IDAN KIN GYÃRU

1 0 0
                                    

*🌴IDAN KIN GYÃRU🌴*
                *To dukkan al’umma*
                                 *🌴TÃ GYÃRU🌴*

*Laifi na ashirin da shida (26): Yin wãtsi ga yiwa ‘yã’yã tarbiyyar musulunci:*

👉🏼 Rashin kula wajen yiwa ‘yã’yã tarbiyya irin ta addinin musulunci, wasu iyãyen sukan yi halin ko in kula ga tarbiyyar ‘yã’yã musamman idan suka lura cewa yãran sunfi sha’awar koyi da ɗabi’ar da ba ta su ba.

✍🏼 Sai aga iyãye na siyãwa ‘yã’yã kãyan sakãwa waɗanda ba su dãce da tarbiyyar musulunci ba, kamar siya musu matsattsun kãya ko wata shiga dai da ana ganin an san cewa ba tarbiyyar musulunci ba ce.

👉🏼 Kai wasu ma sukan siyãwa ‘yã’yã kãyan da ke ɗauke da hotuna ko ma waɗanda suke ɗauke da alãmar (Cross)!

👉🏼 Ko aga uwa ta shirya bikin murnanr ranar haihuwar ‘yã’yãnta ko mace tace da mijinta ya sanyã ɗanta/’yarta a makarantar kõyon wãƙa!

✍🏼 Wasu kuma su dinga sanyãwa ana yiwa ‘yã’yã maza aski na rashin kirki kawai don kwaikwayon arnã kãfirai!

👉🏼 Abin da ya wajaba ga mace musulma shi ne tayi kwaɗayin yiwa ‘yã’yã tarbiyyar musulunci, tayi musu tãnadi na tarbiyyar kamar yadda sahabbai suka yiwa ‘yã’yãnsu tarbiyya, ta yadda ‘yã’yã za su tãso alhãli zuciyarsu na sane da Allah SWT.

✍🏼 Kuma uwa ta lura wajen kula da sallar ‘yã’yã da halartar masallaci da haddar alƙur’ani da kimsa musu cewa da su musulunci zai ci nasara, da kawar musu da kai wajen duk wani abu da ba shi da amfãni a duniya balle kuma a lãhira.

📚 Allah (SWT) yana faɗa cikin Suratut Tahrim ãya ta (6) cewa: ((Yã ku waɗanda suka yi imãni! Ku kãre wa kanku da iyãlanku wata wuta makãmashinta mutãne da duwãtsu ne. a kanta akwai waɗansu mala’iku mãsu kauri, mãsu ƙarfi. Bã su sãɓã wa Allah ga abin da Ya umurce su, kuma sunã aikata abin da ake umurnin su)).

*Allah ya shiryar da mu*

*📝Abba Lawan Hassan {Abu Aysha}.*

IDAN KIN GYARUWhere stories live. Discover now