IDAN KIN GYÃRU

0 0 0
                                    

*🌴IDAN KIN GYÃRU🌴*
                *To dukkan al’umma*
                                 *🌴TÃ GYÃRU🌴*

*Laifi na talatin da ɗaya (31): ƙin neman izinin miji a wasu abubuwa da take ganin kamar ma aikin lãda ne:*

👉🏼 Wasu mãtan sukan faɗa cikin kuskure ba tare da sani ba, ita tana zaton aikin alheri ma take yi, kai har lãda ma za ta samu alhali kuwa laifi ake rubuta mata!

✍🏼 Misali mace tayi azumin nafila ba tare da izinin mijinta ba, ko ta baiwa wani dãmar ya shiga gidanta ko da maƙwabtanta ne shi ma ba tare da izinin mijinta ba.

📚 Ya zo a Hadisi Manzon Allah (SAW) yace: ((Kada/bai halatta mace tayi azumi -na wata rãna banda Ramadan-; alhãli mijinta yana gari; ba tãre da ta nemi izininsa ba)).
Bukhary.

✍🏼 Wato haƙƙin miji a kan mãtarsa yana da yawa, har ta kai cewa ko azumin nãfila za tayi; sai ta nemi izininsa, idan har yana gari, sabõda kar taje tana azumi shi kuma ya dãwo da rãna yana buƙatar alãƙar aure da ita, ita kuma tace azumi take, amma idan ta nemi izininsa hakan sai yasa shi ya kula don ta ƙãrasa azuminta, kuma har ma ya sãmu lãda.

👉🏼 Amma fa hakan na fãruwa ne ga mãtar da take cikakkiyar biyayya ga mijinta; Nana Aisha (RA) tace idan ana bin ta azumi bã ta sãmun dãmar biya; sai a watan sha’aban -don kula da buƙãtun Annabi (SAW)-; sabõda Manzon Allah (SAW) yana yawan azumi a watan, to, kunji tsãbar biyayya irin ta uwar Muminai.

*Allah ya shiryar da mu*

*📝Abba Lawan Hassan {Abu Aysha}.*

IDAN KIN GYARUWhere stories live. Discover now