🌴IDAN KIN GYÃRU🌴

3 0 0
                                    

*🌴IDAN KIN GYÃRU🌴*
                *To dukkan al’umma*
                                 *🌴TÃ GYÃRU🌴*

*Laifi na tara (9): Fãtan mutuwa don an shiga wata masifa:*

👉🏼 Wasu cikin mãta suna yiwa kansu addu’ar cewa su gwãra ma ace su mutu su huta; kawai don wata cuta ta sãme su ko wani bala’in ya afka musu.

📚 Ya zo a Hadisi Manzon Allah (SAW) yace: ((Kada wani a cikinku yayi fãtan mutuwa don wata cuta da ta sãme shi/afkã mishi, idan mutum dõle sai yayi addu’ar: to, yace: “Yã Allah ka rãyã ni idan rãyuwa ta ita tafi alheri, kuma Allah ka karɓi raina idan mutuwa ta ce tafi alheri)).
Bukhary da Muslim.

✍🏼 Wasu ma cikin mãta sukan yi mummunar addu’a ga yãyãnsu; bisa wani kuskure da suka ɗanyi, kawai sai aji irin waɗannan iyãye suna addu’ar sharri ga yãyãnsu da munãnan addu’o’i!

👉🏼 Wata ƙila kiyi addu’ar ta dãce da lõkacin karɓar addu’ar!

📚 Ya zo a Hadisi Manzon Allah (SAW) yace: ((Addu’a guda uku karɓaɓɓu ne bãbu makawa/shakka cikin karɓarsu: Addu’ar mahaifi a kan yãyãnsa, da addu’ar matafiyi, da addu’ar wanda aka zãlunta)).
Bukhary.

👉🏼 Wasu cikin mãta sukan aibata tãre da mummunar addu’ar ga rãnar da suka haifi yãyãn nasu, wanda hakan na cikin zãgin zãmani!

📚 Ya zo a Hadisi Manzon Allah (SAW) yace: ((Allah (SWT) yana cewa: Ɗan Adam yana cutar da Ni, yana zãgi/aibata zãmani, alhãli kuwa Nine zãmani, dukkan al’amura a hannuNa suke, Ina jujjuya dare da yini)).
Bukhary da Muslim.

*Allah ya shiryar da mu*

*📝Abba Lawan Hassan {Abu Aysha}.*

IDAN KIN GYARUWhere stories live. Discover now