Zaune take a bakin gado tayi tagumi tana tunani 'wai ni Bahijjah me nayiwa Inna ne a rayuwa irin wannan tsana haka sai kace kishiyarta, ai koda ni kishiayrtace bai kamata ta dinga nuna irin wanna tsanar agare niba nifa matar danta ce meye ne banayi mata ne?' tana cikin duniyar tunanin ne taji sallamar yaro yashigo cikin dakin dauke da kaya,
"Baban Kabir ne ya dawo" tace "To sannunka da kokari kaji....." ijiye jakar yayi ya fita cen bada jimawa ba sai ga officer lawan ya shigo tayi murna sosai da ganin mijinta haka shima yayi farin ciki sosai dan har sun kasa boye murnar su dukawa yayi ya dauki Kabir yana fadin "Masha Allah ashe haka yaronnan ya girma haka gashi har yazama samari" murmushi Bahijjah tayi tace "Samari a ina?". "Gashi kuwa kina gani yaro mai kama da babarsa" Ya fadi cikin wasa.
"Allah ya kiyaye nikam baiyi kama dani ba sai dai babansa..." wasa yakemasa shikuma sai famar dariya yake.
***Yaune Bahijjah taje gida tun safe domin tayi musu sallama dan gobe ne zasu wuce Zamfara, tayi ziyara sosai dan duk wani jininta na kusa saida taje ta musu sallama, suka mata goma sha na arziki, nanma Ummah tayi mata nasiha sosai mai ratsa zuciya sannan ta bata daddawa da miyar kuka da kayan kamshi irinsu citta da kanumfari masu yawa sosai, tayiwa Ummah godiya bata tafi gida ba sai bayan sallar isha.
Ranar lahadi da misalin karfe goma na safe su Bahijjah suka kama hanyar Zamfara, basu sauka ba sai karfe daya da rabi na rana, Bahijjah tayi mamaki sosai a lokacin da ta shiga dakinta ta tarar da dakin an gyarashi sosai an cenja mata jeren dakin ba kamar yanda ta tafi ta barshi ba, an shimfida mata sabon zanen gado, an cenja mata labulayen dakin sababbi ne aka saka mata, dakin sai kamshi yake kamar dakin sabuwar amarya, tayi matukar mamaki kuma taji dadi sosai, lawal ma saida yayi mamaki yanda yaga dakin an cenja masa fasali dan ba a haka yatafi ya barshi ba, kenan dai wanna garan acikin kwana biyu a kayishi bayan tafiyarsa Sokoto, kuloli tagani harguda uku tana bude kular farko taga farar shinkafa, sai ta sake bude dayan taga jar miya ce a ciki, dayar kuma da ta bude pepesoup din kayan ciki ne tagani a ciki, tarasa abinda zatace sai kawai hawaye yaga suna zuba a fuskarta."Bahijjah lafiya naga kina kuka?" Lawan yayi saurin tambaya, cikin shashekar kuka take Magana "Officer bansan ta hanyar dazan ramawa su Maman Abdul ba dan sun nunamin so da kauna bazan iya biyansu abinda suka min ba, duba kaga fa abinda sukamin gyaran daki harda girki..." tana maganar tana share hawayen da ke zubowa daga idonta.
"Hakane Bahijjah bamuda abinda zamu biyasu saidai muyi masu addu’ar gamawa da duniya lafiya".
Sunci abincin sosai "Bahijjah barana naje na leka office naga meke gudana" Yayi magana yana mikewa "To Allah ya dawo dakai lafiya" "Ameen Bahijjah sai na dawo...""Assalamu alaikum amaryar karni" Maman Abdul ce sai ga sauran matan gidan sunbiyu bayanta sun cika dakin tam har ba gurin zama sunata mata tsiya dariya kawai take binsu da ita.
"Ai munzata bazaki dawo ba har muna shirin tafiya muzo da yaronmu kekuma sai kasha zamanki a Sokoto" nafisa ce ke maganar a cikin zolaya "Hmm ai wallahi da kun kyauta min kun rabani da damuwa" cewar Bahijjah.
"Sannunku da fama naga aiki nagode kwarai Allah yabar zumunci naga harda girki Allah ya saka da alkahiri" "Bamaso kirike godiyarki ba donki mukayi ba dan danmu Kabir mukayi..." inji Maman Fa’iza dariya suka saka gabaki dayansu har Bahijjar da hakadai sukayita firarsu ta bayan rabo har dare yayi sukayi sallama kowacce taje tanemi gurin kwanciya.
***
"Wayyo Allah na zan mutu, cikina Babilon ka taimake wallahi mutuwa zanyi!" ta dafe cikinta tana zube a tsakiyar daki sai birgima take, babilon saurayinta ne da suka kwana tare budar bakinsa yace "Me kikace in me? In taimakeki tabb ashe kina ruwa ai ba yanda banyi ba akan kada kisha wani abu da sunan zubar da ciki amma kikaki to kuma yanzu me kike so namiki nan da kika ganni ko tabaki bazanyi ba dan bazaki mutu ba ace nine kingama tafiyata" kafarsa ya zura takalmi ya fice daga dakin, Ummi ce taji kukan yayi yawa ta fito daga dakinta dan ganin wacece ke kukan"Aa kamar dakin Sa'a ne nakejin ihunnan anyama ba Sa'ar bace baradai na duba!" Sa'a tagani kwance a kasa sai famar birgima take tana fadin "Zan mutu zan mutu....." a gigice ta karaso kanta ta dagota tana fadin "Sa'a meke damunki?" "Ummi ki taimaka min kikaini asibiti mutuwa zanyi ki taimakeni Ummi" bako takalma a kafarta tafito har bakin hanya ta nemi adai-daita sahu tazo ta dauki Sa'a takaita wata private hospital da suke zuwa a duk lokacin da sukaji canji a jikinsu ko suna sun zuabar da ciki dan sun zubar da ciki yafi a kirga, da kyar Nurse din suka samu suka shawo kan abun, sun bukaci wasu yan kudi da za ayimata wata allura, budar bakin Ummi tace
"Nnifa taimakonta nayi kwandalata bazan bada ba dan lokacinda taji dadinta ban sani ba!" tana maganar tana jujjuya baki da ido irin na yan tasha "Taimako da zan iya mata shine naje na sanar da Uwarta inda abinda zata iyayi in kuma bazata iya ba ta barta ta mutu yarta ce ba tawa ba"
***
YOU ARE READING
Kaddarar Rayuwa
ActionA True Life Story!!! kaddarar rayuwata littafine da yake magana akan yanda rayuwa take, zaka iya tsintar kanka acikin kowane yanayi na rayuwa idan kuma kayi hakuri to zakaci muriyar hakurinda kayi...