IDAN KIN GYÃRU

1 0 0
                                    

*🌴IDAN KIN GYÃRU🌴*
                *To dukkan al’umma*
                                 *🌴TÃ GYÃRU🌴*

*Laifi na hamsin da huɗu (54): ƙin runtse ido ga kallon maza:*

👉🏼 Wasu mãtan sukan baza ido wajen kallon haram kuma ba su runtse ido ga mazãjen da bã nã su ba, kai ka ce ãyar da tai hani ga kalle-kalle maza kawai ta shãfa mazan ne banda mãtan!

✍🏼 Allah (SWT) yana faɗa cikin Suratut Nur ãya ta (30-31) cewa: ((Ka ce wa muminai maza su runtse daga ganinsu, kuma su tsare farjojinsu. Wannan shi ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah, Mai ƙididdigewa ne ga abin da suke sanã’antãwa ().

📚 Kuma ka ce wa muminai mãtã su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjojinsu, kuma kada su bayyana ƙawarsu face abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su doka da mayãfansu a kan wuyan rigunansu…)).

✍🏼 Kuma wannan hanin ya shãfi kallon mazaje ne a fili ko ma a talabijin ko jaridu ko mujallu da wasunsu, musamman waɗanda suke motsa wutar sha’awa da faɗawa cikin fitina.

👉🏼 Haka ma dai haramcin ya shãfi kallon mace zuwa ga al’aurar mace!

📚 Ya zo a Hadisi Manzon Allah (SAW) yace: ((Kada namiji ya kalli al’aurar namiji, kuma kada mace ta kalli al’aurar mace)).
Muslim.

📚 A wani Hadisin kuma Manzon Allah (SAW) yace: ((Zinar idãnuwa shi ne kallo)).
Aɗɗabrãny.

*📝Abba Lawan Hassan {Abu Aysha}.*

IDAN KIN GYARUWhere stories live. Discover now