙarshe.

📚 Allah (SWT) yana faɗa cikin Suratul Ahzãb ãya ta (59) cewa: ((Ya kai Annabi! Ka ce wa mãtan aurenka da ‘yã’anka da mãtan muminai su kusantar da ƙasã daga manyan tufãfin da ke a kansu. Wancan ya fi sauƙi ga a gane su dõmin kada a cuce su. Kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai)).

✍🏼 Wato sanya tufafi umurnin Allah ne kuma umurnin Manzon Allah (SAW) ne, don haka mai son Allah da Manzonsa dole subi abin da Allah da Manzonsa cikin duk abin da yayi musu daɗi da ma wanda ransu ba ya so.

👉🏼 Shi hijibi sutura ne ga ‘ya mace ko da mutumin banza ba ya iya kula mai hijabi, amma idan mace ta fito tsirãra ba hijabi to kowane kare da jãki da dõki dole ya taya!

✍🏼 Wanda kuma hakan ba mutunci ba ne ace mace ta fito daga gida zuwa wane wajen maza sama da goma duk suyi ta kulã ta kawai don ta fito babu kayan musulunci a jikinta!

*Allah ya shiryar da mu*

*📝Abba Lawan Hassan {Abu Aysha}.*

IDAN KIN GYARUWhere stories live. Discover now