IDAN KIN GYÃRU

0 0 0
                                    

*🌴IDAN KIN GYÃRU🌴*
                *To dukkan al’umma*
                                 *🌴TÃ GYÃRU🌴*

*Laifi na ashirin da tara (29): Ɗõrawa miji abin da ba zai iya ba:*

👉🏼 Wasu cikin mãta suna ɗõrawa mijinsu abin da ba su da halin yi musu, musamman wajen siyan abin da yake ba wajibi ba, kawai ana yin abin ne don gyãran zama kamar tace sai ya dinga bãta wata babbar kyauta duk sati ko wata.

✍🏼 Ko tace sai ya siya mata kãya mãsu tsãda wata ƙila ma wani anko ne za tayi na wata ƙawarta tun ta makarantar boko!

👉🏼 Haka ma dai ɗõrawa miji wasu abubuwa na kashe kuɗi masu yawa, hakan duk bai dace ba, da yawa mãta suna sanya mazansu neman haram don kawai su kyautata musu, idan mutum ba shi da abin da zai ba ta kuma ta tãkura masa a kan ya biya mata wata buƙata da take da ita, hakan na sanya wasu faɗawa cikin abin da bai dace ba.

📚 Allah (SWT) yana faɗa cikin Suratuɗ Ɗalãƙ ãya ta (7) cewa: ((Sai mawadãci ya ciyar daga wadãtarsa kuma wanda aka ƙuntata masa arziƙinsa, to, sai ya ciyar daga abin da Allah Ya bã shi. Allah bã Ya kallafa wa wani rai fãce abin da Ya bã shi. Allah zai sanya sauƙi a bãyan tsanani)).

✍🏼 Wasu na ganin cewa kowa ya ciyar da ɗaukar nauyin matarsa dai-dai da yadda ake mata a gidansu kafin ya auro ta!

👉🏼 Amma da yawa cikin malamai sunce: A’a ana duba da abin da mijin yake da shi ne, ba abin da aka saba yi mata a gida ba, kuma wannan shi ne abin da waccen ãyar take magana a kai.

*Allah ya shiryar da mu*

*📝Abba Lawan Hassan {Abu Aysha}.*

IDAN KIN GYARUWhere stories live. Discover now